03/09/2026
Ahmed Yayari, tsohon dan takarar gwamnan Jihar Gombe a karkashin jam’iyyar (PDP), kuma tsohon Ma’ajin jam’iyyar na kasa, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance, inda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga takarar gwamna ta Dr. Jamil I. Gwamna, dan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar (APC).
A wata sanarwar dauke da sa hannu Ibrahim Sani Shawai Mai magana da yawun Dr. Jamil Isyaku Gwamna, Yayari, wanda fitaccen jigo ne a harkokin siyasa kuma yake da gogewa mai yawa tun daga matakin jiha har zuwa na kasa, ya ce ya yanke shawarar mara wa Gwamna baya ne saboda dan takarar gwamnan na APC yana da kyawawan halaye, gogewar siyasa, hangen nesa da kuma kwarewar jagoranci da ake bukata domin samar da shugabanci mai ma’ana da kuma kai Jihar Gombe zuwa matsayi mafi girma.
Ya kuma yi alkawarin amfani da gogewarsa ta siyasa, alakokinsa da kuma tsarukan magoya bayansa na matakin kasa domin tabbatar da nasarar Dr. Jamil Gwamna a matsayin Gwamnan Jihar Gombe na gaba. Ya jaddada cewa Gwamna ya fito ne daga gida mai daraja, mutunci da kyawawan halaye, wanda gudummawarsa da jajircewarsa wajen ci gaban da walwalar al’ummar Jihar Gombe s**a shafe tsararraki da dama.
A cewarsa, Gwamna ya bambanta kansa a matsayin dan siyasa mai kishin nauyi, wanda jajircewarsa ba ta tsaya kawai kan burinsa na siyasa ba.
Ya kuma bayyana shi a matsayin shugaba mai bayyananniyar manufa da hangen nesa, wadanda s**a mayar da hankali kan taimakon al’umma, bai wa jama’a damar dogaro da kai da kuma bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban al’umma.
Yayari ya ci gaba da cewa Gwamna ya fahimci tsarin siyasa da yadda yake tafiya, tare da bukatun gudanar da mulki, lamarin da ya sanya shi cikin wadanda s**a dace da bayar da ingantaccen jagoranci ga al’ummar Jihar Gombe.
Hon. Yayari ya tabbatar da cewa shi da magoya bayansa za su sadaukar da lokacinsu, karfinsu da dukkanin damar da suke da ita ta fuskar siyasa domin tabbatar da nasarar burin Gwamna, tare da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar APC a fadin jihar.
Da yake mayar da martani, Dr. Jamil Gwamna ya yi wa Hon. Yayari kyakkyawar tarba, inda ya bayyana matakin da ya dauka a matsayin wani babban ci gaba a siyasance, kuma babban karin karfi ga yakin neman zabensa da kuma iyalan jam’iyyar APC a Jihar Gombe.
Gwamna ya bayyana Yayari a matsayin ginshikin hada kan jama’a da tattara magoya baya a matakin kasa, tare da kasancewarsa gogaggen masani a dabarun siyasa, wanda ba za a iya watsi da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban siyasar Jihar Gombe da Najeriya baki daya ba.
Ya lura cewa gogewar Yayari, kasancewarsa a manyan mukaman siyasa tun daga matakin jiha har zuwa jagorancin jam’iyyar PDP a matakin kasa, za ta kara wa jam’iyyar APC da tsare-tsarenta na siyasa matukar kima.
Ya ce shigowar irin wannan gogaggen kuma mai tasiri a harkokin siyasa na nuna karuwar amincewa da jam’iyyar APC, tare da tabbatar da imanin masu ruwa da tsaki cewa jam’iyyar ita ce mafi sahihancin dandali wajen samar da shugabanci mai ci gaba da kuma dorewar ci gaban Jihar Gombe.
Ana ci gaba da shirye-shiryen karbar Hon. Yayari da magoya bayansa a hukumance cikin jam’iyyar APC, wanda za a gudanar nan ba da dadewa ba. Ana sa ran taron zai hada shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, magoya baya da sauran fitattun mutane masu tasiri daga sassan Jihar Gombe.