25/09/2025
Daya daga cikin manyan zunubai shi ne jingina wa Manzon Allah ﷺ wani abu da bai faɗa ba.
Ko a jingina masa wata karama ko sifa da Allah bai ɗora masa ba, ko kuma ba tada asali a cikin sahihan Hadisai.
Annabi ﷺ ya yi gargaɗi sosai akan hakan yace:
قال رسول الله ﷺ: من كذب عليَّ متعمِّدًا فليتبوأ مقعده من النار
"Duk wanda ya yi masa ƙarya da gangan, to ya tanadi mazauninsa a wuta"
Yin ƙarya ko ka jingina wani abu ga Annabi ﷺ ba tare da wata hujja ba babban zunubi ne.
Kuma yana daga cikin hanyar da jahilai ke bi su gurbata Addini.
Akwai wasu Hadisai da aka ƙirƙira (Mawdu'at) waɗanda a ka jingina wa Annabi ﷺ ƙarya da karamomi da ba Allah ya ɗora masa ba, kuma ba su da asali a cikin sahihan Hadisai.
Ga wasu kaɗan daga cikin su: 👇
خَلَقَ اللهُ نُورَ مُحَمَّدٍ ﷺ مِنْ نُورِهِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ الْخَلْقَ
"Allah ya halicci hasken Annabi Muhammad ﷺ daga hasken sa kafin halittar sauran halittu"
Malamai sun ce wannan ƙarya ne, ba Hadisi bane daga Manzon Allah {ﷺ}.
Sai kuma Hadisin an halicci sammai da ƙassai domin Annabi {ﷺ}
لَوْلَاكَ لَوْلَاكَ مَا خَلَقْتُ الْأَفْلَاكَ
"Wato da ba don kai ba (Annabi ﷺ), da ban halicci sammai da ƙassai ba"
Shi ma wannan ba Hadisi ba ne, ƙarya ce da ba ta da asali.
Sai Hadisin cewa Annabi {ﷺ} ya san gaibu wannan ma ƙarya ce.
Domin Qur'ani ya tabbatar mana cewa Annabi ﷺ bai san gaibu ba sai abin da Allah ya sanar da shi.
Sannan Hadisin Annabi ﷺ yace dukkan halittu an halicce su ne daga haskensa, wannan ma ba gaskiya ba ne, kawai an jingina ƙarya ne ga Manzon Allah ﷺ.
Sai kuma Hadisin cewa wai Annabi ﷺ ya raba haskensa gida biyu aka halicci Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) sai shi kuma aka halicce shi da ɗayan rabin, wannan ma ƙarya ne.
Wallahi mafi yawan waɗannan ƙarairayin suna fitowa ne daga bakin yan BIDI'AH ko mawaƙa daga cinkinsu, suna ƙirƙirar ƙarya suna jingina wa ga Manzon Allah {ﷺ}.