
18/07/2025
KARAMIN SU BABBAN SU š„
Mai Girma Zababbenn Shugaban Karamar Hukumar Wudil, Hon. Abba Muhammad Tukur (Talban Makaman Kano), ya dauki nauyin karatun dalibai 535 daga Karamar Hukumar Wudil a makarantu daban-daban da ke fadin jihar Kano.
An gudanar da taron bayar da shaidar tallafin karatun ne a harabar Jamiāar Kimiyya da Fasaha ta Wudil (KUST Wudil), inda aka bai wa daliban takardun shaidar daukar nauyin karatunsu.
Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, shi ne babban bako na musamman a wajen taron, tare da Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, da sauran jamiāan gwamnati.
A yayin jawabin sa, Hon. Abba Muhammad Tukur, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da karamar hukumar Wudil ke daukar nauyin karatun dalibai da yawa a lokaci guda. Ya ce wannan shiri yana daga cikin tsarin tallafawa alāumma da Kwankwasiyya Movement ke yi, musamman a fannin ilimi.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiwatar da irin wadannan shirye-shirye domin inganta rayuwar matasa da ci gaban alāumma.
An yi adduāar Allah ya ba dukkan mahalarta lafiya wajen komawa gidajensu, tare da yi wa shugaban karamar hukumar fatan karin nasara da dorewar jagoranci nagari.
Khatimu Kulkul
18 July 2025.