Abbass Abubakar

Abbass Abubakar Abbas Abubakar is a driven and innovative individual passionate about making a positive impact

BREAKING: The DSS has arrested 5 people connected to the school kidnapping in Papiri, Niger State. Many weapons includin...
31/05/2026

BREAKING: The DSS has arrested 5 people connected to the school kidnapping in Papiri, Niger State. Many weapons including 15 AK-47 rifles and over 1,400 bullets. Two foreigners were also arrested for allegedly helping the kidnappers.

A Lokacin Yaki Gulf na 1991, Saddam Hussein ya kai ajiyar jiragen yakinsa Iran don ka da a lalata suA lokacin Yaƙin Teku...
18/01/2026

A Lokacin Yaki Gulf na 1991, Saddam Hussein ya kai ajiyar jiragen yakinsa Iran don ka da a lalata su

A lokacin Yaƙin Tekun Gulf na 1991, an yi amfani da fasahar zamani wajen yaƙi. Iraki ta yi jigilar wani kaso mai yawa na jiragen rundunar sojin samanta (IQAF), wanda aka kiyasta ya kai tsakanin jiragen sama 100 zuwa 150+, zuwa Iran don gujewa halakasu daga sojojin kawancen da Amurka ke jagoranta.

Saddam Hussein ya dauki wannan matakin ne don kare mafi kyawun jiragen yakinsa da yin jigilar zuwa Iran, don amfani da su nan gaba, yana mai daukar Iran a matsayin mafaka "mai aminci".

An lalata manyan ramukan karkashin kasa na Iraki da bama-bamai masu sarrafa kansu da aka tsara bisa ka'ida. Saboda haka Iraq taji tsoron lalata jiragen ta gaba daya, Saddam ya aika da jiragen zuwa Iran, yana fatan za a dawo da su bayan yakin.

Jiragen da ta aika sun haɗa da manyan samfura k**ar Su-24 Fencer, Mirage F1, MiG-29 Fulcrum, da Su-25 Frogfoot, da kuma jiragen sufuri na Il-76 da jiragen fasinja na Iraqi Airways.

Duk da cewa Iran ita ce babbar makiyar Iraki a lokacin Yaƙin Iran da Iraki na 1980-1988, Iran ta bar jiragen su sauka amma nan take ta kwace su.

Bayan ƙarshen Yaƙin Tekun Fasha, Iran ta ƙi mayar da jiragen, tana mai da'awar cewa sun zama diyya ta yaƙi, saboda barnar da Iraki ta yi a rikicin da s**a yi na shekaru takwas a baya.

Iran ta gyara yawancin waɗannan jiragen sama ta kuma haɗa su cikin rundunar sojin saman ta (IRIAF).

A wani sauyi na tarihi, rahotanni sun nuna cewa Iran ta mayar da kimanin jiragen sama 88 zuwa Iraki a shekarar 2014 don taimakawa gwamnatin Iraki a yakin da take yi da ISIS.

Mai son karin bayani ya rubuta a Google k**ar haka: Iraqi Warplanes Flee to Iran 1991.

Gwamnan Jihar Yamma Chief Samuel Ládòkè Akíntọ́lá Yana Cikin Wadanda S**a Rasa Ransu A Ranar Juyin Mulkin Watan Junairu ...
16/01/2026

Gwamnan Jihar Yamma Chief Samuel Ládòkè Akíntọ́lá Yana Cikin Wadanda S**a Rasa Ransu A Ranar Juyin Mulkin Watan Junairu 1966

An kashe Chief Samuel Ladoke Akintola a ranar 15 ga Janairu, 1966, a lokacin juyin mulkin soja na farko a Najeriya.

An kashe shi a gidan gwamnati da ke Iyaganku GRA, Ibadan, wanda ya kasance fadar mulki ta Firimiyan Yankin Yamma.

Kisansa wani ɓangare ne na "Juyin Mulki wanda ya yi sanadiyyar asarar manyan 'yan siyasa da dama a faɗin Najeriya, sannan ya kawo ƙarshen Jamhuriya ta Farko a ƙasar.

A cewar rahotanni daga iyalinsa, kimanin sojoji 50 ne, su ka kewaye gidansa har tsawon awanni da dama. Maimakon barin sojoji su yi harbi a gidan da iyalinsa ke ciki, Akintola daga ƙarshe ya bar gidan don fuskantar maharan kai tsaye.

An gano gawarsa a cikin jini a ƙofar gidansa washegari da safe.

A lokacin rasuwarsa, ya riƙe muƙamin Aare Ona Kakanfo na 13 (Field Marshal Janar) na ƙasar Yarabawa. Muƙamin da ya kasance babu wanda ya sake rike shi a ciki tsawon shekaru 21 har sai da aka nada Chief MKO Abiola a shekarar 1988.

Dangantakar Akintola Da Sardauna

Samuel Akintola da Ahmadu Bello Sardauna, manyan abokan siyasa ne a lokacin Jamhuriyar Farko ta Najeriya (1960–1966). An bayyana dangantakarsu ta hanyar sadaukarwa tare' ga haɗin kan ƙasa ta hanyar haɗin gwiwa mai mahimmanci, wanda a ƙarshe hakan ya ba da gudummawa ga mutuwarsu a juyin mulkin soja guda ɗaya.

Ƙungiyar NNA

Akintola, Firimiyan Yankin Yamma, ya ƙulla wani ƙawance na dabarun siyasa da Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Yankin Arewa. Jam'iyyar Akintola ta National Democratic Party (NNDP) ta haɗa kai da Jam'iyyar Northern People's Congress (NPC) ta Sardauna don kafa ƙungiyar Nigerian National Alliance (NNA).

Akintola ya yi imanin cewa domin al'ummar Yarabawa su amfana daga "abin da ya shafi ayyukan ƙasa" daga gwamnatin tarayya, suna buƙatar haɗin gwiwa da Arewa, maimakon su ci gaba da zama yan adawa. Wannan matsayi kai tsaye ya haifar da rashin jituwa tsakaninsa da tsohon maigidansa Obafemi Awolowo.

Girmama Juna

Labarai na tarihi sun bayyana dangantakarsu a matsayin wacce ta kasance ta girmamawa ga juna. Sardauna ya dauki Akintola a matsayin babban abokin aiki amintacce, wanda sau da yawa yakan karbi bakuncinsa a Kaduna.

Gargaɗi na Ƙarshe

A ranar 14 ga Janairu 1966, ƙasa da sa'o'i 24 kafin a kashe su, Akintola ya tashi zuwa Kaduna don ganawa da Sardauna. An ruwaito cewa ya yi wa Sardauna gargaɗi game da juyin mulkin soja da ke tafe, yace suyi kokari su tafi gudun hijira, amma Sardauna ya zaɓi ya yi zamansa, yace babu in da za shi, idan sun mutu kwanansu ne ya kare, idan sun mutu sun gaji iyayensu ne da kakanninsu, don haka mutawa gado ce babu in da zai je.

Sardauna ya raka Akintola zuwa filin jirgin saman Kaduna, s**ayi bankwana, ashe rabuwar kenan. Akintola ya koma Ibadan a wannan maraicen, inda sojoji s**a kashe shi awanni kadan bayan haka. Shi kuma Sardauna daga wannan rakiyar, awa biyar rak ya kara a duniya.

Kisa Tare

Shugabannin biyu su ne manyan wadanda aka yi wa juyin mulkin ranar 15 ga Janairu, 1966 karkashin jagorancin Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu da sauransu. An kashe Bello a gidansa da ke Kaduna, sannan aka kashe Akintola a gidansa da ke Ibadan.

Takaddama a Yammacin Kasa

Duk da cewa wasu suna ganin kawance, a matsayin mai amfani, amma mutane da yawa a Yankin Yammaci Najeriya su na kallon dangantakar Akintola da Sardauna a matsayin "cin amana" ga muradun Yarabawa, wanda ya haifar da tashin hankalin siyasa na "Operation Wetie" na 1965.

Tasirin A Ƙasa

Ƙawancen da s**a yi ya ƙarfafa tushen siyasa na Arewa da Yamma (Yarabawa), wani tsari da ke sake bayyana a siyasar Najeriya har zuwa yau.

ME KE SHIRIN FARUWA A “MIDDLE EAST” NE?🌍 Cikin 'yan kwanakin nan Trump ya dage sai ya kai farmaki kan kasar Iran, saboda...
15/01/2026

ME KE SHIRIN FARUWA A “MIDDLE EAST” NE?

🌍 Cikin 'yan kwanakin nan Trump ya dage sai ya kai farmaki kan kasar Iran, saboda abubuwa 3 kacal:

— Faranta wa Israel don cikar burinta (dominance)

— Gwagwarmayar jaddada superpower (global superpower)

— Rage karfin China da Russia (geopolitics & competition)

Wannan farmakin da yake shirin kai wa ya saba dukkan ka'idojin international law, ko da yake daman ya ce shi ba ya bin international law, kawai yana yin abun da ransa yake so ne.

To, a cikin wannan shekarar ya mamaye kasar Venezuela, ya k**a shugabanta, ya kuma tilasta cewa oil dinta direct za a kai US, akalla 30-50 million barrels.

Wannan lamari ba karamin abu ba ne a wajen China, saboda an kwace mata customer, an yanke hulda tsakaninsu, kuma ana neman mamaye sauran ma.

— China yanzu ita ce take cin karenta babu babbaka a bangaren business, tana da industries na komai, kuma tana da huge market. A hankali kasashen duniya suna komawa cinikayya da ita saboda saukin abubuwa.

— Nan gaba kadan wadannan kasashen za su rage amfani da Dollar za su koma karkashin BRICS, kuma hakan babbar barazana ce ga Dollar. Bugu da kari, a yanzu haka tattalin arzikin US ya fara kuka (forecast ya nuna nan da shekaru kadan ba za su tsira ba), kuma ga mugun bashin da ya musu yawa, wajen $38 trillion.

— Wadannan manyan industries da China take kan fadadawa a matsayinta na #2 a tattalin arzikin duniya, dole suna bukatar huge oil da customers don su rayu. Manyan kasashen da suke ba ta mai su ne: (i) Russia, (ii) Saudi Arabia, (iii) Iran, duk da cewa yanzu suna accelerating renewables, nuclear, da EVs don su rage dogaro da mai

— Alakarsu da Venezuela da sauran kasashen ita ce, suna ba su mai, su kuma su sayar musu kaya. To yanzu Trump ya hana. Ya ce duk wani kayan da Venezuela take bukata, sai dai ta saya daga US, sannan su ba su mai

— Kenan idan US ta karbi iko da kasashen da suke alliance da China, direct hakan zai shafi China ne ta fuskar business sosai. Hakan kuma babban tashin hankali ne, saboda China ita ce #2 a yawan population na duniya, akwai barazana wajen ciyar da mutanenta. Kuma idan karfinta ya ragu, to dole ta manta da batun BRICS ta ci gaba da relying da Dollar

— Idan har Trump bai tashi tsaye ya tabbatar da wadannan abubuwan da yake fafutuka a kai ba, hasashe ya nuna cewa nan da wasu shekaru US ba za ta iya daukar nauyin kanta ba, ga bashi ya yi yawa, kuma ga yawan population, shi ya sa yake deporting immigrants

Now, bayan duk manyan sanctions din da suke bugawa Iran, amma har yanzu tana ci gaba da numfashi, kuma sai Iran din s**a dauko sabon salon bypassing amfani da Dollar a international business.

To dama tun da ba sa ga maciji, sai s**a fito da sabon shirin tada hatsaniya a cikin gida don kifar da gwamnatin, amma ba su yi nasara ba, sai yanzu ya ce suna shirin kai farmaki da sunan Iran tana take hakkin Dan Adam. Regime change din dai shi ne cikar burin Israel na tabbatar da wancen kudirin nata, kuma shi ne zai ba wa US damar juya Middle East tunda Iran ce kadai mai taurin kai a cikin kasashen da ke da power da resources.

Idan hakan ya tabbata, zai tabbatar da:

— Jaddada superpower na US

— Rage wa China da Russia karfi

— Faranta wa Israel rai na kawar da abokan hamayyarta da cikar burinta

Idan China da Russia s**a rasa kasashe a ME da Africa, za su shiga babbar matsala. Kuma hakan ne zai kara tabbatar da US a matsayin superpower. Ga kudi, ga mulki, kuma ga power!

A yanzu dai Saudi Arabia da Qatar sun ce ba za su bari a mayar da ME battlefield ba ta hanyar amfani da kasashensu don kai wa Iran farmaki, don haka daga dukkan alamu US za ta yi amfani da warships dinta ne wajen kai farmakin, kuma reports sun nuna already aircraft carrier dinta ya isa Red Sea.

Idan har US ta kai farmakin, Iran ta ce za ta rama a kan duk military bases dinsu da ke ME (duk da cewa US ta fara kwashe sojojinta a yankin) kuma za ta yi lisi-lisi da Israel, hakan ya sa mutane s**a fara neman shelters tun wuri suna buya.

Bayan duk wadannan, wasu tensions din kuma su ne:

— Trump ya dage sai ya mamaye Greenland ko da ta karfij soji ne k**ar yadda ya ce

— Macron yana shirin fitar da France daga kungiyar NATO

— Europe suna neman shiga ruguntsumi da Russia
..da sauransu

Masana suna ganin cewa matukar Trump bai janye son zuciyarsu ba, wadannan escalations din za su iya janyo WW3. Yanzu dai duk ido ya koma ME, ana jira a ga me zai faru cikin wannan makon.

Allah Ya tsare mu da tsarewarSa. Amin.

26/12/2025

Today news

17/11/2025
Mr. Donald Trump    mere rhetoric rococo's He was  planning and targeting our mineral resources And Nigeria take no stan...
14/11/2025

Mr. Donald Trump mere rhetoric rococo's
He was planning and targeting our mineral resources
And Nigeria take no stand which what Israel occupation in Gaza
There's many to listing politically.
He just mentioned Christian genocide ironically but they know what is really happening in Nigeria.

12/11/2025

Congratulations Abokina
Allah ya kawo babban rabo

Address

Kashere Town
Gombe
771103

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abbass Abubakar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share