27/08/2025
WATA MIYAR SAI A MAƘWÀBTA: Da Alama Rayuwar Kurkukun Saudiyya Ta Fi Ta Nijeriya Daɗi
Daga Imam Aliyu Indabawa
1. Samar da gado mai kyau, shimfiɗa mai taushi, da ɗaki mai faɗi tare da bayan gida mai tsabta a cikin ɗakin zama.
2. A ciyar da Fursuna abinci sau uku a rana, iri-iri, tsakanin naman saniya, naman kaji da kifaye.
3. A ba wa ɗan fursuna kuɗin alawus na kowane wata domin ya iya sayan abin da yake so daga shagunan cikin gidan yari.
4. Gwamnati tana ɗaukar nauyin biyan iyalansa kuɗin ciyarwa a kowane wata tare da bibiyar halin da suke ciki.
5. A yi sallar jam’i a masallacin cikin gidan yari.
6. An samar da cibiyar lafiya a cikin gidan yari domin kula da marasa lafiya.
7. A ba shi damar yin ziyarar iyali kowane mako da yin kira ta waya duk lokacin da yake so; kuma idan yana da aure, a ba shi damar yin khulwa (haduwar aure ta sirri) da matarsa a ɗakin da aka tanada na musamman, karkashin tsaro.
8. Idan Fursuna ya haddace Alkur’ani gaba ɗaya, za a rage masa rabin lokacin hukuncin da aka yanke masa.
9. Ana wanke masa kaya, a yi musu guga da turare mai kamshi kyauta.
10. An kafa cibiyar koyar da sana’o’i domin koyar da ɗalibai cikin gidan yari.
11. Ana shirya kwasa-kwasai na horo ga masu sha’awa su koyi ilimi.
12. Malamai da masana addini na zuwa su gabatar da wa’azi da tarukan ilimi.
Wannan abubuwan ba za ka same su ba sai a cikin Daular Saudiyya – Mulkinta mutunci da darajar ɗan adam suna da daraja sosai.
Manhajarmu ita ce: gidan yari wajen gyara, tarbiyya da horo ne, ba wai hukunci kawai ba. Akwai haƙƙoƙi ga Kowane Fursuna.
Follow for More updates💥👇💥
Pantami Live.TV
Umar Muhammad Gombe