
29/07/2025
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya ce yankin arewacin Nijeriya za ta mara wa shugaba Bola Tinubu a fafukarsa ta neman tsayawa zaɓe a 2027.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Talata a wani taron kwanaki biyu na shugabannin arewa da ake gudanarwa a jihar Kaduna domin duba irin ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu ta yi, musamman kan abin da ya shafi walwalar ƴan yankin.
Ya ce goyon baya da aka bai wa Tinubu a zaɓen 2023 ya fara haifar da ɗa mai ido a ɓangarorin ayyukan more rayuwa da tsaro da noma da kuma mak**ashi.
Taron wanda gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya, ta samu halartar gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, gwamnan Gombe Inuwa Yahaya, sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci, hafsoshin tsaro da kuma sauran ƴansiyasa daga yankin arewa.