16/03/2026
Dujiman Giade Foundation na ci gaba da nuna kulawa da tausayi ga al’umma ta hanyar rabon kayan Sallah ga marayu da marasa galihu a Ƙaramar Hukumar Giade, kamar yadda aka saba yi a duk shekara.
Wannan shiri yana daga cikin manufofin gidauniyar na tallafawa masu buƙata da kuma tabbatar da cewa yara marayu sun samu damar yin bikin Sallah cikin farin ciki da walwala kamar sauran al’umma.
Allah ya saka da alheri, ya ƙara ɗaukaka wannan gidauniya tare da albarkace duk wanda yake bada gudunmawa wajen ganin an cimma wannan kyakkyawan buri. 🤲