
25/05/2025
Wannan shi ne masallacin Quba da aka fara ginawa a tarihin Musulinci, ba da tubali da kasa kawai ba, an kwabashi cike da tsoron Allah tsantsarsa.
لَمَسْجِدٌ أُسِّسَ عَلَى التَّقْوَى مِنْ أَوَّلِ يَوْمٍ أَحَقُّ أَنْ تَقُومَ فِيهِ
A nan aka assasa wanzuwar hijira.. aka tabbatar da sallah.. kuma daga nan aka fara tabbatar da ambaton Allah a ban kasa.
A nan ne Manzon Allah (saw) ya yi alwala, nan ya yi sallah, sannan ya sanar da cewa Musulinci ya samu yancinsa bayan shekaru ana wahalar da shi.
A nan gurin ne Manzon Allah (saw) ya ce raka'a biyu karbabbiya dai-dai take da ladan aikin Umrah saboda kimarsa. Nan miliyoyi s**a yi addu'a aka amsa. Nan miliyoyi s**a yi sallah ta karbu.
Mutane daruruwa na ta shiga. Wasu suna Sallah. Wasu na hoto. Wasu kuma suna fashewa da kuka.
Amma ni kuma...
Ina tsaye ina tunanin cewa masallacin nan ba tarihi kawai yake dauke da shi ba, yana cike da wata ma'ana mai nuni da cewa duk abin da ya zama babba to da dan karami ya fara.
Masallacin Quba yana gaya mana cewa kyallin da yake gabanka a yau, zai iya zama hasken rana matukar ka assasashi da kyakkyawar niyya.