Channel Hausa24

Channel Hausa24 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Channel Hausa24, TV Channel, 1 Gumel Road Gezawa, kano, Gezawa.

SPONSORED A yau Dist. Sen. Saleh Adamu Kwaru* ya gudanar da taron tattaunawa da Daraktocinsa na Shiyyar Kano ta Tsakiya....
06/06/2026

SPONSORED
A yau Dist. Sen. Saleh Adamu Kwaru* ya gudanar da taron tattaunawa da Daraktocinsa na Shiyyar Kano ta Tsakiya. Daraktoci daga Ƙaramar Hukuma (LG) 12 ne s**a halarci taron, yayin da aka karɓi uzurin wasu mutum 3 da ba su sami damar halarta ba saboda wasu dalilai da ba za a iya kauce musu ba.
A yayin taron, ya ba su umarnin gaggawa na su fito da tsarin sake naɗa Masu Gudanarwa (Coordinators) na ƙungiyar 'Kwaru Support Organisation' (KSO), na dukkan Mazubun da ke yankunan nasu da nufin tsara da kuma fito da gagarumin goyon baya ga *H.E Dr. Nasiru Yusuf Gawuna* a takarar Sanata a Kano ta tsakiya.
Daga ƙarshe, taron ya cimma matsayar ɗagewa domin ci gaba da zama a mako mai zuwa don ƙarfafa waɗannan tsare-tsare.

01/06/2026

SPONSORED
A yammacin jiya ne, Dist Sen Saleh Adamu Kwaru ya shirya walima ga tawagar yakin neman zabensa na mazabu 11, domin gode musu kan tallata takararsa ta Majalisar Tarayya a karkashin NDC.

A wurin taron an kara haskaka cancantarsa, da jinjinawa kwarewarsa da kishin al'umma. A karshe tawagar ta lashi takobin cigaba da yada manufofinsa domin tabbatar da nasarar NDC a dukkan zabuka.

01/06/2026
NDC ta tantance Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa daya tilo na jam'iyyar Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban ...
20/05/2026

NDC ta tantance Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa daya tilo na jam'iyyar

Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya amince da Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa guda daya tilo kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Obi ya isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Talata tare da rakiyar Sanata Victor Umeh.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya gurfana a gaban kwamitin tantancewar karkashin jagorancin tsohon ministan ilimi, Sam Egwu.

Da yake magana bayan tantancewar, Egwu ya ce kwamitin ya gamsu da yadda Obi ya amsa tambayoyin da aka yi masa, yana mai cewa ya cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar zabe.

A cewarsa, kwamitin ya tabbatar da Obi a matsayin wanda ya cancanci shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben shekarar 2027.

Daga nan ne aka mika wa Obi takardar shaidar amincewa tare da fom din tsayawa takara mai lamba 001 na jam’iyyar.

A ranar Lahadi 17 ga watan Mayu ne Obi ya karbi fom din nuna sha’awa da na takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC kafin wa’adin farko da aka sanya.

Sai dai a ranar Litinin jam’iyyar ta kara wa’adin karbar fom ga sauran masu neman takara zuwa ranar 24 ga watan Mayu, tare da bayyana cewa karbar cikakkun fom daga wadanda aka tantance zai fara daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Mayu.

Duk da haka, jam’iyyar ta ce ba za a kara wa’adin karbar fom din takarar shugaban kasa ba domin tuni an rufe shi.

VOK HAUSA
20/05/2026

VOK HAUSA

Mutane biyu ne s**a mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Komsilga na kasar Burkina Faso, bayan wata bab...
18/05/2026

Mutane biyu ne s**a mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Komsilga na kasar Burkina Faso, bayan wata babbar mota da ke dauke da dabbobi ta kife, kuma dukkan dabbobin sun halaka.

18/05/2026

BARKA DA SAFIYA
YAN UWA MASU ALBARKA
YAYA KUKA TASHI A YANKIN KU

Ina mamakin Kwankwaso da ya dage shi dole sai ya tallata Peter Obi a ganin sa ai Peter Obi tainuwa daya zaiyi ya bashi k...
17/05/2026

Ina mamakin Kwankwaso da ya dage shi dole sai ya tallata Peter Obi a ganin sa ai Peter Obi tainuwa daya zaiyi ya bashi kujerar da yake tsoronsa yake.

Idan Kwankwaso zai gane ya gane babu yadda zaai Peter Obi ya karbi mulki kuma yai tainuwa daya ya sauka.

Idan baku sani ba ku sani Obi jira yake kawai ya sami dama, bama yan Nigeria ba har Kwankwason saiya matse karshe dole Kwankwaso ya fita daga jam'iyyar ya barshi yai abinda yaga dama, in zaku farka ku farka

Inji Bil'adama

Address

1 Gumel Road Gezawa, Kano
Gezawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Channel Hausa24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

l="false"> Add listing
  • Login
  • Subscribe

    We will notify you when anything happens in Gezawa.