21/11/2025
Tsayuwar Daka a Ibadan: Yadda Kauran Bauchi, Dauda Lawal da Makinde S**a Ceto Mutuncin Jam'iyyar PDP
A babban taron da jam’iyyar PDP ta gudanar a Ibadan ranar Asabar da ta gabata, an ga wani sabon salo na shugabanci da jajircewa wanda ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa PDP har yanzu tana da waɗanda za su tsaya tsayin daka domin kare darajarta.
A cikin waɗanda s**a fito fili wajen nuna wannan kwazo, akwai Kauran Bauchi, wanda ya jagoranci aikin gyara da tsaftace jam’iyya da tsantseni. Tsayuwarsa wajen korar masu tada zaune tsaye a ciki, musamman waɗanda ke aiki da boyayyun manufa don rusa jam’iyyar daga cikin gida, ya zama abin yabo da koyi. A gaskiya, Kauran Bauchi ya zama ginshiƙin da ya hana jam’iyyar durkushewa.
Baya ga haka, Gwamnan Zamfara Dr. Dauda Lawal ya nuna irin kishinsa ga dimokuraɗiyya. Goyon bayansa ga sahihin tsari da adalci a cikin jam’iyya ya karfafa gwiwar mambobi da magoya baya, ya tabbatar masu cewa PDP na da shugabanni da ba za su lamunci karya ko shisshigi ba.
A bangaren Seyi Makinde, Gwamnan jihar Oyo, ya ba da cikakken gudunmawa wajen tabbatar da cewa taron Ibadan ya kasance sahihi, kuma cikin tsarin da ya dace. Makinde ya tabbatar da cewa jam’iyya ta gudana bisa ka’ida, ba tare da batan batu ko rikice-rikice ba, aikin da ya kara tabbatar da cewa PDP jam’iyyar da take da ni’imar shugabanni masu hangen nesa.
A tare, waɗannan manyan shugabanni uku sun yi abin da ake kira ceto martabar PDP, tare da dawo da yarda da kwarin gwiwar jama’a. Sun nuna cewa jam’iyyar adawa ba ta mutu ba, kuma ba za ta mutu ba, muddin akwai shugabanni irin su Kauran Bauchi, Dr. Dauda Lawal da Seyi Makinde.
A Ibadan, PDP ta sake tsayawa kan kafafunta kuma hakan ya sake busawa dimokuraɗiyya a rai.