
02/09/2025
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah Imam Dokta Abdullahi Bala Lau , Shugaban majalisar malamai Dokta Ibrahim Jalo Jalingo da daraktan ‘yan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti na farin cikin gaiyatar jama’a zuwa wa'azin ƙasa a garin kaduna tare da gagarumin taron gabatar da fassarar littafin WHERE I STAND “nan ne matsaya ta” da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya wallafa da Dokta Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa Larabci. Sai littafin AL’AKIDATUS SAHIHA, AHALARI, IZZIYYA, RISALA da ISHMAWI da Dokta Jalo ya juya daga zube zuwa wake.
Za a gudanar da gabatarwar ranar asabar 6 ga watan nan na Satumba 2025 da karfe 9am a dakin taro na Umaru Musa ‘YAR’ADUA HALL da ke Murtala Muhammed Square Kaduna.
Babban bako na musamman, mai girma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu GCFR
Mai masaukin baki, Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Iyayen taro mai alfarma Sarkin musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli
Babban mai gabatarwa Sanata Dokta Abdul’aziz Yari
Mai bitar littattafan babban limamin masallacin Sultan Bello Sheikh Muhammad Sulaiman.
Sai Dokta Ahmad Gumi zai yi magana a madadin iyalan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Manyan baki gwamnoni, shugabannin kamfanoni, tsoffin gwamnonin jihar Kaduna Dokta Ahmed Muhammad Makarfi, Dokta Ramalan Yero da Malam Nasiru Elrufai sai kuma almajirai da daliban marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Kazalika, kungiyar na gaiyatar jama’a zuwa taron karawa juna ilimi da tambayoyi da amsoshi kan illar masu ikirarin bin Kur’ani zallah wato ‘yan Ƙala ƙato da za a gabatar a dakin taro na Umaru Musa ‘Yar adua da ke Murtala Square Kaduna ranar Jumma’a 5 ga watan nan na Satumba 2025 daga bayan sallar la’asar.
Dokta Ibrahim Disina zai jagoranci taron da kulawar shugaban bita da taruka na kasa Dokta Abubakar Abdulsalam Baban Gwale. Masu jawabi sun hada da Sheikh Lawal Shu’aib Triump, Sheikh Abubakar Mazan Kwarai da Sheikh Musa Muhammad Dankwano.
Gabanin nan kwamitin DA’AWA karkashin jagorancin Sautus Sunnah Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina zai raba malamai daga safe zuwa la’asar zuwa masallatan Jumma’a don wa’azi da hububar Jumma’a.
A ranar asabar ɗin daga 8pm akwai gagarumin wa’azi na kasa a masallacin idi na sultan Bello, anan garin kaduna.
Malamai masu wa’azi:
Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
Dokta Ibrahim Jalo Jalingo
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
Sheikh Usman Isa Taliyawa
Sheikh Habibu Yahaya Kaura
Sheikh Muhamad Kabiru Haruna Gombe
Sheikh Barista Sabiu Jibiya
Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan
Sheikh Khalid Usman Khalid Jos
Sheikh Abdullahi Telex
Dokta Ibrahim Idris Darus Sa’ada
Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto
Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo
Farfesa Salisu Shehu
Farfesa Mansur Isah Yelwa
Farfesa Isa Ali Pantami
Sheikh Abdulwahab Abdallah (Imam Ahlis Sunnah)
Sheikh Muhammad Bn Usman
Sheikh Abubakar Sani Birnin Kudu
Sheikh Tijjani Ahmad Guruntun, da sauran malamai
Alarammomi sun hada da:
Alaramma Abubakar Adam Katsina
Alaramma Ahmad Sulaiman Kano
Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
Alaramma Usman Birnin Kebbi da sauran hafizai.
Allah ya ba da ikon halarta amin.
Sanarwa daga babban sakataren JIBWIS Dokta Muhammad Kabir Haruna Gombe ta hannun kwamitin labaru na kasa da hadin guiwar JIBWIS SOCIAL MEDIA
Allah ya ba da ikon halarta amin.
Jibwis Nigeria ...✍️