
19/11/2024
’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun nuna damuwa kan cewa kudirorin Shugaba Tinubu na yiwa dokar haraji garambawul, ba za su haifar da Komai ba, sai dai su kara gurgunta tattalin arzikin Najeriya.
'Yan majalisun sun koka kan matsin rayuwa da yan Najeriya ke fama da su a yankin arewacin kasar.