24/08/2026
🚨 GWARZUWAR HIZB 60 DAGA ƘASAR GHANA.
•Wannan itace Allah ya bata nasarar samun lamba ta ɗaya a haddan HIZB 60 a Musabaqar Duniya da aka gudanar a ƙasar Saudiyya kuma 'yar Ghana ce.
•Allah ya yiwa yankin Afrika baiwar Al-Qur'ani, ta yadda suke iya zuwa cikin larabawan da aka saukar da Al-Qur'ani da yaren su amma kuma su iya samun nasara akan su tare da taimakon Ubangiji.
•Ɗazu na ɗan bi ta kan wani rubutu da wani juyayye mai ƙaramin fahimta yayi akan yadda 'yan Nigeria da 'yan Afrika suke samun nasara a Musabaqar Duniya, yana nuna cewar ana basu ne don a ƙarfafe su amma ba wai don ƙoƙarin su yakai ba.
•To kunga shi wannan ba'a kallon sa ballantana a saurari maganar sa, domin Al-Qur'ani an saukar dashi ne kawai da harshen Larabci amma ba larabawa bane kaɗai aka saukarwa dashi ba, saboda haka kowa zai iya koyon sa kuma ya ƙware acikin sa koda ko ba balarabe bane, haka kuma za'a iya samun balaraben da bazai iya karantawa ba duk da cewar da yaren nasu aka saukar dashi.
Allah ya ƙara mana Ni'imar Al-Qur'ani kuma yasa yayi mana jagora zuwa Aljannah Amin.