09/05/2026
LOKUTA (16) WANDA ALLAH YAKE AMSA ADDU'O'IN BAYINSA.
01- Ko wane daya bisa uku (1/3) na dare ana amsa addu'a kamar yadda hadisi ya nuna hakan.
02- Ana amsa addu'a a tsakanin kiran sallah da tayar da iƙama, kamar yadda hadisi ya nuna hakan.
03- Ana amsa addu'a a ƙarshen kiran kowacce sallah ta farilla.
04- Ana amsa addu'a ya yin saukar ruwan sama, kamar yadda hadisai s**a nuna hakan.
04- Ana amsa addu'a a lokacin da aka yi sahu-sahu za a tafi yaƙin ɗaukaka kalmar allah ﷻ da kuma ya yin da aka yi sahun kafin a fara yaƙin, kamar yadda hadisai s**a nuna hakan.
05- Ana amsa adu'a a ranar juma'a a wani lokaci musamman ma bayan sallar juma'ar zuwa faɗuwar rana.
06- Ana amsa addu'a ya yin da za a sha ruwan zamzam tare da kyakykyawar niyyah, kamar yadda hadisi ya nuna.
07- Ana amsa addu'a a cikin sujjada, kamar yadda hadisi ya tabbata a cikin hadisi.
08- Ana amsa addu'ar wanda ya kwaikwayi irin addu'ar da Annabi ﷺ Yunusa ya yi, it ace: “La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin.”
09- Ana amsa addu'a a cikin tahiyyar sallah ta ƙarshe, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.
10- Idan Musulmi ya yiwa ɗan uwansa Musulmi addu'a ba tare da ya sani ba, ita ma karɓaɓɓiyar addu'a ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.
11- Addu'ar ranar arfa ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
12- Idan musulmai s**a haɗu wasu suna addu'a wasu suna cewa amin, ita ma wannan addu'ar karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.
13- Ana amsa addu'a a ya yin da mutum ya fuskanci Allah ﷻ da tsarkin zuciya, wato iklasi mai ƙarfi
14- Addu'a bayan an gama alwala, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.
15. Lokacin da aka gama karatun Alqur'ani ko wa'azi ko wata koyarwa ta ilimi. Shima lokacin karbar addu'a ne.
16. Lokacin da akaji zakara yayi chara. Shima lokacin amsar
addu'a ne kamar yazo a hadisi.
Allah ya amsa dukkan buqatun mu na alkhairi, na sharri kuma ya maida mana su na alkhairi.