21/04/2025
Kukan Kurciya......(2)
Daga cikin abin da Imam Alkadi Iyad - Allah ya yi masa rahama - ya lissafa cikin zagi da batanci ga Annabi S.A.W akwai; Mutum ya ambaci zagi ko batanci ga Annabi (S.A.W) ya ce, wai wani ne ya fadi hakan, kuma a duba ba a ga wannan magana ba, to shi ne ya yi wannan zagin, don haka, hukuncinsa, hukuncin wanda ya zagi Annabi ne. Ga abin da yake cewa a cikin "Ash-shifa (2/246). Ya ce:
وإن اتهم هذا الحاكي فيما حكاه أنه اختلقه ونسبه إلى غيره، أو كانت تلك عادة له، أو ظهر استحسانه لذلك، أو كان مولعا بمثله والاستخفاف له، أو التحفظ لمثله وطلبه، ورواية أشعار هجوه صلى الله عليه وسلم وسبه، فحكم هذا حكم الساب نفسه، يؤاخذ بقوله ولا تنفعه نسبته إلى غيره، فليبادر بقتله، ويعجل إلى الهاوية أمه.
Ma'ana: "Idan aka tuhumci wannan mai kawo labarin (zagi ga Annabi) cikin labarin da ya kawo cewa, shi ne ya kirkiri wannan labari ya dangana shi ga waninsa, ko kuma dama hakan al'adarsa ce, ko kuma ya nuna kyan abin, ko kuma dama yana yawan kawo irin hakan, da daukarsa ba komai ba, ko kiyayewa daga irin wannan abin, da neman wakokin da a yi wa Annabi Zambo da zagi, to hukuncin mai yin haka, shi ne hukuncin mai zagin Annabi, za a k**a shi da wannan zance, kuma cewa wani ne ya fada ba zai amfane shi ba. Kawai a gaggauta kashe shi, a gaggauta kai shi uwarsa wutar Hawiya".
Wannan shi ne abin da Alkali Iyad ya fada, don haka duk wanda zai ce auren Manzon Allah (S.A.W) da Nana Safiyya F......, ya dangana hakan ga Imamu Muslim, har ya ba da lambar hadisi, kuma a ce ya bude ya karanto wurin, ko ya nuna wurin, amma ya kasa, saboda babu hakan a ciki, karya kawai yake, to ko shakka babu shi ne ya yi wannan batanci ko zagin.
Hakanan wanda zai ce sahabbai mata suna zuwa wajen Annabi (S.A.W) su nuna suna bukatarsa, irin bukatar....!. Ya ce hakan yana Sahihul Bukhari, a ce, nuna wurin ya kasa, don babu a ciki. Shi ma ba shakka shi ya yi wannan batancin ko zagin!.
Don haka, babu sharri ko kage a maganar nan, sai dai a wurin wanda yake da son zuciya, ko ya jahilci lamarin.
Allah ka kara mana so da imani da biyayya ga Annabi (S.A.W), ka tabbatar da dugaduganmu a kan sunnarsa. Ameen
Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo