15/04/2025
TAKAITACCEN TARIHIN MOULANA PROFESSOR IBRAHIM AHMAD MAQARI.
An haifi MOULANA Farfesa Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari a ranar 15 ga Satumba, 1976, a birnin Zariya, Jihar Kaduna, Najeriya. Ya fara karatun firamare a Jihar Katsina a shekarar 1987, inda ya haddace Al-Qur'ani mai girma yana dan shekara 13 zuwa 14 a Madarasatul Faidatul Islamiyya ta gidan Sheikh Yahuza a Zariya.
Bayan kammala karatun firamare, ya ci gaba da karatun sakandire a Kwalejin Nazarin Larabci ta Jama'atu da ke Zariya, Jihar Kaduna. Daga nan ya tafi Jami'ar Al-Azhar da ke Alkahira, Masar, inda ya kammala digiri na farko a shekarar 1999. Ya samu digiri na biyu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2005, sannan ya kammala digirin digirgir (PhD) a Jami'ar Bayero da ke Kano a shekarar 2009.
Farfesa Maqari ya fara aikin koyarwa a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, a shekarar 1999. Daga baya, ya koyar a Jami'ar Jihar Kaduna a matsayin babban malami a shekarar 2010, sannan ya koma Jami'ar Bayero Kano, inda ya zama farfesa a sashen Larabci da Harsuna. A shekarar 2012, an nada shi babban limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Baya ga ayyukansa na ilimi, Farfesa Maqari ya kafa cibiyar Tazkiyyah Educational Resource Center da ke Abuja, tare da makarantu kusan 30 na Qur'ani da Islamiyya a fadin Najeriya.
Reliable and trusted information, entertainment and movies.