AAS News Hausa

  • Home
  • AAS News Hausa

AAS News Hausa 📰 AAS News Hausa
Breaking News | Najeriya & Duniya
📢 Tallace-tallace & Promotion: WhatsApp: https://wa.me/message/KFQSNKU27AF6I1

20/04/2026

Iran ta ce ba za ta koma tattaunawa karo na 2 ba a Islamabad

18/04/2026

Da Dumi-Dumi: Iran ta sake kulle Mashigin ruwan Hormuz

Iran: Ikon mashigar ruwan Hormuz na hannun mu Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko a Iran, Mohammad Reza Aref, ya bayyana c...
18/04/2026

Iran: Ikon mashigar ruwan Hormuz na hannun mu

Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko a Iran, Mohammad Reza Aref, ya bayyana cewa ikon mashigar ruwan Strait of Hormuz na hannunsu.

Ya ce ko dai a bai wa Iran haƙƙinta a teburin tattaunawa, ko kuma za ta karɓe shi a fagen daga. Wannan furuci na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin Iran da United States ta ƙare ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Gwamnatin Tinubu Ta Inganta Wutar Lantarki Fiye da Baya – Bwala Mai ba Shugaban Ƙasa shawara, Daniel Bwala, ya bayyana c...
18/04/2026

Gwamnatin Tinubu Ta Inganta Wutar Lantarki Fiye da Baya – Bwala

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara, Daniel Bwala, ya bayyana cewa wutar lantarki ta inganta a sassa daban-daban na Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ya ce an samu ci gaba a fannin samar da lantarki, wanda ke taimakawa jama’a da harkokin kasuwanci.

👉 Kai fa an samu ingancin wutar lantarki a yankinku kuwa? Ka faɗi ra’ayinka a comments 👇

Source: The Sun Nigeria

17/04/2026

DA DUMI-DUMI: Iran ta buÉ—e Straight of Hormuz Bayan cimma yarjejeniya

Atiku zai sake tsayawa takara a 2031 – Ministan AbujaMinistan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki tsohon M...
17/04/2026

Atiku zai sake tsayawa takara a 2031 – Ministan Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ke yawan neman takara ba tare da nasara ba.

Wike ya kuma yi hasashen cewa Atiku zai sake fitowa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2031 duk da alkawuran da aka ce ya yi na daina takara daga 2027.

Messi ya sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta UE Cornelia a ƙasar Spain Lionel Messi ya sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta UE Cornel...
17/04/2026

Messi ya sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta UE Cornelia a ƙasar Spain

Lionel Messi ya sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta UE Cornelia wadda ke mataki na uku a ƙasar Spain, inda ya zama cikakken mamallakinta.

Fitaccen tauraron ɗan wasan na Argentina ya bi sahun babban abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo, wajen mallakar ƙungiyar ƙwallo a Spain.

👉 Kana ganin Messi zai iya mayar da ƙungiyar babba kuwa? Ka faɗi ra’ayinka a comments 👇

LABARI ME DAUKAR HANKALI Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya karanta wata addu’a a wani taron Kirista da aka yi a ...
17/04/2026

LABARI ME DAUKAR HANKALI

Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya karanta wata addu’a a wani taron Kirista da aka yi a Pentagon wadda aka ce ta samo asali ne daga kalaman fim ɗin Pulp Fiction, ba daga ayar Littafi Bible kai tsaye ba.

Rahotanni sun nuna cewa kalaman sun yi k**a da sanannen zancen da Samuel L. Jackson ya faɗa a fim ɗin, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da s**a daga jama’a.

Hegseth ya danganta addu’ar da wani aikin ceto na sojoji da aka yi a rikicin Iran, amma lamarin ya haddasa muhawara kan amfani da kalaman fim a wajen ibada da harkokin gwamnati.

👉 Kana ganin ya dace jami’ai su riƙa amfani da irin wannan hanya a taron ibada kuwa? Ka faɗi ra’ayinka a comments 👇

Tinubu: Ba zan ji tsoro ko ja da baya saboda matsin lamba baShugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kalubalanci ‘yan ad...
17/04/2026

Tinubu: Ba zan ji tsoro ko ja da baya saboda matsin lamba ba

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kalubalanci ‘yan adawa, yana mai cewa ba zai ji tsoro ko ya ja da baya saboda matsin lamba ko barazana ba.

Ya sake jaddada cewa zai ci gaba da aiwatar da manufofinsa na gyaran ƙasa duk da s**a da adawa daga wasu ɓangarori.

DA DUMI-DUMI: MTN Sun dakatar da bayar da bashiKamfanin MTN Nigeria ya sanar da dakatar da sabis É—in MTN Xtratime, wanda...
16/04/2026

DA DUMI-DUMI: MTN Sun dakatar da bayar da bashi

Kamfanin MTN Nigeria ya sanar da dakatar da sabis É—in MTN Xtratime, wanda ke ba kwastomomi rancen kati da data.

Kamfanin ya ce an É—auki wannan mataki ne domin bin sabbin dokokin bayar da rance ta yanar gizo da hukumar Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC) ta fitar.

Wannan na nufin masu amfani da sabis ɗin ba za su iya karɓar rancen airtime ko data na ɗan lokaci ba har sai an samu sabon tsari.

👉 Kana amfani da Xtratime kuwa? Wannan mataki zai shafe ka? Ka faɗi ra’ayinka a comments 👇

China ta ce ba za ta tura mak**ai Iran ba – AmurkaSakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa ƙasar China ta ...
16/04/2026

China ta ce ba za ta tura mak**ai Iran ba – Amurka

Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa ƙasar China ta bai wa Amurka tabbacin cewa ba za ta tura mak**ai zuwa ƙasar Iran ba a lokacin tsagaita wuta.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, tare da fargabar sake komawa rikici.

👉 Kana ganin China za ta cika wannan alƙawari kuwa? Ka faɗi ra’ayinka a comments 👇

DA DUMI-DUMI: Iran ta yi barazanar rufe kogin maliyaƘasar Iran ta yi barazanar rufe hanyar kogin Red Sea, yayin da Amurk...
16/04/2026

DA DUMI-DUMI: Iran ta yi barazanar rufe kogin maliya

Ƙasar Iran ta yi barazanar rufe hanyar kogin Red Sea, yayin da Amurka ke matsa wa China lamba ta daina sayen man Iran.

A gefe guda kuma, ƙasar Pakistan ta bayyana cewa akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar nukiliya cikin lokaci kaɗan idan tattaunawa ta yi nasara.

Rahotanni sun nuna cewa wannan rikici na iya ƙara tsananta idan ba a samu sulhu cikin gaggawa ba.

👉 Kana ganin za a samu zaman lafiya ko rikicin zai ƙara zafi? Ka faɗi ra’ayinka a comments 👇

Address

Nigeria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AAS News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share