Dr Ghali Panda Media Crew

Dr Ghali Panda Media Crew Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dr Ghali Panda Media Crew, Media/News Company, Gaya local govt, Gaya.

KWANKWASIYYA 🛑🛑🛑🛑🛑🛑
06/09/2025

KWANKWASIYYA 🛑🛑🛑🛑🛑🛑

Cikin Hotuna:Jam’iyyar NNPP ta gudanar da taron NWC inda aka tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi zaɓen 2027 tare d...
28/08/2025

Cikin Hotuna:

Jam’iyyar NNPP ta gudanar da taron NWC inda aka tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi zaɓen 2027 tare da tsara mafita ga ‘yan jam’iyya da kuma alkiblar da ya dace a dosa.

Taron ya samu halartar jagoran Kwankwasiyya na ƙasa, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, tare da mataimakin gwamnan jihar Kano, Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, da kuma zababbun ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da aka zaɓa karkashin inuwa ta jam’iyyar NNPP.

Shugabannin jam’iyyar NNPP na ƙasa da na jihohi ne s**a jagoranci taron, inda aka cimma matsaya cewa za a ci gaba da tafiya a cikin jam’iyyar NNPP, bisa hujjar cewa dukkan ‘yan jam’iyya sun nuna gamsuwa da ita. Sai dai hakan bai hana buɗe ƙofa da bai wa sauran jam’iyyu damar tattaunawa da haɗin kai a bisa tsari na siyasa ba.

Alhamdulillah 🙏Cikin ikon Allah jiya Lahadi *10/08/2025* Mai girma Ɗan majalisar tarayya Mai wakiltar ƙananan hukumomin ...
11/08/2025

Alhamdulillah 🙏

Cikin ikon Allah jiya Lahadi *10/08/2025* Mai girma Ɗan majalisar tarayya Mai wakiltar ƙananan hukumomin Gaya/Ajingi/Albasu *Hon Dr Ghali Mustapha Tijjani Panda* ya ƙaddamar da Shirinsa na Tallafin Takin Zamani Guda 1800 ga Manoma yankin Gaya/Ajingi/Albasu.

Hon Sunusi surajo kwankwaso da jagoran karamar hukumar Gaya Commr Baffa sani Gaya da jagoran karamar hukumar Albasu Hon Ƙasim Batayya jagororin ƙaramar hukumar Ajingi Alh. Amadu da Alhaji Audu ɗan gwangwan, shugaban ƙaramar hukumar Albasu da shugaban ƙaramar hukumar Ajingi Shugabannin jam'iyya sune s**a jagoranci Ƙaddamar da Wannan shiri.

Bayan Ƙaddamar da Tallafin Takin Zamani *Hon Dr Ghali* ya Gwangwaje Ƴan gwagwarmaya mutum 8 da kyautar sabbin babura Masu ƙafa 2.

Muna roqon Allah yasakawa Mai girma member da Alkhairi, Allah ya cigaba Da Temakonsa cikin dukkanin Al'amuransa damu baki daya 🙏

✍️ Bashir Ɗanzarewa Gaya.
Matemaki na musamman ga Hon Dr Ghali.

Alhamdulillah 🙏    Yau 07/08/2025 Mai Girma Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu *Hon. Dr. Ghali M. Tij...
07/08/2025

Alhamdulillah 🙏

Yau 07/08/2025 Mai Girma Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu *Hon. Dr. Ghali M. Tijjani Panda* ya biyawa Ɗaliban Da yake ɗaukar nauyin karatunsu ƴan 1st batch su (30) kudin makaranta na shekara ta 2 biyu waɗanda suke karatu a School of Nursing, Kano, ta hannun Wakilinsa Dr Tukur Panda

*Dr. Ghali Panda scholarships scheme**

(1st Batch)

1. Amina Umar
2. Fatima sulaiman inuwa
3. Zainab abdulmanaf
4. Hauwa Mahmud
5. Aisha abubakar
6. Zainab Yusuf madaki
7. Bilkisu Abubakar ishaq
8. Ummusalma aliyu adam
9. Suwaida Umar
10. Hafsat Abdullahi
11. Ummulkhairi Muhammad Nuhu
12. Aisha Kabir
13. Fiddausi sagir
14. Maryam baffah gaya
15. Khadija Abdulkadir
16. Hasiya baffah gaya
17. Amina Ahmad Muhammad
18. Aisha Ridwan Muhammad
19. Ummulsalama Muhammad
20. Bilkisu Usman Nasir
21. Saadatu Abdulmalik
22. Sadiya Tasiu Abdullahi
23. Fatima Adamu isa
24. Asma'u Lawan Dawaki
25. Maryam Ridwan Umar
26. Nasiba balarabe
27. SADIYA Musa ALIYU
28. Hafsat SHEHU Hassan
29. Zainab Mahmud
30. Khadija Uba

✍️Bashir Ɗanzarewa Gaya

Muna godiya Dr. 🙏🙏🙏
03/08/2025

Muna godiya Dr. 🙏🙏🙏

Gangaran kafi Gwani 🛑🛑
02/08/2025

Gangaran kafi Gwani 🛑🛑

 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ABUBUWA GOMA 10 DA SUKE SA MUTUWAR ZUCIYABabban Tabi'i Ibrahim bin Adhama (R.H), wata rana y...
01/08/2025



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ABUBUWA GOMA 10 DA SUKE SA MUTUWAR ZUCIYA

Babban Tabi'i Ibrahim bin Adhama (R.H), wata rana yazo wucewa ta kasuwar Basra, sai mutane s**a taru akansa s**a kewayeshi, sai s**a ce masa ya Baban Ishaq, Lallai Allah yana cewa a cikin littafinsa "KU ROKE NI ZAN AMSA MUKU" amma munayi ba'a amsa mana, sai ya basu amsa da cewa: zuciyoyinku ne s**a mace daga abubuwa guda goma (10)

1. Kun san Allah amma baku ba shi hakkinsa.

2. Kuna karanta Al-'Kur'ani amma baku aiki dashi.

3. Kuna riya cewa kuna son Manzon Allah (S.A.W) amma kuna barin sunnar sa.

4. Kuna cewa lallai shaidan makiyin kune amma bakwa saba masa.

5. Kuna cewa lallai ku kuna shaukin son shiga Al-jannah amma bakwa aikin shigarta

6. Kuna cewa lallai ku kuna tsoron wuta amma bakwa aikin guje mata.

7. Kuna cewa lallai mutuwa gaskiya ce amma bakwa mata tanadi.

8. Kuna shagaltuwa da sa ido akan laifukan mutane amma kuna mantawa da naku

9. Kuna cin Ni'imomin Allah (S.W.A) amma bakwa gode masa.

10. Kuna binne matattunku amma bakwa daukar izina dasu.

Allah Ya Kara Bamu Ikon Kiyaye Dokokinsa Bijahi Rasulillahi (S.A.W).

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Safiya.

*Jumu'at Mubarak*

Rayuwar duniya chike take da kalubale kala-kala, yau kana farin chiki gobe kishiyarsa kada ka ruɗe lokacin da wani abu m...
31/07/2025

Rayuwar duniya chike take da kalubale kala-kala, yau kana farin chiki gobe kishiyarsa kada ka ruɗe lokacin da wani abu mara daɗi na rayuwa ya tunkaro ka. ka sani nutsuwarka a wannan hali shi ne kashi hamsin na maganin matsalarka".

Ya ubangiji ka kara mana nutsuwa ka yaye mana duk wata damuwa.

Allah yaƙara yi mana ruƙo Da hannayenka Hon Dr Ghali Mustapha

Allah yayi ruƙo da hannayenka Mai girma member Hon Dr Hon Dr. Ghali Mustapha Tijjani
30/07/2025

Allah yayi ruƙo da hannayenka Mai girma member Hon Dr Hon Dr. Ghali Mustapha Tijjani

Assalamu Alaikum  🙏Ba shakka Muna ta ganin  Rubutun ƴan'uwa daban-dabaan na ƙorafi tare da shawarwari ga Mai girma Hon D...
30/07/2025

Assalamu Alaikum 🙏

Ba shakka Muna ta ganin Rubutun ƴan'uwa daban-dabaan na ƙorafi tare da shawarwari ga Mai girma Hon Dr Ghali Mustapha

Da farko Muna ƙara bawa ƴan'uwa haƙuri, ba don komai ba Sai domin Mun san mafi yawa daga masu ƙorafi masoya ne na haƙiƙa, kuma ƙaunace da soyuwar harkar ta saka su ƙorafin kira azo a gyara.

Muna son ƴan'uwa su sani, tuni muka miƙa dukkanin shawarwarin ƴan'uwa ga Mai girma Member, kuma ya bamu tabbaci akan irin kyawawan tsare-tsaren da yayi na kawo cigaba ga matasa da yankunan Mu masu albarka Nan ba da Daɗewa ba.

Babbar shawarar da nake so na bawa ƴan'uwa shi ne Mu dage da yiwa shugabannin mu addu'a, mudena cin mutunci ko aibata Shugabanni koda Muna da banbancin ra'ayi, haka muma Matasa mudena cin mutuncin juna Sabo da siyasa Alhali ba ita ce ta haɗa Mu ba.

Muna ƙara baku haƙuri ƴan'uwa Amadadin Mai girma Member 🙏

✍️ Bashir Ɗanzarewa Gaya
Matemaki na Musamman ga Mai Girma Ɗan majalisa🙏

Allah yazama Gatanka 🤲Allah ya shiga lamuranka 🤲Allah yaƙara yin ruƙo da hannayenka 🤲Allah yaƙara kareka Daga sharrin ma...
29/07/2025

Allah yazama Gatanka 🤲

Allah ya shiga lamuranka 🤲

Allah yaƙara yin ruƙo da hannayenka 🤲

Allah yaƙara kareka Daga sharrin masu sharri,🤲

Allah yabaka ikon sauke Nauyin Al'ummar Gaya, Ajingi, Albasu.

Hon Dr Ghali Mustapha

28/07/2025

Address

Gaya Local Govt
Gaya

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr Ghali Panda Media Crew posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share