11/09/2026
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ɗaliban Najeriya za su fara samun megabyte 100 na data kyauta a kullum, domin shiga zaɓaɓɓun shafukan yanar gizo da dandamalin ilimi, daga ranar 1 ga Oktoba, 2026.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da shirin Zero-Rated Access to Educational Platforms and Content in Nigeria.
Shirin da Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, ke aiwatarwa tare da kamfanonin sadarwa da Ma’aikatar Ilimi, zai fara ne da ɗaliban makarantun sakandare da manyan makarantun gwamnati.
A ƙarƙashin shirin, ɗalibai za su iya amfani da data ɗin wajen shiga dakunan karatu na zamani, manhajojin koyarwa, tsarin gudanar da karatu da sauran dandamalin ilimi da gwamnati ta amince da su.
Gwamnati ta ce manufar shirin ita ce rage matsalar tsadar data, tare da tabbatar da cewa babu ɗalibin da za a hana samun ingantaccen ilimi na zamani saboda rashin kuɗin data.