16/11/2024
Labarin Yadda Wani Ɗan Nigeria Ya Mallaki Bitcoin guda 1,500
A shekarar 2012, nayi wani hatsari akan titin Gwarzo Road, wanda aka fi sani da titin BUK a yanzu, a waccen lokacin titin hannu ɗaya ne. Cikin ƙaddarawa ta Ubangiji sati ɗaya kenan dana siya motar da nayi hatsarin da ita 2.7 million, shekara biyu nayi ina tara kuɗin siyar motar wannan abin ya faru, wannan hatsarin da nayi ya tilasta ni siyar da wannan motar a farashin 1.2M kacal saboda ta samu nakasa sosai.
Duba da lalacewar kuɗin bazasu kai na siya wata motar da nake so ba, wani abokina amintacce ya bani shawarar na jarraba harkar Bitcoin, a waccen lokacin farashin dollar guda ɗaya N155.5 ne, don haka saina chanza wannan kuɗin zuwa dollar $7,700. Sai nayi amfani da dollar na siya Bitcoin guda 1500 a farashin duk Bitcoin guda ɗaya $5. WANNAN BITCOIN ƊIN DANA SIYA SHINE SHAWARA MAFI GIRMA A KASUWANCI DANA TAƁA YANKEWA A RAYUWATAH.
A ƙarshen shekarar 2012, farashin Bitcoin ya tashi zuwa $13. A July shekarar 2014 lokacin da akayi launching ɗin USDT sai da BTC ya kai farashin $770, a lokacin ina India ina yin Masters. Daga wannan lokacin na fahimci akwai wani abu da Ubangiji yake nufi dani. A haka naci gaba da zuba kuɗina a Bitcoin da dukkan wasu abubuwa da suke da alaƙa dashi.
Yau farashin Bitcoin ha haura $90,000, kuma da dukkam alamu yana daf da dosar $100,000 harma ya haura.
Kamar yadda na zuba hannun jari a kasuwar Crypto, na zuba hannun jari a dukiya ta zahiri, na siya wani fili a Tudun Yola a 2014 akan kuɗi 5 million, yau darajar wannan filin ta kai 90 Million. IDAN BAKA YARDA DA CRYPTO BA, KA SIYA FILI.
A wannan rayuwar, Crypto da Fili sune sahihiyar hanya da zaka adana dukiyar ka su ƙara daraja a tsawon lokaci ka samu riba sosai idan an kwatanta da sauran su, suna da wani ƙarfi da suke ƙara daraja ba tare da kayi musu wata ɗawainiya ba kana chan kana baccin ka amma kullum suna ƙara daraja kana ƙara zamowa Attajiri.
______
Akwai darussa masu yawa acikin wannan labarin nasa, wanne da wanne zaku iya fito mana dashi?
💎Ka kyautata zaton ka ga Allah, ƙaddarar data same ka yanzu kake jin babu daɗi, ƙila mataki ce ka taka ga wata babbar nasara da zaka cimma.