News Harvest Hausa

News Harvest Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from News Harvest Hausa, Media/News Company, Garki, Garki II.

MANUFAR NEWS HARVEST NIGERIA

News Harvest Hausa Jarida ce ta Yanar Gizo wacce ta zo da manufar samar da sahihan labarai da ingantattun rahotanni na ci gaban ƙasa da haɗin kai tare da bada gudun mowa

Hukumar tace fina-finai ta  Kano ta haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma'aiki sannan ta gayyaci Mai Dubun Is...
16/09/2025

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma'aiki sannan ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tazul Izzi

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta dukkan muƙabalar mawakan addini a jihar, sai dai idan an samu sahalewar hukumar tun kafin gudanar da su.

Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin kaddamar da kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Malam Isha Abdullahi, Daraktan Harkokin Musamman na hukumar.

El-Mustapha ya ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon muƙabalar da aka gudanar ba tare da izini ba tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi, wadda ya bayyana a matsayin karya ƙa’idodin hukumar.

Hukumar ta bai wa mawakan biyu tare da masu gabatar da muƙabalar wa’adin awanni 24 su bayyana gaban kwamitin binciken.

A cewar hukumar, shirya irin wannan muƙabala ba tare da amincewar ta ba ya sabawa dokar Tace Fina-finan Jihar Kano, kuma hakan na iya haifar da ɗaukar matakan shari’a masu tsanani.

Shugaban hukumar ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da tsarawa da kuma sa ido kan harkokin mawakan addini da masu nishadantarwa a jihar, bisa tanadin doka. Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da tallafa wa hukumar da bayanai masu amfani da za su kawo zaman lafiya, fahimtar juna, da bunƙasar al’adu a jihar.

A kullum aƙalla motoci 10 ke lalacewa baya ga fashewar gilashinsu a hanyar Dukku, wadda mintuna 50 kacal, yanzu ta koma ...
16/09/2025

A kullum aƙalla motoci 10 ke lalacewa baya ga fashewar gilashinsu a hanyar Dukku, wadda mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu…

Daga
Rilwan Muhammad da Rabilu Abubakar, Gombe

Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta.

A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu saboda lalacewar hanyar, abin da ke jawo gajiya da takaici ga fasinjoji da masu tuƙi.

An fara gina hanyar Gombe-Dukku-Darazo ne tun a shekarun 1980, aka gyara ta a farkon shekarun 2000. Sai dai daga baya aka yi sakaci da ita duk da kasancewarta hanyar da matafiya daga jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Bauchi da wasu ke bi.

“Gyaran motoci na cinye mana kuɗi”
Usman Abubakar, direba mai shekaru 45 da gogewar tuki na sama da shekaru 19, ya ce lalacewar hanyar na sa direbobi kashe kuɗi masu yawa wajen gyaran motoci.

“Gaskiya hanyar ta lalace matuƙa. A da tafiyar Dukku zuwa Gombe kan ɗauki mintuna 45, yanzu kuwa ko awa biyu ba ta isa ba. Rami ne a ko’ina, musamman daga Tongoyel zuwa Bojude da Bozonshulwa. Sau da dama idan ka fito da safe sai ka tarar da motoci sun tsaya cak a hanya. Shock absorber, gilashi da sauran sassan mota suna yawan lalacewa saboda ramukan hanyar,” in ji shi.

Ya ce a da ‘shock absorber’ na iya kaiwa shekara biyu kafin ya lalace, amma yanzu ko watanni uku bai yi ba sai ya karye. Hakazalika tsohon gilashi da ake siya ₦90,000 yanzu cikin sati biyu kawai sai ya fashe.

Usman ya kuma ce ya sha yin haɗura a hanyar cikin watanni biyu kacal, inda tayar motarsa ta fashe, ‘shock absorber’ ya karye, sannan kingpin ya lalace — duka sakamakon shiga ramuka.

Wani direba, Abubakar Hassan, ya ce lalacewar hanyar ta kai shi ga tunanin barin aikin tuƙi gaba ɗaya saboda asarar kuɗi.

“Idan ruwan sama ya sauka, tafiya sai ta koma tamkar azaba. Sau da dama motoci kan kwana a hanya saboda lalacewa,” in ji shi.

Fasinjoji sun bayyana ƙalubale
Kabiru Zubairu, ɗaya daga cikin fasinjojin da ke yawan amfani da hanyar, ya ce, “A da tafiyar kilomita 72 kan ɗauki mintuna 45 zuwa 60, yanzu ta koma awa biyu. Idan na taso Dukku da karfe 7:00 na safe, yanzu sai mu isa bayan 9:00. Wannan na jawo mana jinkiri sosai.”

Wani fasinja, Abubakar Aliyu, ya ce mutane da dama sun daina zuwa Gombe saboda halin hanyar. “Idan ka yi tafiya sai jikinka ya yi ciwo. Wasu matasa kan zuba yashi a cikin ramuka, amma ruwan sama yana wanke shi,” in ji shi.

Mai sharhi a harkokin jama’a, Sulaiman Sa’idu Liman, ya ce kusan kilomita 64 daga cikin 72 na hanyar Dukku zuwa Gombe sun lalace, kuma motoci yanzu ba sa iya wuce gudu na kilomita 20 a awa ɗaya.

“Hanyar na da muhimmanci ga tattalin arziki da walwalar al’umma. Ana jigilar kayan gona, kayayyakin lafiya da marasa lafiya ta wannan hanya zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) Gombe,” in ji shi.

Likita Aliyu Bashir kuwa ya ce lalacewar hanyar na haifar da matsaloli ga lafiyar jama’a, musamman ƙura da ke haddasa cutar asma, da kuma haɗarin haihuwa kafin lokaci ga mata masu juna biyu saboda girgizar mota.

Kungiyoyi da direbobi sun yi kira
Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dukku (DCF), Muhammad Bala Hashidu, ya yi kira da a gaggauta gyaran hanyar gaba ɗaya.

Shi ma shugaban Kungiyar Direbobi ta NURTW a Dukku, Abdulhamid Hassan, ya ce kusan kowace rana ana samun aƙalla motoci 10 da ke lalacewa a kan hanyar, abin da ya rage musu kuɗin shiga.

Gwamnati ta magantu
Mai magana da yawun gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da takwarorinta na Arewa maso Gabas domin samun tallafin Gwamnatin Tarayya wajen gyaran hanyar.

“Kwanan nan gwamnonin yankin sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu inda s**a roƙi a gyara muhimman hanyoyi ciki har da wannan. Domin hanya ta tarayya ce, gwamnatocin jihohi ba su da ikon gyaran ta kai tsaye. Amma gwamnoni sun dage wajen ganin an gyara ta,” in ji shi.

Address

Garki
Garki Ii

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when News Harvest Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share