09/04/2026
PROF. GARKUWA: MATASHI MAI CIKAKKEN CAPACITY A SIYASAR JIHAR GOMBE
Daga Walid Usman Japanise
Prof. Abdullahi Bappah Garkuwa ba kawai matashi ba ne a siyasar Jihar Gombe, matashi ne mai hangen nesa, kwarewa da cikakken ƙarfin jagoranci (capacity) wanda ya tabbatar da kansa a aikace. Ga wasu hujjoji masu ƙarfi da ke nuna dalilin da yasa ake kallonsa a matsayin ginshiki a siyasar jihar:
Kyakkyawar Mu’amala da Malamai:
Prof. Garkuwa mutum ne mai haɗa kai, wanda yake da kyakkyawar alaka da dukkan malamai a Jihar Gombe—daga Izala har zuwa Darika. Wannan mutunci da girmamawa da yake samu daga gare su ba a banza yake ba, domin a lokacin da yake jagorantar shirin BESDA, ya tallafa musu matuƙa a dukkan kananan hukumomi 11 na jihar.
Tsari (Structure) Mai Ƙarfi a Fadin Jiha:
A lokacin da yake shugabanci a BESDA, Prof. Garkuwa ya samar da ayyukan yi ga dubban al’umma, wanda hakan ya gina masa gagarumin goyon baya a matakin ƙasa (grassroots). A yau, yana da jama’a a kowace ƙaramar hukuma da suke masa biyayya bisa kyakkyawan aikin da ya musu a baya. Duk inda ya kira, ana masa amsa.
Tallafi da Jinƙai Ga Al’umma:
Prof. Garkuwa ya nuna a aikace cewa shi jagora ne mai tausayi da kula da jama’a. Ya raba tallafi iri-iri kamar:
Motoci da mashuna masu yawa
Gidaje da filaye
Kayan sana’a kamar kekunan dinki sama da guda dubu
Wadannan ayyuka sun shafi dubban iyalai, suna inganta rayuwarsu kai tsaye.
Karɓuwa a Siyasa:
Babu shakka Prof. Garkuwa na daga cikin matasan da s**a fi karɓuwa a siyasar Gombe. Duk wani ɗan takarar gwamna da ya samu goyon bayansa, zai amfana da ɗimbin kuri’u daga sassa daban-daban na jihar, domin alherinsa ya ratsa lungu da saƙo.
Farin Jini da Amincewar Jama’a:
Allah Ya albarkace shi da farin jini na musamman. A siyasar 2023, ya kasance daga cikin matasan da s**a yi tsayin daka wajen mara wa Mai Girma Gwamna baya, tare da nuna cikakken jajircewa da aiki a fili.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Prof. Garkuwa girma, ɗaukaka da lafiya, Ya kuma sa ya gama da duniya lafiya. Ameen.
Walid Usman Japanise ✍️
Jagaban Matasa