ABU ANSAR TV

ABU ANSAR TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ABU ANSAR TV, TV Channel, Gombe.

Abu Ansar TV – Tashar yada ilimin addinin Musulunci, wa'azi, karatun Al-Qur'ani da shirye-shirye masu anfani ga al'umma.(إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَنْفَقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِج)

Bayan ya lashe gasar Ƙur'ani a'a Saudiya Abdurrahim ya dawo ya Najeriya kuma ya ci gaba da ja wa babansa baƙi a tafsirin...
23/06/2026

Bayan ya lashe gasar Ƙur'ani a'a Saudiya Abdurrahim ya dawo ya Najeriya kuma ya ci gaba da ja wa babansa baƙi a tafsirin da yake gabatarwa na satio-sati. ❤️

Wannan shi ne mai wuri ya zo mai tabarma sai ya naɗe. Daga dawowa Professor Mansur Isa Yelwa ya ce ai ba ka isa ba yaro, ba hutu, mu tafi ka ja baƙi....

Wannan abin ya min daɗi.

Allah ƙara masa albarka ka ƙara wa iyayenmu lafiya.

ABU ANSAR TV

23/06/2026
RAYUWA BA GASA BACE!!"Rayuwa ba gasa ba ce ta wa yafi wani kyan kaya ko dukiya, rayuwa gasa ce ta wa zai bar gurbi mafi ...
23/06/2026

RAYUWA BA GASA BACE!!

"Rayuwa ba gasa ba ce ta wa yafi wani kyan kaya ko dukiya, rayuwa gasa ce ta wa zai bar gurbi mafi kyau bayan tafiyarsa.

Sau da yawa muna shagala da gyara fuskarmu da suturarmu, amma muna mancewa da gyara zukatanmu da mu'amalarmu.

Mutuncin mutum ba ya ga abin da yake nunawa a fili, yana ga abin da yake aikatawa lokacin da babu kowa sai Allah.

Ya dace kalamanmu su zama magani, ayyukanmu su zama haske,rayuwarmu kuma ta zama darasi ga waɗanda za su zo bayunmu.

Wane gurbi k**e fatan ki bari a zuciyar mutane bayan baki?

ABU ANSAR TV

DAGA AL-QUR'ANI KAI TSAYE: SU WAYE MATA NAGARI?Sheikh Dr. Mansur Isah Yelwa Hafizahillah ya ce:Akwai wasu mutane da suke...
23/06/2026

DAGA AL-QUR'ANI KAI TSAYE: SU WAYE MATA NAGARI?

Sheikh Dr. Mansur Isah Yelwa Hafizahillah ya ce:

Akwai wasu mutane da suke ganin
nagartar mace tana auna ne da yawan sallarta,
Yawan azuminta, yawan sadakarta ko
Kuma yawan hajjin da ta yi.

Amma Allah Madaukakin Sarki ya nuna
cewa akwai wani babban ma'auni
Da mutane da yawa suke mantawa da shi.

Allah Ya ce:
Arrijalu qawwamuna alan nisa...

Sannan Ya ci gaba da cewa:
Fassalihatu qanitat...

Malam ya ce:
Ka lura, Allah da kansa ya fara bayanin waye mace ta gari.

Ya ce:
Fassalihatu — Mata nagari.

Sai Ya bayyana sifarsu:
Qanitat — Masu biyayya.

Malam ya ce,
Allah bai fara da cewa mata nagari su ne
masu yawan nafila ba, ko masu yawan azumi ba,
Ko masu yawan Umara ba.

Sai dai Ya fara da sifar biyayya da mutunta
Tsarin da Allah Ya kafa a cikin aure.

Saboda haka, idan ana son a san
wace ce mace ta gari a wurin Allah,
ba wai kawai a duba yawan ibadarta ba.

A duba yadda take kallon matsayinta a cikin gida.
A duba yadda take mu'amala da mijinta.
A duba yadda take girmama umarnin Allah a rayuwar aurenta.

Malam ya ce:
Akwai mace mai yawan ibada,
Amma tana raina tsarin da Allah Ya kafa.

Akwai kuma mace mai sauƙin hali,
Mai biyayya, mai kiyaye hakkokin gidanta,
Wadda Allah Ya sanya cikin jerin "Fassalihatu Qanitat."

Don haka, Musulunci bai zo ya tauye mace ba.

A'a, ya zo ne ya ɗaukaka ta, ya ba ta matsayi,
ya nuna mata hanyar da za ta samu yardar Allah da Aljannah.

Duk wanda yake son sanin ma'aunin
nagarta a wurin Allah, to ya koma ga abin da Allah Ya faɗa,
Ba abin da ra'ayin mutane ko zamani suke faɗa ba.

Allah Ya sa mu fahimci addininmu yadda ya kamata.

🤲 Allah Ka ƙara wa Sheikh Dr. Mansur Isah Yelwa lafiya,
albarka da tsawon rai a kan alkhairi.
Ka saka masa da aljannar Firdausi
saboda ilmantar da al'umma. Amin.

🤲 Masu sharing wannan saƙo,
Allah Ya saka muku da alkhairi.
Ya gyara mana zukatanmu,
Ya sa mu karɓi gaskiya idan ta zo mana,
Ya ba maza da mata ikon yin rayuwa bisa
Koyarwar Al-q

Female Section 3rd position goes to Amatulhakim Ibrahim jaloDaga jahar Taraba 🏆🤗🥰Allahumma barik 🙏💯ABU ANSAR TV
23/06/2026

Female Section
3rd position goes to Amatulhakim Ibrahim jalo

Daga jahar Taraba 🏆🤗🥰

Allahumma barik 🙏💯

ABU ANSAR TV

🚨HAFIZAH MAIMUNA.•Ita wannan shahararriya ce bata buƙatar sai an muku bayanin ta da kuma yadda karatun ta yake da nutsuw...
23/06/2026

🚨HAFIZAH MAIMUNA.

•Ita wannan shahararriya ce bata buƙatar sai an muku bayanin ta da kuma yadda karatun ta yake da nutsuwa da kuma motsa zuciya, kusan kowa ya santa kuma yaji karatunta.

•Ta shahara da karatu da Riwayar Khalaf, kuma babu shakka ta ƙware matuƙa a karatu da wannan Riwayar, kusan tana daga cikin Mata mahaddata a Nigeria da s**a fara shiga Duniyar ɗaukaka, su uku ne, da ita da Aisha Muhammad Auwal, Fatima Ahmad Tijjani, waɗannan Matan sunyi lokaci.

•Musabaƙar da aka gabatar a Borno wannan shekarar da ta wuce, da yawan mutane sunyita zaman jiran Gona ta hau kan kujera, tana daga cikin 'yan takarar da ake da sa rai akan su, kuma Alhamdu lillah duk da bata samu lamba ba amma dai tayi karatu mai cikeda nutsuwa.

Allah ya ƙarawa rayuwar ta Albarka Ameen.
ABU ANSAR TV

😭 Ya kai mijin da matarka ta kamu da rashin lafiya, aka rubuta mata magani, amma ka ƙi siya mata alhali kana da iko... k...
23/06/2026

😭 Ya kai mijin da matarka ta kamu da rashin lafiya, aka rubuta mata magani, amma ka ƙi siya mata alhali kana da iko... ka ji tsoron Allah!

Ka tuna cewa wannan Matar taka, ta bar gidan iyayenta ne domin ta zauna tare da kai.

Ita ce mai kula da gidanka, mai rainon 'ya'yanka, mai taya ka murna idan ka samu nasara, kuma mai tausaya maka idan ka shiga damuwa.

Yaya zuciyarka za ta yarda ta ga wannan Matar taka tana ciwo, taje asibiti an rubuta mata magani tana riƙe da takardar magani tana cewa ka siya mata, amma ka juya mata baya?

Manzon Allah ﷺ yace:
"Ya isa mutum zunubi ya tozarta waɗanda ciyar da su ya wajaba a kansa."

Matarka amana ce a hannunka, rashin kula da lafiyarta ba kawai rashin tausayi ba ne, har ma cin amana ne da Allah zai tambaye ka a kai ranar Alƙiyama.

Wata rana kai ma za ka iya kwanciya a gadon asibiti kana buƙatar wanda zai kula da kai.

Idan ka shuka tausayi, tausayi za ka girba, Idan ka shuka wulakanci da sakaci, sakamakonsa zai dawo gare ka.

😭 Ka siya mata magani kafin ka siyawa kanka abin more rayuwa.

😭 Ka kula da lafiyarta kamar yadda kake son a kula da taka.

😭 Ka tuna cewa addu'ar wanda aka zalunta ba ta da shamaki tsakanin ta da Allah.

Allah yasa mazajenmu su zama masu tausayi da kyautatawa ga iyalansu, ya sanya gidajen Musulmi cike da rahama da jinƙai.🤲💕
ABU ANSAR TV

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ABU ANSAR TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category