
31/07/2025
RAMIN MUGUNTA!
*
MUGUWAR GASA!
*
Babi na 98: *Ku kamo shi!!!*
*
Wannan chapter WhatsApp group ne s**a dauka muku nauyin ta. Kuyi joining domin hada karfi da karfe ana samun chapter kullum:
👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/FbMgmm5lU8vKPQixKFVcyj?mode=ac_t
*
*Wannan littafin sadaukarwa ne ga Fatima Umar Muhammad*
*
Marubucin ✍️RUHIN JARUMTAKA ✍️
*
✍️✍️✍️ Marubucin littafin - Muhammad Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
*
Mamaki haɗe da bugun zuciya sau uku-uku ya baibaye Aiyini. Wannan babbar alama ce da zata nunawa mutum cewa, Aiyini ta san wannan sabuwar fasaha wadda Arshan yayi amfani da ita a yanzu.
A daƙiƙa ta gaba Arshan ya juye ya dawo ainihin mutum mai tsoka da jini. Arshan ya kwarara uban ihu wanda ba zaka kwatanta shi da komai ba, sai ihun fusataccen mutum.
Arshan ya sake afkowa Aiyini s**a ci gaba da fafatawa. Fuskar Aiyini ɗauke da gagarumin mamaki wanda yafi na kowanne lokaci ta fara kare hare-haren Arshan, ba tare da ta mayar masa da martani ba.
A wannan lokaci a cikin zuciyarta tunanin guduwa take yi saboda kashe Arshan bai da wani amfani a wajen ta.
Ya zamo mata dole ta koma gida ta bayar da labarin Arshan.
Sai da wannan kalmar ta ɗan tsaya mata a rai, wai kashe Arshan?!
Shi kuwa Arshan ƙoƙarin cika umarnin da Lasirina Ajamen ta bashi yake yi. Tabbas yaji muryar Lasirina Ajamen tana yi masa gargaɗi akan yayi gaggawar mallakar wannan sarƙa kuma ya koma wajen masoyiyarsa kafun wani mummunan abu ya faru da ita.
Arshan yana cikin wannan hali, yaga Aiyini ta fara yin baya-baya. Da farko bai gane abinda take nufi ba, ya ɗauka duk a cikin shiri ne. Amma bayan ɗan lokaci sai ya gano cewa, ƙoƙarin tserewa take.
Arshan na fuskantar haka ya fara ƙoƙarin dakatar da ita.
Aiyini ta sake tashi sama ta dira akan iska. Tana daga saman ta sake turowa Arshan irin wannan baƙar guguwa.
Arshan ya juye ya koma walƙiya. Walƙiyar ta ratsa ta cikin wannan guguwa kuma ta fice, ba tare da guguwar tayi mata komai ba.
Arshan yana fitowa daga cikin walƙiyar, ya kirawo ainihin ɗalasimin takobin Sikaí.
“[Sikaí]” inji Arshan.
Nan take sararin samaniya ta fara rawa. Wata irin walƙiya ta cika sararin samaniya gaba ɗaya. Babu abinda mutum zai gani, idan ya ɗaga kansa da ya wuce wannan walƙiya.
Takobin Sikaí ta ratso cikin walƙiyar ta taho da gudu ta dira akan hannun Arshan.
A wannan lokaci sinadaran walƙiya suna ta yawo a cikin jikin Arshan tamkar jinin jikin sa.
Aiyini tana ganin wannan abu dake shirin faruwa, ta fasa guduwa ta tsaya.
Ko babu komai ita 'yar ƙabilar Jorash ce. Kuma a yadda take ikirari ita 'ya ce a wajen Babban Sarki Dur'hamu.
Arshan yana ganin wannan budurwa ta juyo ta fuskance shi sai ya cika da tsananin farin ciki.
Aiyini ta buɗe hannayenta biyu take ta dira ƙasa akan turba. A daƙiƙa ta gaba ta shafi tufafin dake jikinta da hannunta guda.
Nan take tufafin s**a juye s**a koma baƙaƙe ƙirim. Duk bayan daƙiƙa sai kaga tufafin s**a ƙara duhu, duhu abun tsoro da firgitarwa.
Fatar jikin Aiyini ta fara haske da sheƙi tamkar wata daren goma sha-biyu.
Arshan ya haɗe gira. Wai tana nufin tun farko da s**a fara fafatawa bada ainihin ƙarfinta take yaƙar sa ba?
Wani guntun murmushi Aiyini tayi wanda ba zaka fassara shi da komai ba, sai na fidda raini.
Ƙwayar idanun Aiyini ta fara komawa jajawur. Kai kace duk bayan daƙiƙa sake hurata ake.
Tsantsar kafiya, ƙarfin iko da buwayar masu mulki ya cika waɗannan idanu.
Tabbas inda ace akwai wasu mutanen daban a wannan waje da tuni sun zube a gaban wannan budurwa suna ta mubaya'a ga waɗannan maɗaukakan idanu nata.
Arshan yaga gashin kan Aiyini ya ƙara tsaho tamkar wanda ake jan sa. Gashin ya tafi ƙasa da gudu kuma ya shige cikin ƙasar dake wannan daji.
Ƙasar dajin gaba ɗaya tayi girgiza na tsahon daƙiƙa biyu kacal. Ba don Arshan ya lura ba da abu ne mawuyaci ya gane hakan.
“ASÉN X. AJAMEN!
“Mene ne abinda ya kawo ka duniyar mu?!”
Muryar Aiyini ta daki kunnuwan Arshan. Saɓanin yadda ta saba yi masa da farko.
A wannan lokaci akwai tsananin ƙarfin iko da sirrin nauyi a cikin muryar ta. Tabbas inda kunnuwan ƙaramin hatsabibi muryar ta shiga da tuni kunnuwansa sun fashe, jini ya fara zubowa.
To, amma duk wannan bai dami Arshan ba. Babban abinda ya bashi mamaki shi ne, jin ta kira shi da suna: Asén X. Ajamen.
Ba don Arshan ya taɓa wannan sarƙa ba da cikin sauƙi zai yi musun wannan suna saboda bai ma taɓa jin sunan ba, sai yau ɗin nan.
To, amma duk da haka zuciyar Arshan ta yarda cewa, shi ne Asén X. Ajamen. Duk da cewa shi kansa bai da cikakkiyar amsar wannan suna.
Arshan yayi gaggawar kawar da wannan tunani daga ransa. Muryar sa na fita ɗaiɗai kuma cike da nutsuwa da lissafi ya mayarwa Aiyini amsa.
“Ku 'ya'yan Hamu ku bani sarƙar da nazo nema!”
Aiyini ta ɗan yi shuru tana kallon wannan sarƙa dake wuyanta. Budurwar ta tuno yadda aka yi ta mallaki wannan sarƙa.
“Hmm!” tayi ajiyar zuciya cikin tsananin nutsuwa. Arshan ya nemi abinda yafi komai daraja a wajen ta.
Babu buƙatar ta bashi amsa. Kawai ɗaga ƙafarta guda tayi ta daki iska da ita.
Wani ƙatoton yanka ya bayyana a gabanta. Kai kace saran takobi-mai-tafiya aka ɗauko aka sari iska da ita. Sai da aka bari iskar ta tsage sa'annan aka aikowa shi Arshan.
Wani ƙaramin rami ya bayyana akan iska kuma ya yiwo kan Arshan da gudu. Tun kafun ya ƙaraso gaban Arshan yake ta haɗiye duk abinda yake shiga gabansa.
Abubuwan sun fara daga iska zuwa komai da komai.
A daƙiƙa ta gaba Arshan ya sari iska da takobin sa. Wani abu ya fice daga takobin k**ar tsuntsu mai fuka-fuki. Waɗannan hare-hare guda biyu suna haɗuwa da juna iska ta dare gida biyu.
A fusace Arshan ya ɗaga takobin Sikaí sama. Walƙiyar dake ta sukuwa a cikin sararin samaniya ta fara dunƙulewa a waje guda. Bayan ɗan lokaci walƙiyar ta samar da wani ƙatoton layi guda ɗaya na walƙiya. Kai kace bishiyar dabino ce saboda tsabagen kauri.
Ƙatoton layin ya taho da gudu ya haɗe da takobin Arshan, take takobin ta fara haske.
Arshan ya nuna Aiyini da wannan takobi. Nan take wannan ƙatoton layi na walƙiya yayi kan budurwar da gudu.
Tufafin dake jikin Aiyini s**a fara ƙonewa suna narkewa saboda tsananin zafin dake fitowa daga cikin wannan walƙiya.
Sai dai itama ba'a bar ta a baya ba. Tuni ta girgiza gashin kanta. Gashin kan ya tarwatse a cikin iska.
Kasancewar gashin a haɗe yake da ƙasar wannan daji yasa wani kaso na ƙasar shima ya warwartsu.
Ƙasar ta koma dunƙule-dunƙule. Cikin ƙiftawar ido fiye da dunƙule goma s**a haɗu a waje guda s**a samar da wani ƙatoton bango.
Bangon ya shiga tsakanin Aiyini da wannan walƙiya ta Arshan.
Dukkansu s**a zubawa abinda yake faruwa idanu. Cikin ƙasa da daƙiƙa goma walƙiyar ta daki wannan bango.
Kai inda ace mutum yana tsaye a wannan waje da tuni ya kurumce saboda masifaffen ƙaran da ya tashi sama. Kamar faɗowar aradu guda arba'in a lokaci guda.
Wannan daji yayi wata mahaukaciyar girgiza. Babu shiri ƙura ta tashi sama ta turnuƙe ko'ina.
Walƙiyar dake sararin samaniya ta fara tsatstsagewa tamkar zata tarwatse.
Jini ya fara zubowa daga bakin Arshan da hancinsa a karo na biyu saboda wannan mummunan gamo da s**a yi.
A ɓangaren guda itama Aiyini abinda yake faruwa da ita kenan. Tuni jini ya fara yoyo daga bakinta.
Jini na ɗiga akan ƙasa. Wani saƙo ya shigo allon ruhin Aiyini. Babu wanda yasan abinda s**a tattauna da koma wane ne.
Shi kuwa Arshan tunanin yadda zai tsinke wannan sarƙa daga wuyan Aiyini yake yi a wannan lokaci.
Bayan komai ya gama lafawa Arshan yayi arba da yadda ita kanta Aiyini ta jikkata sai ya cika da farin ciki.
Ko babu komai hakan zai taimaka masa sosai da sosai.
Wannan hari da Arshan yayi amfani da shi yanzu, hari mai matuƙar tsada. Shi kansa harin yana cinye sinadari ɗari nan take.
Saboda haka zaka iya cewa, Arshan ba zai sake maimaita irin wannan hari a yanzu ba. Saboda bai da isasshen sinadari.
“GIRGIZAR ƘASA!” inji Aiyini.
Wani haske ruwan ƙasa ya fito daga bakinta ya shige cikin gashin kanta. A hankali hasken ya rinƙa yin ƙasa har ya shige cikin wannan sahara da ta mamaye wannan daji.
Arshan yaji ƙasar tayi wani irin motsi. Kafun ya sake ankara tuni ta fara girgiza tana farfashewa tana samar da manya-manyan ramuka.
Nan take ta fara zaizayewa tana haɗiye dukkan abinda ke samanta. Arshan ya dakawa Barbossa tsawa.
Take Barbossa yayi gaggawa fitowa daga wajen da yake ɓoye kuma ya ɗauki Arshan a gadon bayansa.
Zuwa yanzu Aiyini ta daina yiwa Arshan kallon komai sai hatsabibi. Duk wannan fafatawa da s**a yi, idan ka tuna cewa a cikin doron ƙasa ta farko suke sai kayi mamaki.
Wasu baƙaƙen mutum-mutumi waɗanda aka samar daga baƙar ƙasa s**a fara fitowa daga cikin ramukan da wannan girgizar ƙasa ta haifar.
Sai dai Arshan bai da lokacin ɓatawa wajen fafatawa da mutum-mutumi a wannan karon.
Cikin jimami wata murya ta yiwa Arshan magana a cikin allon ruhin sa.
“Ka tabbata zaka aikata abinda kake tunani!” zazzaƙar murya ce k**ar ta mace.
Arshan ya gyaɗa kai, kafun ya furta.
“Sikaí turu Andev!” Arshan yayi magana cikin wani tsohon yare wanda hatta waɗanda suke jin Dahamísh zaiyi wahala su gane abinda ya faɗa.
Idanun Arshan na dama wanda yake ɗauke da hoton tauraro Sairanàm ya fara zubar da jini. Duk da cewa zogi yana ratsa Arshan amma bai damu ba.
Zanen tauraro Sairanàm ya bayyana akan karfen takobin Sikaí. Jikin Arshan ya fara juyewa yana komawa walƙiya.
Jikin sa yana gama komawa walƙiya, Arshan ya kirawo fasahar sa ta Kabancan.
Walƙiya idan ta haɗu da sauri tafi ƙarfin idanu su ga abinda zai iya faruwa.
Aiyini tana tsaye bata san abinda ke faruwa ba, taji an shaƙo ta ta baya. Arshan yasa hannun sa ya tsinke sarƙar dake ɗaure a wuyan Aiyini.
Sarƙar tana tsinkewa wani mugun jiri ya ɗebi Aiyini. Kawai ta sulalo ƙasa sumammiya.
Arshan ya damƙe wannan sarƙa da kyau, yana jiran shima abinda zai faru gare shi saboda abinda ya aikata yanzu-yanzu.
Ganin Arshan ya fara yin hazo-hazo. Kafun daga bisani Arshan ya sulale ƙasa sumamme.
Aljani Barbossa yayi gaggawar ɗauke Arshan sa'annan ya fara sharara azababben gudu ɗauke da shi.
***
~Bayan kwanaki uku da faruwar wannan al'amari.
~Babbar shalkwatar mayaƙan Jorash.
***
A wani babban sansani na sojojin ƙabilar Jorash. Wani rukuni ne na wasu dakaru guda goma tsaitsaye.
Dukkansu sun wuce matakin Otaki mai inuwa, tuni sun karɓi muƙaman ƙananan kyaftin a cikin rundunar.
Wani babban soja wanda yake matakin kwamanda yana tsaye a gaban su, fuskar sa ɗauke da ɓacin rai da fushi.
A hannun sa yana riƙe da hoton Arshan guda ɗaya. Kwamandan ya nunawa waɗannan kyaftin guda goma dake gabansa hotunan Arshan ya ce.
“Sunan sa: Arshan.
“Muna buƙatar sa a raye ko kuma a mace!”
Waɗannan kyaftin guda goma s**a zaro takubbansu s**a ɗan risina a gaban wannan kwamanda. Alamun sun karɓi wannan aiki da ya basu.
Babu jimawa aka kawo ingarmun dawakai guda goma aka baiwa waɗannan kyaftin.
Take s**a hau dawakan sa'annan s**a zabure su da azababben gudu. Cikin ƙiftawar ido s**a fice daga wannan sansani sannan s**a tunkaro doron ƙasashen ƙasa.
A wannan rana babbar shalkwatar sojoji ta mayaƙan ƙabilar Jorash dake doron ƙasa ta biyu ta bayar da umarnin a kamo mata Arshan.
Kuma babban tashin hankalin har ƙananan kyaftin guda goma aka tura masa.
Muƙamin ƙaramin kyaftin yana gaba da matakin Otaki a ƙabilar Jorash. Duk wanda ya zamo ƙaramin kyaftin tofa ya fara gawurta a lamarin jarumtaka.
***
~Ɓangaren Aiyini.
~Wani sashe a cikin doron ƙasa ta farko.
***
A daidai wannan lokaci Aiyini tana tsaye a cikin wani ƙatoton lambu a gaban wani tafkin wanka ta juya ta baiwa wani kyakkyawan saurayi baya.
Daga inda take tsaye mutum zai na jiwo sautin sheshsheƙar kukanta.
“Kamar ni...?! Kamar ni...?!!” ba tare da ta ƙarasa magana sai kuka ya ƙwace mata, muryarta ta sarƙe.
“Kada ki damu, masoyiya ta.
“Kiyi sani cewa, kin fafata yaƙi ne da Asén wanda muka shafe fiye da shekaru ɗari muna jiran bayyanar sa.
“Kuma ba don ya tsere ba, na tabbata da ya shiga hannun ki...”
Aiyini tayi wata irin ajiyar zuciya...
“Kamar ni...?!!! Kamar ni...? Ace na gagara samun nasara akan wani...?!
“Ba zan yarda da hakan ba...?!”
Kyakkyawan saurayin ya taso yazo bayan Aiyini ya tsaya.
“Ina baƙin ciki bisa rashin samun nasarar da kika yi. Amma baƙin cikin zubar da hawayen ki yafi kowanne a waje na.
“Kina matsayin khal kizo kina kuka akan wani ɗan ƙaramin jarumi?”
Aiyini tana jin batun wannan saurayi hankalinta ya ɗan kwanta. Ta goge hawayen dake zubowa daga idanunta. Ta juyo ta dube shi.
“Yaushe za'a sake ƙaddamar da kamfen?!” inji Aiyini.
Saurayin yayi guntun murmushi. “An kusa...”
“Yaushe?” Aiyini ta yamutse fuska.
“Ɗaya daga cikin ababe guda uku da zasu janyo a ƙaddamar da kamfen ya faru. Saura abubuwa guda biyu. Abubuwa guda biyun ma suna daf da faruwa!”
“Mene ne waɗannan abubuwa guda uku, Elanuyil?”
Sunan wannan saurayi Elanuyil. Koma wane ne shi zuwa yanzu ba'a bayyana ba. Amma ga dukkan alamu yana da tsananin kusanci a wajen Aiyini tunda shi ne mai kwantar mata da hankali.
“Abu na farko wanda MAJALISAR MANYA ta bayyana shi ne, mutuwar Ambahà!
“Babu wanda yasan abubuwa guda biyun, sai Babban Sarki da Waziri da kuma Yarima!”
Elanuyil ya kamo kafaɗun Aiyini ya fuskance ta ya fara bata labari mai daɗin gaske.
“Tuni na shigar da ƙorafi a babbar kotun doron ƙasa ta biyu. Zuwa yanzu an ɗauki tsatstsauran matakin da ya dace akan Asén.
“Babbar shalkwata dake doron ƙasa ta biyu ta tura mayaƙa muƙamin ƙananan kyaftin har guda goma su kamo shi kuma su gurfanar dashi.”
Aiyini tana jin wannan labari ta cika da tsananin farin ciki. Aiyini ƙaramar yarinya ce ko matakin Otaki mai inuwa bata wuce ba. Ballantana ta shiga matakin ƙaramar kyaftin.
Abu na ƙarshe da ya faru shi ne, fara sumbatar juna tsakanin Aiyini da wannan saurayi mai suna Elanuyil!
Wannan kenan.
****
THANKS FOR READING 🤗✍️