
26/08/2025
Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Akko, Hon. Habib Hassan Kumo (Gatan Akko), ya kaddamar da rabon kayan abinci ga al’ummar ƙaramar hukumar Akko.
Taron kaddamarwar, wanda aka fara da mutanen da ke da buƙata ta musamman, ya gudana ne a ranar Litinin a garin Kumo, hedkwatar ƙaramar hukumar Akko.
Da yake jawabi, Hon. Habib Hassan Kumo ya bayyana godiyarsa ga samun damar tallafawa al’ummar sa, tare da jaddada cewa wannan ba shi ne karon farko da ake raba irin wannan kayan tallafi ba.
A nasu tsokaci, Alhaji Muhammad Seyoji, Galadiman Akko, da kuma Alhaji Marka, shugaban jam’iyyar APC a Akko, sun yaba da wannan mataki. Sun kuma yi kira ga sauran jagororin siyasa a yankin da su yi koyi da shi wajen tallafawa jama’a.
Shi ma Acrt. Usman Muhammad, wanda ke zama ko’odinetan hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas a Gombe, ya yi kira ga waɗanda s**a ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace domin amfaninsu da na iyalansu.
Wasu daga cikin waɗanda s**a amfana da tallafin sun nuna farin ciki da godiya ga Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Akko bisa wannan taimako, inda s**a ce hakan zai rage musu ɗaura da talauci tare da inganta rayuwar yau da kullum.