Habibu Umar

Habibu Umar Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Habibu Umar, Digital creator, Gombe.

18/05/2026
Tunaninka zai sauya a kan nankarwa bayan karanta wannan binciken 👇
16/05/2026

Tunaninka zai sauya a kan nankarwa bayan karanta wannan binciken 👇

DA DUMI-DUMI: A yau Laraba matasan gidan Professor Isa Ali Pantami da s**a hada mishi fiye da Naira miliyan sittin (N60,...
29/04/2026

DA DUMI-DUMI: A yau Laraba matasan gidan Professor Isa Ali Pantami da s**a hada mishi fiye da Naira miliyan sittin (N60,000,000) kudin siyan form din tsayawa takara sun cika burinsu na siyan form din.

Idan baku manta ba a ranar Jumma'a da ta gabata Matasan da Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, PhD, yayi silar taimakon rayuwarsu da masoyanshi s**a kudiri aniyar saya mishi form din tsayawa takarar Gwamnan jihar Gombe a kokarin matasan na maida halaccin taimakonsu da Professor Isa Ali Pantami yayi a rayuwarsu.

Wannan dalilin yasa matasan s**a kafa kwamitin gaggawa a tsakaninsu ba tare da wani ya saka su ba, inda a cikin kwanaki biyu kacal s**a hada fiye da Naira miliyan sittin (N60,000,000) kudin da ya zarce na iya siyan form din.

Dukkannin mutanen da s**a bada gudummuwarsu babu wanda aka saka ya bayar kowa radin kanshi

Wannan yake kara nunawa duniya cewa Majidadin Daular Usmaniyya ya kafa matasa da ayyukan yi a damar da ya samu.

A yau Laraba wakilan wasu daga cikin matasan s**a je inda ake saida form din, s**a cika burinsu na siyawa Malam Professor Isa Ali Pantami form din k**ar yadda s**a kudiri aniya.

Hanyar farko da zaka samarwa kanka cigabaDuk abunda yake jawo maka tashin hankali, firgici, ko rashin nutsuwa akai-akai,...
29/04/2026

Hanyar farko da zaka samarwa kanka cigaba

Duk abunda yake jawo maka tashin hankali, firgici, ko rashin nutsuwa akai-akai, ka nemi hanyar gyara shi ko ka nisance shi idan babu mafita

- idan budurwa ce, nemi wata

- idan aure ne, kayi iya ƙoƙarinka kuma babu wata mafuta to a rabu kowa ya k**a gabansa

- Idan abokai ne masu cutarwa, ka canja su. Kar ka tsaya acikinsu kana habaice-habaice marar amfani

- idan muhalli ne (gari ko unguwa) to ka canja muhalli

- idan wani mutum ne, to ka nisance shi
-------------------------

⚠️ dole sai mutum yana acikin kwanciyar hankali da nutsuwa yake tunani mai kyau, sannan yake samarwa rayuwarsa cigaba mai inganci

Mafiyawanku damuwa da ɓacin rai ke hana ku kaiwa zuwaga matakin rayuwa mai amfani.

SHIN KO SOYAYYA TANA DA AMFANI GA RAYUWAR MATASHI MAI NIYAR GINA KANSA?A gaskiya idan za a faɗa kai tsaye soyayya a wann...
30/03/2026

SHIN KO SOYAYYA TANA DA AMFANI GA RAYUWAR MATASHI MAI NIYAR GINA KANSA?

A gaskiya idan za a faɗa kai tsaye soyayya a wannan mataki tana zama jinkiri ne ga matashi mai son gina kansa.

Ba wai saboda soyayya kanta mummuna bace amma saboda lokacin da ake yin ta da kuma nauyin da take ɗauka.

Matashi mai manufa yana buƙatar:
• Lokaci
• Hankali
• Ƙarfi
• Tsari mai ƙarfi

Amma idan ya shiga soyayya:
• Lokacinsa yana raguwa
• Hankalinsa yana rarrabuwa
• Yana fara fifita mutum sama da burinsa

A hankali:
• Yana rage ƙoƙari a rayuwa
• Yana shiga damuwa da tunani
• Yana kashe kuɗi a inda bai k**ata ba

Gaskiya mai ɗaci ita ce:
soyayya tana iya zama jaraba da zata karkatar da kai daga hanyar ka.

• Zata sa ka manta da burinka
• Zata sa ka jinkirta gina rayuwarka
• Zata sa ka ɗauki alhakin da baka shirya ba

Ka sani
ba lokaci bane na soyayya idan baka ginu ba lokaci ne na gina kanka da kafa rayuwarka.

• Ka fara da burinka
• Ka fara da tsarinka
• Ka fara da makomarka

Domin idan ka gina kanka, soyayya zata zo da sauƙi amma idan ka fara da soyayya, zaka iya rasa komai.

Kai a wane mataki kake yanzu kana gina kanka ne ko soyayya ta riga ta ɗauke hankalinka?

✍️ Habibu Umar

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Habibu Umar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share