13/10/2025
Kamfanin Credit Direct ya tallafawa ma'aikata 100 a Katsina
Yayin da ake bikin makon hidimtawa abokan hulɗa na shekarar 2025, kamfanin Credit Direct mai zaman kansa ya raba tallafin wasu kayayyaki na musamman ga ma’aikatan gwamnati 100 a jihar Katsina.
Kamfanin Credit Direct Limited, wanda reshe ne na First City Monument Bank, wato (FCMB), ya raba jikkuna 100 da ke ɗauke da wasu kayayyakin amfanin yau da kullum ga ma’aikatan gwamnati da ke hulɗa da FCMB a jihar Katsina.
Jaridar Hikaya ta ruwaito cewa an gudanar da wannan shiri ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025, domin nuna jajircewar kamfanin wajen nuna godiya ga abokan hulɗa da kuma ƙarfafa alaƙar zumunci ta hanyar ayyukan ci gaban al’umma masu tasiri.
An gudanar da bikin a Ofishin Credit Direct Limited da ke cikin bankin FCMB a Katsina, inda aka raba kayan abinci da na amfanin yau da kullum ga ma’aikatan gwamnati daga sassa daban-daban na ma’aikatu. An bayyana taron da nufin ƙarfafa zumunci, nuna godiya, da kuma haɓaka jin daɗin abokan hulɗar da s**a kasance masu aminci ga kamfanin tsawon shekaru.
A yayin da yake jawabi, Musa Ayuba, wakilin kamfanin Credit Direct Limited a jihar Katsina, ya bayyana cewa wannan tallafi na cikin shirin alhakin jama’a, wato (Corporate Social Responsibility - CSR) na kamfanin domin nuna godiya ga abokan hulɗa da kuma tallafa wa al’umma. Ya ce kamfanin na ɗaukar ma’aikatan gwamnati a matsayin abokan ci gaba kuma zai ci gaba da tallafa musu ta hanyar samar da lamuni mai sauƙi da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki.
Ayuba ya ƙara tunatar da cewa a watan Disamba 2024, kamfanin ya raba kayan abinci ga fiye da mutane 200 waɗanda s**a tsinci kansu cikin matsin rayuwa sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da kuma waɗanda s**a rasa matsuguni (IDPs) a fadin jihar Katsina. Ya ƙara da cewa wannan ya nuna irin tausayi da jajircewar kamfanin wajen rage wahala da kawo sauƙi ga al’umma, inda ya ƙara da cewa hangen kamfanin a fannin CSR ba ya tsaya kan harkar kasuwanci kaɗai ba, sai da tasirin zamantakewa da ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma.
Shi ma Alhaji Mannir Lawal, Darakta na Sashen Gudanarwa da Kayan Aiki a Ofishin Babban Sakataren Ma’aikata, ya yaba wa kamfanin bisa irin tallafin da yake bai wa ma’aikata lokaci zuwa lokaci. Ya bayyana Credit Direct Limited a matsayin kamfani mai gaskiya da amana, wanda ke da kyakkyawar niyya ga walwalar abokan hulɗarsa. Ya kuma yi kira ga sauran kamfanoni da su kwaikwayi irin wannan aiki na alheri, yana mai cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyin walwalar jama’a ba.
A nasa bangaren, Alhaji Abdurrahman Lawal, Darakta na Sashen Kula da Bashi, ya jinjinawa kamfanin bisa nuna damuwa da bukatun ma’aikatan gwamnati, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tattalin arziki. Ya bayyana cewa wannan tallafi zai ƙara wa ma’aikata kwarin gwiwa da ƙaunar aiki, tare da ƙarfafa su wajen inganta ayyukan gwamnati.
An kammala taron da mika kayan tallafin ga ma’aikata da kuma ɗaukar hotuna, inda jami’an gwamnati da ma’aikata s**a nuna godiyarsu ga kamfanin Credit Direct Limited bisa gaskiya, jajircewa da kyautata hulɗa da al’umma.