18/09/2025
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta huɗu sun mutu, yayin da wasu uku s**a jikkata bayan motarsu ta taka wani abin fashewa a Rafah da ke kudancin Gaza.
A wani labarin kuma rundunar sojin ƙasar ta ce wani mutum ɗan ƙasar Jordan da ke tuƙa motar ɗaukar kayan agaji ya kashe sojojinta biyu a mashigar sarki Hussein da ke kan iyaka.
Jami'an tsaro sun ce mutumin ya soma ne da harbin sojojin kafin ya caccaka musu wuƙa.
Sun ce daga bisani wani mai gadi ya harɓe direban.
Hukumomi a Jordan sun ce an kulle mashigar, wadda ake kira mashigar Allenby a Isra'ila, saboda cunkoson ababen hawa.