
18/08/2025
Sojojin Sama Sun Kuɓutar da Mutane 62 daga Hannun Ƴan Bindiga a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da kuɓutar mutane 62 da aka yi garkuwa da su, bayan wani luguden wuta na sojojin saman Najeriya da ya kai farmaki a sansanin fitaccen ɗan fashi Muhammadu Fulani da ke Jigawa Sawai, Ƙaramar Hukumar Danmusa, wacce ke iyaka da Jihar Zamfara. Harin da aka kai da misalin ƙarfe 5:10 na yamma ranar Asabar ya tilasta wa ‘yan bindiga barin sansaninsu, abin da ya bai wa waɗanda aka yi garkuwa da su damar tserewa.
Rahotanni sun nuna cewa mutane 12 daga cikin waɗanda s**a kuɓuta na samun kulawa a Asibitin Gwamnati na Matazu, yayin da wasu 16 ke tsare a sansanin sojoji na FOB da ke Kaiga Malamai. Gwamnati ta tabbatar da cewa za a haɗa waɗannan mutanen da iyalansu bayan an kammala binciken lafiya.
A cewar wasu daga cikin waɗanda aka ceto, ‘yan bindigar sun watse bayan luguden wutar da aka kai musu, abin da ya sa mutane kusan 62 s**a samu damar tserewa ta wurare daban-daban. Mafi yawan waɗanda aka sace an ɗauke su ne daga ƙauyen Sayaya a daren Litinin, 11 ga Agusta, 2025, lokacin da ‘yan bindigar Fulani s**a kai hari. Kungiyar ta dade tana addabar Matazu, Kankia, Dutsinma da wasu sassa na Jihar Kano.
Domin magance maimaita hare-haren ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Matazu da Bakori, gwamnatin jihar ta tura rundunar Quick Response Wing ta sojojin sama don dawo da zaman lafiya. Rundunar tsaro na ci gaba da sa ido a yankin domin gudanar da ƙarin aikin ceto. An bayyana cewa yankin na ci gaba da kasancewa cikin natsuwa.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gidaje na Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ya yaba da ƙoƙarin jarumtakar dakarun tsaro a madadin Gwamna Dikko Umaru Radda. Ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kawo ƙarshen matsalar ta’addancin ‘yan bindiga a Katsina tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.