Jaridar AREWA

Jaridar AREWA Sahihan labarai na yankin arewa a yau

Wafatin Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) 21 Ga Watan Ramadan Shekara Ta 40 Bayan Hijira Sayyidina Ali bin Abi Talib (AS) ya y...
11/03/2026

Wafatin Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) 21 Ga Watan Ramadan Shekara Ta 40 Bayan Hijira

Sayyidina Ali bin Abi Talib (AS) ya yi shahada a ranar 21 ga watan Ramadana, shekara ta 40 bayan hijira (40 AH), bayan da Abdurrahman bn Muljam ya soka masa takobi mai dafi a masallacin Kufa yayin sallar asuba. Ya yi wafati yana da shekaru kusan 63 a duniya, wanda hakan ya kawo karshen halifancinsa. An soka masa takobi a Masallacin Kufa, Iraki, a ranar 19 ga Ramadana, baiyi wafati ba sai bayan kwanaki 2, a ranar 21 ga watan Ramadan.

Imam Ali (AS) ya bar gado mai girma na ilimi, adalci, da sadaukarwa, kuma ana tunawa da shi a matsayin daya daga cikin mafi girman sahabbai da kuma shugabannin Musulunci.

EVANGELIST USMAN YA MUSULUNTA. Daga Muhammed Sani Munkailah Matashin Pastor wanda ya shahara mai suna Usman Ɗan fulani y...
28/02/2026

EVANGELIST USMAN YA MUSULUNTA.

Daga Muhammed Sani Munkailah

Matashin Pastor wanda ya shahara mai suna Usman Ɗan fulani ya musulunta bayan kwakkwawar tattaunawa tsakanin sa ba Mallam Adamu ashaka da Mallam baban chinedu a wannan makon.

Evengelist ɗin ya kai wa shararen malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Abubakar gumi ziyara bayan dowawar sa musulunci

Allah ya tabbatar mu cikin addinin Musulunci.

Kuyi like na Jaridar AREWA domin samun labarai DA ƊUMI-ƊUMIN SU.

CHINA ABOKIYAR KIRKI .Daga Muhammed Muhajir Aliyu Bayanani daga China pulse ya tabbatar da cewa lran tayi amfani da taur...
28/02/2026

CHINA ABOKIYAR KIRKI .

Daga Muhammed Muhajir Aliyu

Bayanani daga China pulse ya tabbatar da cewa lran tayi amfani da tauraron dan adam ne na china duka domin gano sansanij sojin Amurka duka a gabas ta tsakiya .

Kada ku manta ko sati ba'a yi ba China ta sai da makamin Hyperasonic sama da dubu uku ga lran

Wannan ƙawance Allah ya masa albarka , tabbas yayi armashi .

Allahumma a izzal islama wal muslimin

Kuyi like na Jaridar AREWA

TSARKI YA TABBATA GA ALLAHDaga Mallam Bolari A wani mataki na mayar da zazzafan martani, |ran ta sanya wa yakinta sunan ...
28/02/2026

TSARKI YA TABBATA GA ALLAH

Daga Mallam Bolari

A wani mataki na mayar da zazzafan martani, |ran ta sanya wa yakinta sunan "The Seal of the Blood" (Hatimin jini)

|ran ta harba samfurin makamanta na linzami wanda ake kira hypersonic missiles zuwa |sra¡|a wanda a yanzu haka b¡ran£n |sra'¡|a suna shan wuta

Yaa Allah Ka sa kàrshen |sra'¡|a ne yazo.

Kuyi Like na Jaridar AREWA

IRAN TA KAI HARE-HARE MANYAN SANSANONIN SOJIN GABAR TA TSAKIYA..Daga Jaridar AREWA Askarawan Juyin juya Halin Iran sun m...
28/02/2026

IRAN TA KAI HARE-HARE MANYAN SANSANONIN SOJIN GABAR TA TSAKIYA..

Daga Jaridar AREWA

Askarawan Juyin juya Halin Iran sun maida martanin hare hare a sansanin sojin Amurka da suke gabar ta tsakiya a safiyar Asabar.

Hare haren na faruwa ne jin kaɗan bayan da Amurka da Isra'ila s**a kaddamar da hare hare a kasar Iran ciki har da Babban birnin kasar ta Tehran.

An tabbatar da hare haren ramuwa ga ƙasashen da suke da sansanonin soji na Amurka a gabar ta tsakiya
(1) Hariq air base IRAQ
(2) Al tanf garrison base SYRIA
(3) Ali al salem base. KUWAIT
(4) US navy fifth fleet. BAHRAIN
(5) Al udeid air base QATAR
(6) Al dhafra air base UAE

Allah ka kawo saukin wannan Rikicin.

Shugaban kasar Amurka Donald trump ya tabbatar da aniyar sa na yaƙar ƙasar Iran, ya fita da sanarwar ne. Daga Jaridar AR...
28/02/2026

Shugaban kasar Amurka Donald trump ya tabbatar da aniyar sa na yaƙar ƙasar Iran, ya fita da sanarwar ne.

Daga Jaridar AREWA

In da tuni aka fara kai munanan hare-hare kasar Iran in da hare sun kai wajen 30 a mabanbanta wajaje da kuma jefa misilles bomb sama da 50.

Shugaban kasar Amurka Donald trump ya ayyana cewa zasu kwace Iran tare da ƙona dukkan inda suke da karfi, sannan kuma ƙasar ba zasu taɓa mallakar nukiliya a hukumance ba.

Ya ƙara da cewa, bayan sun gama da ƙona manyan sansanonin soji da na gwamnatin kasar Iran zasu afkawa shugabannin ƙasar.

Sannan ƙasar za ta dawo karkashin ikon su.

Allah ya taimaki Iran yasa su yi nasara.

Wannan bawan Allah yana cikin wanda akayi garkuwa da su wanda bidiyon sa, ya zaga kafafen yada Labarai. Yana cikin wani ...
27/02/2026

Wannan bawan Allah yana cikin wanda akayi garkuwa da su wanda bidiyon sa, ya zaga kafafen yada Labarai. Yana cikin wani hali na taɓuwa da kuma rashin lafiya.

Ya tabbatar da cewa yayi wajen wata shida a wajen Ƴan garkuwa da mutanen.

Sannan kuma yana dab da rasa ganin sa, Dan yanzu ma baya kallo sosai.

Jaridar AREWA ta bi sahun Al'ummar Arewa ta na ƙara ƙira akan Gwamnatoci da jami'an tsaro su bi dukkan hanyar da ta dace domin yaƙi da wannan Al'amari domin dawo da martaban yankin arewa.

Wasu daga cikin Hotuna da s**a ta da Hankalin Al'ummar arewa a kwana kwanan nan. Sun nuna yadda akayi garkuwan wani wand...
27/02/2026

Wasu daga cikin Hotuna da s**a ta da Hankalin Al'ummar arewa a kwana kwanan nan.

Sun nuna yadda akayi garkuwan wani wanda ya gama bautar ƙasa kwanan nan da wasu mata guda wanda suke riƙe a wajen ƴan ta'adda cikin halin Rayuwa ko mutuwa.

Mutanen ƙasar Nigeria suna ta ƙiraye-ƙiraye akan gwamnatoti su yi iya yin su domin kawo ƙarshen wannan Ta'addancin.

Daga Jaridar AREWA

27/02/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR-RAJIUM

Wani Video mai firgici da tozarci ya fito in da wani daga cikin ƴan satan mutane Domin neman kuɗin fansa, yake ta dukan wani daga cikin wanda s**ayi garkuwa dashi.

Bidiyon yana daga cikin wanda ss**a ɗagawa mutane hankali.

Inda a kwana kwanan nan, wannan Aiki na garkuwa da mutane da kuma da farmaƙin garuruwa musamman Alƙaryu yake sake ta'azzara a yankunan Arewa.

Mutane suna ƙira da gwamnatoci na tarayya da na garuruwa da su tashi su haɗa karfi da dabaru domin yaƙi da Ta'addanci da ya jefa yankunan Arewa cikin zulumi.

Kuyi like da share na
Jaridar AREWA domin samun labarai daga yankin arewacin Nigeria

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar AREWA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share