29/12/2025
Masallacin Da Annabi Muhammadu SAW Ya Taba Yin Sallah A Cikinsa Dake Birnin Madina
Wadin Al-Farʿ yana kudu da birnin Madina Munawwara, nisan kimanin kilomita 120 a kan babban titin da ke tsakanin Madina da Makka.
Wadin Al-Farʿ yanki ne na noma, yawon buɗe ido da kuma tarihi. A da, hanya ce ta tsofaffin ayarin kasuwanci tsakanin Madina da Makka. Ya shahara da noman kowane irin dabino, inda a da yake da fiye da rijiyoyi hamsin (50) masu gudana da ke shayar da dubban dabino. Sai dai da tafiyar lokaci, yawancin waɗannan rijiyoyi sun lalace, kuma abin da ya rage su ne rijiya uku kacal: Ayn Al-Madiq, Ayn Abi Dibaʿ, da Ayn Umm Al-ʿIyal.
Masallacin Al-Burūd (Masallacin Annabi saw)
Masallacin Al-Burūd yana a Wadin Al-Gharb, a ƙauyen Al-Madiq daga arewacin yankin. Mutanen yankin suna saninsa da sunan Masallacin Annabi saw. Yana ɗaya daga cikin masallatai uku da Annabi SAW ya yi sallah a cikinsu.
Bayanin Hukumomi da Masana Tarihi
Gwamnan Wadin Al-Farʿ, Mubarak Al-Muraqi, ya bayyana cewa Masallacin Al-Burūd sananne ne a wajen mutanen yankin da sunan Masallacin Annabi SAW, kuma yana daga cikin muhimman wuraren tarihi a yankin. Yana cikin Wadin Al-Gharb a ƙauyen Al-Madiq, ɗaya daga cikin ƙauyukan da ke ƙarƙashin gundumar. Ya ƙara da cewa yankin na ɗauke da wuraren tarihi masu shekaru da dama; wasu har yanzu suna nan ana kula da su ta hannun al’umma da kuma sa ido daga hukumomi, yayin da wasu ba a ganin komai face ragowar alamominsu.
Marubuci Abdul-Muttalib Al-Badrani ya ce: Masallacin Al-Burūd na daga cikin muhimman wuraren tarihi a Al-Madiq, Wadin Al-Farʿ. Yana a kan tsaunin Wadin Al-Gharb gaba ɗaya. Yana ɗaya daga cikin masallatan da Annabi saw ya yi sallah a cikinsu lokacin da ya ratsa Wadin Al-Farʿ. Ya ƙara da cewa wasu mutane sun canja sunansa zuwa Al-Barīd (ƙaramin Al-Burūd), amma har yanzu mutanen yankin na kiran sa Masallacin Annabi SAW, kuma har zuwa kwanan nan suna gudanar da Sallar Idi a cikinsa.
Allah SWT ya sanya alkhairi, ya bamu albarkan wannan Masallaci, Amiin Yaa ALLAH
Daga: Fityanu Islamic Centre
29, December 2025