
31/03/2025
Na samu kiraye kiraye daga al’ummar yankina da ‘yan Najeriya da dama dangane da mummunan kisan gilla da aka yi wa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a Jihar Edo. Ina Allah wadai da wannan ta’asa, kuma na yi tir da wannan kisan gilla da aka yi wa wadannan bayin Allah.
Ina kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakin k**a wadannan azzalumai tare da tabbatar da cewa an hukunta su daidai da girman laifin da s**a aikata.
Najeriya ƙasa ce mai yalwar kabilu da addinai daban-daban. Saboda haka, dole ne mu zauna lafiya da juna, mu rungumi juna a matsayin ‘yan uwa domin ci gabanmu da zaman lafiyarmu.
Allah Madaukakin Sarki ya jikan wadanda s**a rasa rayukansu, ya ba su Aljannatul Firdaus. Allah ya ba iyalansu hakuri da juriya.
Insha Allah, za mu tabbatar da cewa an yi adalci, kuma wadannan azzalumai ba za su tsira ba.
Zan kuma gabatar da kudiri a zauren Majalisar Dattawa kan wannan lamari.
- Sanata Barau Ibrahim Jibrin
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai