Qudus News Hausa

Qudus News Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Qudus News Hausa, Newspaper, Gombe.

Gaza 🥲
10/05/2025

Gaza 🥲

Gaza🥲
04/05/2025

Gaza🥲

03/05/2025
YANZU-YANZU: Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Yahaya Sariy, ya sanar da cewa Dakarun Yaman sun kai wasu Hare-hare birnin H...
03/05/2025

YANZU-YANZU: Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Yahaya Sariy, ya sanar da cewa Dakarun Yaman sun kai wasu Hare-hare birnin Haifa da kuma Arewacin Isra'ila a jiya Juma'a.

Yahaya Sariy ya bayyana cewar makaminsu ya isa inda suke bukata ba tare da Isra'ila sun dakatar da shi ba.

Sannan ya kara da cewa za su ci gaba da kai farmaki Isra'ila domin taimakon al'ummar Palastinu har sai sun samu yanci.

"Nasara ta na ga Allah da Rasulullah da Muminai.."

Ahlul-bayt Radio/TV
03 – 05 – 2025

Takaitaccen Rahoto: Gobarar Daji a Isra'ila – Afrilu 30, 2025A ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, gobara mai girma ta tas...
01/05/2025

Takaitaccen Rahoto: Gobarar Daji a Isra'ila – Afrilu 30, 2025

A ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, gobara mai girma ta tashi a dazukan kusa da birnin Urushalima, lamarin da ya haifar da halin gaggawa a Isra'ila. Gobarar ta bazu cikin sauri sak**akon zafi da iska mai karfi, lamarin da ya tilasta rufe hanyoyi da kwashe mazauna al'ummomi fiye da tara.

An rufe manyan hanyoyi, ciki har da Highway 1 da 3, yayin da mutane fiye da 40 s**a jikkata – galibinsu sak**akon shakar hayaki. Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana lamarin a matsayin “halin gaggawa na kasa,” inda ya bukaci karin motoci da jiragen kashe gobara.

Isra'ila ta nemi taimako daga kasashen duniya, kuma kasashe k**ar Italiya, Siprus, da Girka sun turo jiragen kashe gobara. Rundunar sojin Isra'ila da kungiyoyin agaji na cikin aikin kashe gobarar.

Gobarar ta tilasta soke wasu taruka na bikin Yom HaZikaron da ranar 'Yancin Kai. Hukumomi na ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar, kuma an riga an k**a wasu da ake zargi da kone da gangan.

Ina so in nuna godiyata ga dukkan 'yan kishin kasa masu son zaman lafiya da 'yanci, da kuma 'yan Afirka masu kishin nahi...
01/05/2025

Ina so in nuna godiyata ga dukkan 'yan kishin kasa masu son zaman lafiya da 'yanci, da kuma 'yan Afirka masu kishin nahiyar, wadanda s**a hada kai a fadin duniya a ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, domin nuna goyon baya ga kudirinmu da hangen nesanmu na sabon Burkina Faso da sabuwar Afirka, 'yantacciya daga mulkin mallaka da sabuwar koloniyalizm.

Goyon bayan da kuka nuna da wannan alamar tausayi sun kara mana kwarin gwiwa cewa wannan gwagwarmayar da muke yi domin samar da duniya mai adalci da daidaito tana da tushe.

Ba za mu taba durkusawa a gaban kalubale ba; za mu tsaya tsayin daka har sai al'ummarmu sun samu 'yancin gaske. Tare da ku, muna da tabbacin cewa nasara akan miyagun hanyoyi tana gab da samu.

Tare da juna, cikin hadin kai, za mu fatattaki mulkin mallaka da sabuwar koloniyalizm don samun Afirka mai 'yanci, cike da mutunci da cikakkiyar mulkin kai.
CAPTAIN IBRAHIM TRAORE

Labari Da Dumi-Dumi!An K**a Manjo, jami’in Sojin Birtaniya a Najeriya Bisa Zargin Safarar Muggan Mak**aiManjo, jami’in r...
01/05/2025

Labari Da Dumi-Dumi!
An K**a Manjo, jami’in Sojin Birtaniya a Najeriya Bisa Zargin Safarar Muggan Mak**ai

Manjo, jami’in rundunar sojin Birtaniya an k**a shi daga hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) bisa zargin shigo da mak**ai ba bisa ka’ida ba cikin kasar.

An gano mak**an da s**a hada da bindigogi 57 na kiran AK-47, bindigogi shida masu harbi da famfo (pump-action), da fiye da harsasai 3,000 a wani filin sirri a jihar Delta.

Hukumomin DSS na ci gaba da bincike kan dalilin safarar wadannan muggan mak**an da yiwuwar alaka da kungiyoyin taaddanci na cikin gida da na waje..

Majiyar labari: ✍️The African Dream.

DA DUMI-DUMI: Cikakken RahotoMinistan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da ake samu...
27/04/2025

DA DUMI-DUMI: Cikakken Rahoto

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da ake samu a tattaunawar da ake yi tsakaninsu da Amurka. Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin farfado da yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015, wato JCPOA (Joint Comprehensive Plan of Action), wacce Amurka ta fice daga cikinta a zamanin Shugaba Donald Trump a shekarar 2018.

Araghchi, wanda ke jagorantar tawagar Iran a cikin tattaunawar da ake gudanarwa a birnin Vienna, ya ce ana samun ci gaba mai kyau, kuma akwai kyakkyawan fata cewa za a kai ga cimma matsaya mai kyau idan aka ci gaba da tattaunawa cikin gaskiya da nufin warware matsaloli.

Tattaunawar, wacce ke karkashin jagorancin ƙasashen da s**a rattaba hannu kan yarjejeniyar (Faransa, Birtaniya, Rasha, China da Jamus), na da nufin dawo da Amurka cikin yarjejeniyar tare da tabbatar da cewa Iran ta koma bin duk ka’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar.

Rahotanni na cewa ana gudanar da muhimman tattaunawa tsakanin wakilan Iran da na sauran ƙasashe, inda ake amfani da wakilai na biyu wajen musayar saƙonni da Amurka saboda Iran ba ta yarda ta zauna kai tsaye da Amurka ba har yanzu.

Araghchi ya bayyana cewa ko da yake akwai ƙalubale da dama, an samu sauye-sauye masu kyau da ke nuna cewa dukkan ɓangarori na da sha'awar ganin an samu nasara.

Haka kuma, jami’an diplomasiyyar Iran suna jan hankali cewa kafin Iran ta dawo cikakken bin yarjejeniyar, dole Amurka ta dage takunkuman tattalin arziki da ta kakabawa Tehran, wanda s**a shafi albarkatun mai da sauran manyan sassa na tattalin arzikin ƙasar.

Tattaunawar dai na ci gaba, kuma ana sa ran za a sami wani babban taro domin ɗaukar matakin gaba idan aka kammala warware sabani da ke tsakanin ɓangarorin.

AN KADDAMAR DA LITTAFIN “RAYUWATA” A ABUJADaga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Ranar Asabar 28 ga Shawwal 1446 (26/4/...
27/04/2025

AN KADDAMAR DA LITTAFIN “RAYUWATA” A ABUJA

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Ranar Asabar 28 ga Shawwal 1446 (26/4/2026) aka kaddamar da littafin tarihin Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda ya bayar da kansa mai suna “RAYUWATA”.

A yayin jawabinsa a wajen taron, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa: “Na fadi wani abu a takaice (a gabatarwan littafin), cewa, wannan littafi sak**ako ne na tunani da ya zo mana da muke tsare bayan waki’ar da aka sanya ma suna waki’ar Buhari, sai muka ga Allah Ta’ala ya bar mu da rai, tunda sun zo kisa ne kawai, ba yadda za a ce ma an rayu a wannan hali, amma dai da yake Allah ne me raya wa. K**ar yadda nace, Allah da ya kai Musa (AS) hannun Fir’auna, ya raine shi, sai ya kai mu hannunsu kuma, suna so su kashe amma kuma sai suna kula da mu.

“Sai muka ga to tunda dama ta samu, bari mu fadi wani abu wanda watakila in ba mu muka fada ba ba za a sani ba. Ita Malama sai ta yi rubutu; ita ta rubuta ne, ta saka da Ingilishi ‘A brief history of the Islamic movement.’ Ni kuma sai na yi bayani da baki, ina fada tana sajjalawa, muna yi k**ar muna magana ne, k**ar ma tana min tambayoyi ne ina amsawa, sai dai da aka rubuta littafin ba a sa tambaoyin nata ba, sai aka mai da shi littafi. Amma k**ar muna magana ne, idan mutum ya saurari sautin zai ji muna magana ne.” Inji Jagora.

Ya kara da cewa: “Kusan duk abin da na fada duk a takaice ne kuma a gurguje, domin kowane bangare na rayuwar zai zama akwai magana mai tsawo wanda shi kansa zai iya zama littafi. Alal misali, da zan ce zan bayar da labarin karatuna na zaure ne kawai, to ai zan yi littafi ne, amma kawai sai na fada a gurguje kawai. Haka karatun nizamiyya, shima zai iya zama littafi, amma shima sai ya tafi a gurguje. Kuma gidajen yari kowanne littafi ne.”

Shaikh Zakzaky ya yi tsokaci akan wasu daga kusa-kuran da aka samu daga aikin rubuta littafin daga ‘audio’ din bayanan, k**ar amfani da kalmar ‘na yi’ maimakon ‘in yi’, da kuma yadda aka rubuta sunayen wasu mutane ba daidai ba, wanda ya yi fatan za a gyara kafin a sake bugawa.

Jagora ya yi bitan wasu daga abubuwan da ya kawo a cikin littafin da s**a shafi rayuwarsa da darussan da za a dauka. Haka kuma ya kawo wasu daga darussan da ya bayar dangane da fitintinun da s**a rika aukuwa a cikin Harka sak**akon kusten makiya, inda ya ba da misalin wani rikici da ya riska bayan ya fito daga kurkukun Fatakwal karo na farko a tsakanin sistoci, da yadda ya warware shi. Da fitinar ‘yan Zuhudu da ita makiya s**a kurdo da ita, da fitinar Tawayiyya.”

Yace, “Makiya ba sun daina ba ne, an dinga kunno fitina kenan, in sun yi na waje, sai su yi na ciki. Da yake wadansu abubuwan duk sun dan fiffito a labarinmu na Tajriba da muke samu, har takai ma a wani lokaci da nake bayani nake cewa, yanzu duk wata fitina da za ta kunno kai, ana farata mun santa sarai. Mutum ko guna-guni ya fara yi, mukan ce ahan, dama an taba yi; Faqad madat sunnatil auwalin. An riga an yi irinsa.”

Sak**akon raba taron da aka yi kashi biyu; na safe da na yamma, a kowanne Jagora (H) ya samu fitowa ya gabatar da takaitaccen jawabi, inda a karshe ya yi wa ‘yan uwa nasiha akan yin abu don Allah. Yace: “Ko tagwaye ne ake rigima, sai ka ji guna-guni ana cewa Ummah ta fi son Hassan, ko ta fi son Husaini, dubi yadda take ji da shi. To haka nan abin ya gada, a yi ta guna-gunin, amma in ka sa kanka kana yin abinka don Allah ne, kar ka damu da komai, a haka nan nasara za ta zo.”

Ya kammala da cewa: “Amma in kace wai sai an kawar da duk matsaloli komai ya zama daidai, kowa ya zama ‘perfect’ to ai ba zai yiwu ba, kana neman ‘impossible’ ne, za ka bata lokacinka ne, a cigaba kawai haka nan, a yi ta yi kawai har a yi nasara insha Allah.”

Kafin jawabin Jagora (H), sai da aka gabatar da Dr. Hussaini Hassan, wanda ya yi sharhin littafin. Bayan tsokacin Jagora (H), an kira daidaikun ‘yan uwa da lajanonin Harka Islamiyyah, inda s**a sayi kwafin littafan. A cikin mako mai k**awa za a cigaba da kaddamar da littafin a Da’irorin kasar nan k**ar yadda kwamitin kaddamarwar s**a ba da sanarwa.






26/04/2025

DA ƊUMI-ƊUMI:Indiya ta janye jirgin ruwan yaƙinta mai ɗauke da jiragen sama, INS Vikrant, daga Tekun Larabawa, kuma baya...
27/04/2025

DA ƊUMI-ƊUMI:

Indiya ta janye jirgin ruwan yaƙinta mai ɗauke da jiragen sama, INS Vikrant, daga Tekun Larabawa, kuma baya cikin aikin kai farmaki kan Pakistan yanzu.

A halin yanzu, an ajiye jirgin a sansanin rundunar sojin ruwa na INS Karwar.

Da safiyar nan an yi nasarar shawo kan gobarar da ta tashi a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaei dake Bandar Abbas a ƙa...
27/04/2025

Da safiyar nan an yi nasarar shawo kan gobarar da ta tashi a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaei dake Bandar Abbas a ƙasar Iran k**ar yadda sanarwa ya fito daga kafar yaɗa labarai na Iran Military.

Sanarwan ya ƙara da cewa: "Godiya ga jirgin IRGC II-76, ma'aikatan jirgin sama masu saukar ungulu na Red Crescent, da kungiyoyin kashe gobara bisa namijin kokarinsu."

Ya zuwa hada wannan rahoto mun samu tabbacin rasuwar mutane 25 a yayinda mutane sama da 1,000 s**a jikkata k**ar yadda ma'aikatan kiwon lafiya na Iran ta bayyana.

"Nasara ta na ga Allah da Rasulullah da Muminai.."

Ahlul-bayt Radio/TV
27– 04 – 2025

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qudus News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category