16/06/2026
Shugaba Tinubu Ya Amince da Ɗaukar Ma’aikatan Tsaron Daji 1,000 a Katsina, Gwamna Raɗɗa Ya Nemi Haɗin Kan Al’umma Wajen Yaƙi da Matsalar Tsaro
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin tsaro a jihar inda a ranar Talata 16 ga watan Yuni 2026, ya haɗa taron tattaunawa da ƙungiyoyin malaman addinin Musulunci da sauran masu ruwa da tsaki domin samo hanyoyin da al’umma za su taka rawa wajen kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.
A lokacin zaman an bai wa wasu daga cikin malaman damar tofa albarkacin bakin su domin ba Gwamnan wasu shawarwari da suke ganin za su ƙara taimakawa akan ƙoƙarin da gwamnatin ke yi wajen magance matsalar tsaro a jihar Katsina.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Gwamna Radda ya bayyana cewa an shirya zaman ne domin sauraron ra’ayoyi da shawarwarin malaman addini kan yadda za a samu mafita mai ɗorewa ga matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa yaƙi da ƴan bindiga ba aiki ne da hukumomin tsaro kaɗai za su iya yi ba, yana mai cewa haɗin kan al’umma da bayar da bayanai masu amfani na da muhimmiyar rawa wajen cimma zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa bincike ya nuna akwai wasu daga cikin jama’a da ke taimakawa masu aikata laifuka ta hanyoyi daban-daban, ciki har da samar musu da bayanai da kuma taimakawa wajen sayar da dabbobin da aka sace. Saboda haka, ya ce wajibi ne a wayar da kan al’umma domin kowa ya fahimci rawar da yake da ita wajen yaƙi da rashin tsaro.
Gwamna Radda ya bayyana malaman addinin Musulunci a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen gina kyawawan ɗabi’u da tarbiyya a cikin al’umma, yana mai cewa shawarwarin su na da matuƙar amfani wajen samar da mafita ga matsalolin tsaro.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ɗauki matakai masu tsauri domin dakile ayyukan masu laifi, ciki har da haramta amfani da babura a wasu ƙananan hukumomi da matsalar tsaro ta fi kamari kamar Musawa da Matazu. Haka kuma, an sanya takunkumi kan amfani da wasu cibiyoyin POS da wuraren cajin wayoyi da ake zargin suna taimakawa ayyukan masu laifi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an hana sayar da man fetur na bunburutu a wasu wurare a faɗin jihar domin rage damar da ‘yan ta’adda ke samu wajen gudanar da ayyukansu.
Ya ce duk waɗannan matakai an ɗauke su ne bayan tuntuba da shugabannin al’ummomin yankunan da abin ya shafa, tare da alƙawarin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
A wani muhimmin ci gaba kuma, Gwamna Radda ya sanar da cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da buƙatar gwamnatin jihar na ɗaukar matasa maza da mata 1,000 aiki a matsayin Ma’aikatan Tsaron Daji domin ƙarfafa ayyukan tsaro a jihar.
Ya ƙara da cewa za a samar wa waɗannan ma’aikata kayan aiki da horon da s**a dace domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Haka kuma, Gwamna Radda ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa ci gaba da tallafa wa jihar da kuma ƙara yawan jami’an tsaro daga rundunar soji, ’yan sanda da Hukumar Tsaro ta DSS da aka tura jihar.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu sa ido tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai, yana mai jaddada cewa tsaro alhakin kowa ne kuma haɗin kan jama’a ne zai tabbatar da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Katsina.
Mustapha Samaila Ingawa (MS Ingawa)
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
June 16, 2026.