Arewa Ayau

Arewa Ayau Gaya Local Government

Da dumi dumiGwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Litinin amatsayin ranar hutun a duk fadin Jihar, bisa alhinin rasuwar '...
01/06/2025

Da dumi dumi

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Litinin amatsayin ranar hutun a duk fadin Jihar, bisa alhinin rasuwar 'yan wasan guje guje da tsalle tsalen Jihar 22, akan hanyar su ta dawowa daga Jihar Ogun a ranar Asabar.

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN Hatsari ya rutsa da tawagar wasanni na Kano a Hanyar komowa daga gasar National Spo...
31/05/2025

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN

Hatsari ya rutsa da tawagar wasanni na Kano a Hanyar komowa daga gasar National Sports Festival da aka gudanar a jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne lokacin da motar, wadda ke dauke da mutane kusan 35, ta kife daga wata gada, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin fasinjojin.

An garzaya da waɗanda s**a jikkata zuwa babban asibitin Kura domin samun kulawar gaggawa.

Cikin hotuna: Taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo mai suna "Being...
13/05/2025

Cikin hotuna: Taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo mai suna "Being True to Myself" wato "Fadawa Kaina Gaskiya".

Waɗanda s**a halarci taron sun haɗa da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da tsofaffin mataimakan shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Namadi Sambo da tsofaffin shugabannin majalisar dattawa, Ken Nnamani, Paius Ayim.

Sauran su ne, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya da na Jigawa, Umar Namadi da na Plateau, Caleb Mutfwang da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu.

SANARWA. JIRGIN FARKOAlhazan kananan Hukumomin Doguwa, Tudun Wada, Bebeji, Garun Malam, Tofa, Ajingi, Wudil, Gaya, Rimin...
13/05/2025

SANARWA. JIRGIN FARKO

Alhazan kananan Hukumomin Doguwa, Tudun Wada, Bebeji, Garun Malam, Tofa, Ajingi, Wudil, Gaya, Rimin Gado, Madobi da Kabo su fito sansanin Alhazan jihar Kano domin tafiya kasa mai tsarki a Yau Talata 13 ga watan May 2025 da misalin ƙarfe takwas na dare (8:00pm).

Ana bukatar kowanne Alhaji da Hajiya su fito sanye da uniform da jakunkunan da aka basu.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!Mai girma shugaban ƙaramar hukumar Gaya Hon Mahmoud Gaya Tajo Sani yana sanarda ɗaliban ƙar...
13/05/2025

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Mai girma shugaban ƙaramar hukumar Gaya Hon Mahmoud Gaya Tajo Sani yana sanarda ɗaliban ƙaramar hukumar Gaya cewar Kano state college of health science and technology sun buɗe admission ranar litinin 12-05-2025 12:00am zasu rufe ranar Lahadi 18-05-2025 11:59am, ga makarantun da za suyi admission ɗin:

1. School of health technology Kano.
2. School of health technology Bebeji.
3. School of hygiene Kano.

https://kascohsat.edu.ng ga link ga masu sha'awa, idan kayi apply sai ka cire slip ɗin kayi photocopy ka kawo local government secretariat ta hannun Rt. Hon Speaker Nazifi Sabiu Kalahaddi

Sen Abdullahi Ubale Gaya
Talata 13-05-2025.

Certificate in Community Health (JCHEW) 2-Years OND Community Health (CHEW) 3-Years ND Health Information Management (HIM) 2-Years OND Health Information Management Technician (HIMT) 3-Years OND Biomedical Engineering Technology (BET) 3-Years…

Gwamnan kano Abba K Yusuf ya bada umarnin ɗaukar security guards guda 17,600 domin kula da makarantun gwamnati.
12/05/2025

Gwamnan kano Abba K Yusuf ya bada umarnin ɗaukar security guards guda 17,600 domin kula da makarantun gwamnati.

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya je ziyarar taʼaziyyar rasuwar ɗan uwan Alh. Murtala Sule Garo.Hotuna daga Isah Mu...
12/05/2025

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya je ziyarar taʼaziyyar rasuwar ɗan uwan Alh. Murtala Sule Garo.

Hotuna daga Isah Muhammad Salisu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin tantance ma'aikatan wucin gadi na Besda domin ɗaukar su aiki.
12/05/2025

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin tantance ma'aikatan wucin gadi na Besda domin ɗaukar su aiki.

Yadda Akayi Shagalin Bikin Amarya Ayshatul Humairah Da Angonta Na Amana Alhaji Dauda Kahutu Rarara a Daren Jiya a Birnin...
12/05/2025

Yadda Akayi Shagalin Bikin Amarya Ayshatul Humairah Da Angonta Na Amana Alhaji Dauda Kahutu Rarara a Daren Jiya a Birnin Kano.

Taron Ya Sami Halartar Manyan Baki Irin Su Tsohon Gwamna Katsina Kuma Shugaban Hukumar TET FUND Na Kasa Rt. Hon. Aminu Bello Masari Da Gwamnan Jahar Gombe Kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Alhaji Inuwa Yahaya Da Kwamishinonin Jahar Katsina Da Kwamishinonin Jahar Gombe Da Kwamishinonin Jahar Jigawa Da Masu Bawa Gwamna Shawara Na Jahohin Jigawa Da Gombe Da Katsina.

Sannan Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Akan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu Ya Aiko Wakilinsa Wajen Wannan Shagalin Bikin.

Karamin Ministan Tsaro Da Babban Ministan Taro Suma Duk Sun Aiko Da Wakilansu Wajen Shagalin Wannan Bakin.

Mataimakin Shugaban Sanatocin Nigeria 🇳🇬 Sanata Barau Jibrin Maliya Shima Ya Aiko Da Wakilinsa Wajen Wannan Shagalin Bikin.

Sannan Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam Shima Ya Aiko Da Wakilinsa Wajen Wannan Shagalin Bakin.

Alhamdulillah Anyi Taro Lafiya An Gama Lafiya.
Allah Ka Dauwamar Da Zaman Lafiya Tsakanin Amarya Da Ango...🤲-🤲

Rabi'u Garba Gaya
Media Aide To Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara.

Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso, Ph.D., FNSE, ya karɓi digirin digirgir na girmamawa daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko ...
10/05/2025

Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso, Ph.D., FNSE, ya karɓi digirin digirgir na girmamawa daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, waccce akafi sani da Kano University of Science and Technology, Wudil. Ragowar wanda aka bawa sun haɗa da:

Alhaji Dahiru Barau Mangal
Engr. Prince Arthur Ikpechukwu Eze, OFR
Barr. Ahmad Adeniyi Raji, SAN
Alhaji Mustapha Ado Muhammad

Jagoranmu abin alfaharinmu shine wanda yayi:

1. Shugaban ƙungiyar ɗaliban ta KADPOLY
2. Tsohon ma'aikacin gwamnati tsahon shekaru 17
3. Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta ƙasa (1992)
4. Ɗan komitin gyaran kundin mulkin Nigeria (1994-1995)
5. Tsohon gwamnan jihar Kano sau biyu (1999-2003 da 2011-2015)
6. Babban ministan tsaro Nigeria (2003-2007)
7. Ɗan komitin sulhun Dafur da Somalia (2003-2007)
8. Sanatan ƙasar Nigeria (2015-2011)
9. Takarar zangon farko na tsayawa shugaban Nigeria (2015 da 2019)
10. Jagoran NNPP kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa (2023)
11. Shine wanda ya ƙirƙiro tagwayen jami'o'in nan na Kano KUST (2000 & 2012)
12. Shine babu gwamnati yakai manyan Scholars su 370 zuwa ƙasashen waje na Dubai, India and Sudan ta gidauniyar Kwankwasiyya
13. Ya kuma kafa ƙungiyar nan ta Kwankwasiyya mai albarka.

A jawabinsa, yace yayi abubuwa da yawa na cigaban al'umma, amma yana so jama'a su tuna dashi a matsayin sa na wanda ya ƙirƙiro tagwayen jami'o'i a Kano. Sannan ya sadauƙar da digirin ga al'ummar Kano, Nigeria da kuma masu son cigaban jami'a a duk inda suke. Madugu kenan, Allah Ya kara lafiya, nisan kwana da ɗaukaka.

Ni dai Jagora ya burgeni ta hanyar kai matasa 370 zuwa ƙasar waje, ku kuma ta ina yafi burgeka?

Arewa Ayau.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya saki wasu fursunoni mata 8 daga gidan gyaran hali na Goron-Dutse, ta hanyar biya...
10/05/2025

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya saki wasu fursunoni mata 8 daga gidan gyaran hali na Goron-Dutse, ta hanyar biya musu tara da basuss**an da ake binsu.

Cikin waɗanda aka sako akwai mata masu juna guda biyu da mata masu shayarwa biyu.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne lokacin da ya kai ziyarar bazata gidan gyaran halin, tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce maƙasudin ziyarar gwamna Abba Kabir ita ce duba halin da fursunonin ke ciki tare da duba hanyoyin da gwamnatin jihar za ta tallafa wa jin daɗinsu.

Hikima Radio And Tv

Bulama ya roki a Bude idon wannan jami'in 😅Arewa Ayau.
10/05/2025

Bulama ya roki a Bude idon wannan jami'in 😅

Arewa Ayau.

Address

Gaya Local Government
Gaya

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Ayau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share