20/03/2026
20/03/2026
Eid-el-Fitr: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Taya Al'ummar Musulmi Murnar Sallah; Ya Buƙaci a Ci Gaba da Addu'o'i da Jajircewa Don Ganin Bayan Manyan Ƙalubalen Rayuwa
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya yi ƙira ga Al'ummar Musulmi da sauran 'yan ƙasa su ci gaba da jajircewa ga ibada, sadaukarwa da addu'o'i da aka saba a watan Ramadan, yayin da ake murna da bukukuwan sallar azumi (Eid-el-Fitr) na bana.
A saƙonsa na barka da sallah da ya fitar don murnar kammala azumin watan na Ramadan cikin nasara, Gwamnan ya jaddada cewa Eid-el-Fitr ba kawai lokaci ne na murna ba, lokaci ne ma na yin tunani da nazari mai zurfi, yana mai ƙira ga masu imani su ci gaba da ɗabbaƙa darussan da s**a koya a watan mai tsarki a harkokinsu na yau da kullum.
"Yayin da muke bikin Eid-el-Fitr, ina mana tuni cewa mu ci gaba da ɗabbaƙa kyawawan darussan watan Ramadan waɗanda s**a shafi ibada, biyayya da jajircewa. Dole ne mu yi riƙo da ƙa'idodin Musulunci waɗanda ke haɓaka zaman lafiya, haƙuri, tsantsaini da ƙauna," in ji Gwamnan.
Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada muhimmancin ci gaba da addu'o'in zaman lafiya, haɗin kai da wadata, musamman a wannan lokaci da ƙasar nan ke fuskantar ƙalubalen zamantakewa dana tattalin arziƙi.
Ya yi ƙira ga al'umma da cewa kar su yanke ƙauna, su ci gaba da dagewa kan imani da haɗin kai, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa Najeriya za ta yi nasara da samun ƙarin haɗin kai.
Ya kuma yi ƙira ga al'ummar Jihar Gombe su ci gaba da girmamawa da kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin dake ci gaba da wanzuwa a jihar, yana mai bayyana zaman lafiya a matsayin ginshiƙin ci gaba mai ma'ana.
Gwamnan ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyan jama'a ba, yana mai alƙawarin ci gaba da mai da hankali kan samar da romon demokraɗiyya ga jama'a.
Gwamna Inuwa Yahaya, wanda kuma shine Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, ya bayyana muhimmancin wannan lokaci, musamman ganin yadda harkokin siyasa ke ƙara kankama a faɗin ƙasar nan, yayin da babban zaɓen 2027 ke gabatowa, yana mai roƙon a ci gaba da addu'o'i don samun zaɓe mai inganci cikin kwanciyar hankali da lumana.
"A wannan mawuyacin lokaci da za a gudanar da harkokin siyasa da zaɓe nan ba da jimawa ba a ƙasarmu, ina roƙon mu duka, mu ci gaba da yin addu'o'in samun zaman lafiya, musamman ga shugabanninmu a matakai daban-daban, akan Allah Ya ba su hikima kuma Ya daafa mu su wajen sauƙe nauyin dake kansu," in ji shi.
Gwamnan ya buƙaci shugabannin addinai, sarakuna da al'umma baki ɗaya su ƙara himma wajen inganta haɗin kai, haƙuri, da kuma zaman lafiya a tsakanin al'umma daban-daban, yana mai cewa irin waɗannan ɗabi'u suna da matuƙar muhimmanci ga ci gaba da ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya bayyana matuƙar godiya ga al'ummar Jihar Gombe saboda goyon baya da haɗin kan da suke baiwa gwamnatinsa, yana mai ƙira garesu, su sabunta jajircewarsu ga ci gaban jihar baki ɗaya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatarwa al'ummar jihar ci gaba da jajircewar gwamnatinsa na hamzarta samar da ci gaba a fannoni masu mahimmanci, yana mai alƙawarin ƙarfafa ribar da ake samu da kuma samar da wadata mai ɗorewa ga kowa.
Ya yi wa al'ummar Musulmi fatan alheri da gudanar da bukukuwan sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe