
08/07/2025
ASUU ta dakatar da yajin aiki bayan gwamnatin tarayya ta biya albashin watan Yuni
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta janye barazanar shiga yajin aikin da ta yi a baya, bayan biyan albashin watan Yuni 2025 ga membobinta da aka yi jinkiri.
Shugaban reshen ASUU na Jami’ar Abuja, Dr. Sylvanus Ugoh, ya tabbatar da hakan a wata hira da jaridar LEADERSHIP a ranar Talata.
Dr. Ugoh ya ce ƙungiyar ta dakatar da shirin janye ayyuka ne bayan da aka fara ganin albashin watan Yuni a asusun membobin kafin ƙarewar wa’adin ƙarfe 11:59 na dare da reshen ya bayar.
“Albashin watan Yuni na membobinmu ya fara shiga kafin ƙarshen wa’adin ƙarfe 11:59 na daren Litinin, 7 ga Yuli, 2025 da ASUU UniAbuja ta bayar. Don haka, reshen bai fara janye ayyuka ba k**ar yadda majalisar ƙungiya ta yanke a baya,” in ji Ugoh.