07/05/2024
Wlh wannan tsarin da FG ta kawo sai ya sake jefa Al'umma cikin mawuyacin hali, akwai yan kasuwan da suke transaction a rana sama da 100M, kenan fa naira 500K za'a cire masu na Cyber Levy hakanan a banza a wofi, taya kuke tunanin bazasu laftawa kayan su tsada ba..
Ni kaina dan karamin dan kasuwa kudin da za'a cajeni a rana dana lissafa wlh sun kai ayi lafiyayyen jari dasu.
Banki su kwashi kudinmu suje suyi kasuwanci su samu riba, sannan duk wata a cire mana Monthly Charges, sannan kuma itama yanzu Federal Government tace zata dinga cire 0.5% a cikin dukiyarmu da mukasha wuya muka tara.
Yanzu idan zakayi transaction ko zaka tura kudi naira 1M, FG zasu cire 5k daga cikin wannan 1M din naka, haka idan zaka tura 500K zasu cire 2,500, Idan 2M zaka tura zasu cire 10K, idan 3M katura za'a cire 15K, haka idan 100M zaka tura za'a cire maka 500K
Wai kudin za'ayi amfani dasu domin kula da tsaron kafar internet.
Me ake tsare mana a Internet din, komai mu mukeyi da kanmu, Hac-king nan idan akayi maka ka dinga fama da banki kenan, akan su taimaka maka.
Wallahi ko kwandala aka cire min bazan yafe ba, ba'a san ya kayi kasha wuya wurin neman kudinka ba, a tilasta maka a cire maka hakkinka.
Wannan zalunci ne, sanadiyyar wannan da yawa zasu rasa kasuwancinsu..
Copied: Salisu Abdurrazak Saheel