
26/05/2025
HON. USMAN BELLO KUMO YA ZIYARCI KUMO, YA RABA TALLAFIN SALLAH DA BAYANI KAN MUHIMMAN AIYUKA
Litinin, 26 ga Mayu, 2025
A wani jawabi da ya janyo farin ciki a zukatan jama’a, Rt. Hon. Usman Bello Kumo ya iso garin Kumo domin gudanar da hidimar Sallah da kuma gabatar da sabbin tsare-tsaren ci gaba ga al’ummar Akko. Wannan ziyara ba kawai ta nuna kulawa ba ce, amma ta ƙara tabbatar da yadda yake goyon bayan jama’arsa.
Hon. Kumo ya ware naira miliyan 250 domin saukaka rayuwa a lokacin Sallah, alamar jajircewarsa wajen ganin kowa ya samu damar murnar bukukuwan cikin walwala da natsuwa.
Baya ga hakan, ya ziyarci fadar Lamidon Akko, inda ya gana da manyan masu rike da mukaman gargajiya da na siyasa, yana bayyana cikakken shirin da ya ke da shi na ƙarfafa ci gaba a Akko, duk da kalubalen siyasa.
Cikin bayanan da ya fitar akwai:
Shigar da aikin filin wasa na Kumo cikin kasafin kuɗi na 2025, da fara aikin a watan Yuli.
Biyan diyya ga masu gidaje da aikin zai shafa, domin komawarsu ba tare da wata wahala ba.
A karkashin rarraba tallafi, Hon. Kumo ya bai wa dubban iyalai kayan abinci da tufafi a sassa daban-daban na Akko, Gona da Pindiga. Ya kuma bayar da zannuwa 10,000 ga mata tare da naira miliyan 50 domin taimakawa su dinka kayan.
Ya kuma ja hankalin shugaban Karamar Hukumar Akko da ya nemi sahalewar Gwamna domin sabunta yankin GRA na Kumo zuwa unguwar zamani domin ma’aikatan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Kumo.
A wani bangare na horar da matasa, ya tura wasu zuwa Yola domin horon noma na zamani, da kuma wasu 35 suna karɓar horo a dinki da ƙirƙirar takalma a Gombe.
Wannan ziyarar ta fi kowace magana, Aiki ne da nufin ci gaban jama’a da raya yankin Akko.
Wannan ne irin jagorancin da ake bukata, Wanda ke aiki ba da gajiyawa, yana tallafawa jama’a ba tare da nuna bambanci ba.
~Comrd Sani Yahaya Akko