
29/06/2025
TARIHIN IMAM MUSLIM IBN AKIL, JAKADAN IMAM HUSAIN (AS) KASHI NA BIYU (2).
Lokacin da Muslim ya ga irin wannan yanayi da kuma irin wannan adadi na jamaโa da s**a mika wuya, nan take sai ya rubuta wa Imam Husaini (AS) wasika da bayyana masa yadda alโamurra suke a Kufa da kuma irin ayyukan da ya gudanar, da bukatar ya iso. A bangare guda kuma ko shakka babu irin wannan yanayi ba zai buya wa Yazid da kuma gwamnansa na Kufan wato Nuโuman bn Bashir ba.
Da farko dai Nuโuman bn Bashir ya so kawo karshen irin wannan yanayi ta hanyar ruwan sanyi sai dai abin ya ci tura. Irin siyasar da Nuโuman din dai ya dauka wajen magance wannan matsala ba ta yi dadi wa wasu daga cikin โyan amshin shatan wannan hukuma ba, su na masu tsoron rasa matsayin da suke da shi na siyasa da kuma zamantakewa, don haka sai daya daga cikinsu mai suna Abdullah bn Muslim (da ma wasu na daban irin su Ammara bn Ukbah da Umar bn Saโad bn Abi Wakkas) ya rubuta wa Yazid wani rahoto ya na mai bayyana masa yadda alโamurra suke gudana da kuma irin hatsarin da ake ciki, don haka ya bukace shi ya da tsige Nuโuman bn Bashir a matsayinsa na gwamna da kuma aiko wani mutum mai kaushin hali wanda zai yi maganin lamarin da karfin tuwo.
Bayan isowar wadannan sakonni, sai Yazid ya fara tunani da kuma neman wani mutum wanda ya yi kaurin suna wajen ayyukan taโaddanci da rashin tausayi da imani, mai tsananin son mulki ko ta yaya, haka nan kuma wanda ya fi kowa tsananin gaba da Ahlulbaiti (AS). Don haka bayan bincike da shawarwari, bai ga duk wani mutumin da ya dace da wannan matsayi in ban da Ubaidullah bn Ziyad, wanda a wancan lokacin shi ne gwamnan Basra. Don haka sai ya ba shi wannan aikin, ya na mai umartarsa da ya yi amfani da tursasawa da kuma kaushin hali bugu da kari kan zubar da jinin duk wani danโadawa har sai an kawo karshen wannan adawa ga hukumarsa.
Ba tare da bata lokaci ba Ubaidullah bn Ziyad ya k**a hanyar Kufa zuciyarsa cike da fushi da mugunta, su kuwa mutanen Kufa su na nan cikin shirin tarbar...