Jewel FM Gombe

Jewel FM Gombe A Radio Nigeria FM station in Gombe broadcasting on frequency 103.5Mhz. The station is located along Bauchi road adjacent Federal High Court.

AGILE Gombe Ta Raba Naira Miliyan 726 Ga Ƴan Makarantar Sakandare Mata
17/10/2025

AGILE Gombe Ta Raba Naira Miliyan 726 Ga Ƴan Makarantar Sakandare Mata

17/10/2025
17/10/2025

Shirin Dandalin Shairai Tareda Sayyadi Habu Kwantin Bege

Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Tinubu Na Kara Janyo Jama’a Zuwa APC – Gwamna OtuGwamnan Jihar Cross River, Sanata Bassey ...
17/10/2025

Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Tinubu Na Kara Janyo Jama’a Zuwa APC – Gwamna Otu

Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Bassey Otu, ya yabawa gyare-gyaren tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, inda ya ce waɗannan sauye-sauyen su ne babban dalilin da ke janyo mutane da dama su shiga jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

Ya bayyana cewa manufofin Tinubu na tattalin arziki suna ƙara ɗaukar hankalin ’yan Najeriya, suna ganin jam’iyyar APC a matsayin mafita ga ci gaban ƙasa.

Shin dagaske hakanne?

AGILE Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Inganta Makarantu da Tallafin Karatu a GombeShirin AGILE (Adolescent Girls Initiative...
17/10/2025

AGILE Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Inganta Makarantu da Tallafin Karatu a Gombe

Shirin AGILE (Adolescent Girls Initiative for Learning & Empowerment) ya kaddamar da bayar da Tallafin Inganta Makarantu (School Improvement Grants - SIGs) da kuma tallafin karatu ga ‘yan mata matasa a fadin Jihar Gombe domin inganta iliminsu.

Gwamnatin Gombe ta Sa hannu kan Yarjejeniya da Kamfanin Rano Air don Fara Zirga-zirgar Jiragen Sama daga Abuja zuwa Gomb...
17/10/2025

Gwamnatin Gombe ta Sa hannu kan Yarjejeniya da Kamfanin Rano Air don Fara Zirga-zirgar Jiragen Sama daga Abuja zuwa Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanin Rano Air Limited domin fara jigilar fasinjoji ta jiragen sama daga Abuja zuwa Gombe da kuma dawowa.

Wannan ya biyo bayan ganawar da aka gudanar tsakanin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, da manyan jami’an kamfanin a gidan gwamnatin jihar da ke Abuja, inda s**a kammala shirin fara wannan sabis.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya sa hannu a madadin Gwamnatin Gombe, yayin da Babban Manajan Ayyuka na Rano Air, Mista Abah Godwin, ya sanya hannu a madadin kamfanin. Shugaban filin jirgin sama na Brig. Zakari Maimalari da ke Gombe, Injiniya Suleiman Daniel Musa, da Mista Auwal Sulaiman Ubale sun kasance cikin wadanda s**a halarci taron shaidar yarjejeniyar.

A karkashin wannan yarjejeniya, Rano Air za ta fara zirga-zirgar jirgi sau hudu a mako ta hanyar amfani da jirgin Embraer 145 mai daukar fasinjoji 50. Ayyukan za su kasance a ranakun Litinin, Laraba, Juma’a da Lahadi.

Insha Allahu yau juma'a da misalin 3 zuwa 4 zaku zamu karbi bakuncin syd Alh Habu conty Bege Gombe acikin shirin dandali...
17/10/2025

Insha Allahu yau juma'a da misalin 3 zuwa 4 zaku zamu karbi bakuncin syd Alh Habu conty Bege Gombe acikin shirin dandalin sha'irai.

Public Announcement Gombe State Transport Service Gombe line AN SAMU IYAYEN MUHSINBiyo bayan sanar war da hukumar Gombe ...
17/10/2025

Public Announcement

Gombe State Transport Service
Gombe line

AN SAMU IYAYEN MUHSIN

Biyo bayan sanar war da hukumar Gombe Line tayi.

Ansamu Iyayen MUHSIN kuma sun zo tare da Principal din Makarantansu, da Mokobta. Tare da hukumar Yansanda ta Megapark mun Mika Shi wa iyayensa.

Muna Kira da Al umma da iyaye a Kula sosai.

Muna Godiya wa al'umma bisa gudumar dasu Ka bayar domin nemo Iyayen wannan yaron.

Mungode

Sani Sabo PhD
Director General/Sole-Administrator
Gombe Transport Services
Gombe line

PUBLIC ANNOUNCEMENT GOMBE LINEMuna Kira da Al umma in akwai Wanda ya San wannan yaron 'Muhsin' ya sanar da iyayensa huku...
17/10/2025

PUBLIC ANNOUNCEMENT

GOMBE LINE

Muna Kira da Al umma in akwai Wanda ya San wannan yaron 'Muhsin' ya sanar da iyayensa hukumar sufuri ta Gombe Line na rike da Shi bayan yazo Shi daya wai zai tafi Abuja.

Yace sunan Babanshi Ukasha makaniki ne a Abuja, kuma Sunnan mamar Shi Fatima a unguwar Nayinawa, Yana Wata makaranta Nasara Primary School.

Iyaye a dinga Kula da yara sosai domin muna samun ire iren matsololi haka. muna da record da na irin waennan matsololin muna aiki tare da hukumar naptip da Women affairs.

Daga record din mu a Wata Tara dasu Ka wuce mun mayar da yara Sama da 95 tare da hadin guiwan yansanda da Hukumar NAPTIP dakuma ministry of Women affairs.

Yanzu karfe Shida na safe, k**ar wannan yaron ace ya bar gidansu da kayan SA wai zai tafi Abuja.

Comrade Sani Sabo

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe Ta Gano Motoci da Aka SataRundunar ‘Yan sanda ta Jihar Gombe ta bayyana nasarar da ta...
16/10/2025

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe Ta Gano Motoci da Aka Sata

Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Gombe ta bayyana nasarar da ta samu wajen gano wasu motoci da aka sace daga wurare daban-daban a cikin jihar.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya ce binciken da jami’an tsaro s**a gudanar ya taimaka wajen gano motocin bayan samun bayanan sirri daga jama’a.

Ya kara da cewa an k**a wani mutane da ake zargi da hannu a satar motocin, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu da s**a gani da ba su yarda da shi ba, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin jihar.

Ta kuma yi alkawarin ci gaba da daukar matakan da s**a dace wajen dakile aikata laifuka a jihar.

TCN Ta Fara Aikin Gyaran Na Tsawon Kwana Goma a Babban Tashar Wutar Lantarki ta GombeMazauna da ‘yan kasuwa a Jihar Gomb...
16/10/2025

TCN Ta Fara Aikin Gyaran Na Tsawon Kwana Goma a Babban Tashar Wutar Lantarki ta Gombe

Mazauna da ‘yan kasuwa a Jihar Gombe na fuskantar yiwuwar samun tangarda ko karancin wutar lantarki na tsawon kwanaki goma, sak**akon fara aikin gyaran da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya fara a babban tashar wutar lantarki da ke cikin jihar.

Aikin gyaran wanda ya shafi muhimman sassa na tashar zai shafi isar da wutar lantarki zuwa sassa daban-daban na jihar, wanda hakan zai iya janyo matsalolin wutar lantarki a gidaje da wuraren kasuwanci.

Hukumar TCN ta bukaci hadin kai da fahimtar jama’a yayin da ake gudanar da aikin, tana mai cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da ingantacciyar wuta a nan gaba.

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC
16/10/2025

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

Address

Bauchi Road
Gombe

Opening Hours

Monday 06:30 - 23:00
Tuesday 06:30 - 23:00
Wednesday 06:30 - 23:00
Thursday 06:30 - 23:00
Friday 06:30 - 12:00
Saturday 06:30 - 12:00
Sunday 06:30 - 12:00

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jewel FM Gombe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jewel FM Gombe:

Share