16/05/2026
To kunji fa
Da ɗumi-ɗumi: “Ban taɓa yin nadamar cire tallafin mai ba” —Shugaba Tinubu
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai yi nadamar cire tallafin mai da kuma haɗa kasuwar canjin kuɗaɗen ƙetare wuri guda ba, yana mai cewa ci gaba da biyan tallafi “rayuwa ce ta ƙarya” a tattalin arzikin duniya na yanzu.
Tinubu ya faɗi hakan ne yayin taron Africa CEO Forum da aka gudanar a Kigali na ƙasar Rwanda, inda ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakan ne domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durƙushewa.
Shugaban ya ce:
“Rayuwa ce ta ƙarya ka yi tunanin za ka ci gaba da biyan tallafi a cikin tattalin arzikin duniya.”
Ya ƙara da cewa tsarin kasuwar canjin kuɗi guda ɗaya ya taimaka wajen rage tangarɗa da kuma bai wa masu zuba jari kwarin gwiwa.
Sai dai tun bayan cire tallafin mai da sauya tsarin dala, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa, hauhawar farashi da wahalar tattalin arziki.
Wasu na ganin matakan sun zama dole domin gyara tattalin arziki, yayin da wasu ke zargin gwamnati da ƙara jefa talakawa cikin ƙunci.
Shin kai kana goyon bayan cire tallafin mai da Tinubu ya yi, ko kuwa kana ganin ya jefa mutane cikin wahala?