Arewa dae

27/04/2026

baza Abarmu bayaba.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana matsayin sa ne dangane da taɓarɓarewar tsaron da Najeriya ke ci ga...
27/04/2026

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana matsayin sa ne dangane da taɓarɓarewar tsaron da Najeriya ke ci gaba da fuskanta, wanda ke kai ga rasa ɗimbin rayukan jama’a.
Obasanjo ya jaddada cewar, kare rayukan jama’a da dukiyoyin su, su ne sahun gaba a kundin tsarin mulki, saboda haka duk gwamnatin da ta gaza yin haka, ba ta da hurumin ci gaba da zama a karagar mulki.

25/04/2026
ƴan ta’addan sun kuma yi awon gaba da baburan da sojojin ke aiki da shi a yankin baya ga wata motar yaƙi guda.A cewar ma...
20/04/2026

ƴan ta’addan sun kuma yi awon gaba da baburan da sojojin ke aiki da shi a yankin baya ga wata motar yaƙi guda.

A cewar majiyoyin da misalin ƙarfe 3 na tsakaddaren jiya ne ƴan ta’addan s**a farmaki Kemanji guda cikin ƙauyukan da ke zagayen gandun dajin Kainji, guda cikin dazukan da mayaƙan Ansaru ke ɓoye.

Guda cikin masu gadin gandun dajin da ya nemi a sakaya sunanshi ya ce a tsakaddaren ne mayaƙan s**a fito daga dajin kuma kai tsaye s**a nufi kan sansanin sojin tare da buɗe musu wuta.

Ganau ɗin ya ce nan take ne ƴan ta’addan s**a kashe sojojin guda 3 tare da jikkata wasu 4.

Wata majiya ta daban daga ƴan sakan da ke taimakawa sojojin, ta ce sojojin sun kashe ƴan ta’adda da dama a harin na tsakaddare.

Har zuwa yanzu dai rundunar sojin Najeriya da ƴansandan jihar ta Kwara basu tabbatar da faruwar harin ba, haka zalika ko da manema labarai s**a tuntuɓe su basu ce komai kan lamarin ba.

An Hana Daliba Rubuta Jarabawar JAMB Saboda Ta Ki Cire Hijabinta A Yayin Da Zata Shiga Dakin JarabawaWata daliba ta kasa...
19/04/2026

An Hana Daliba Rubuta Jarabawar JAMB Saboda Ta Ki Cire Hijabinta A Yayin Da Zata Shiga Dakin Jarabawa

Wata daliba ta kasa rubuta jarabawar share fagen shiga Jami'a JAMB bayan da aka bukace ta cire hijabinta a gaban jama’a kafin shiga dakin jarabawa.

Rahotanni sun nuna cewa dalibar ta ki amince wa da cire Hijabin nata, lamarin da ya sa aka hana ta shiga rubuta jarabawar, abin da ya jawo cece kuce a Shafukan sada zumunta.

Cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta an ga lokacin da wani jami'in tsaro ya kori dalibar bayan da ta ki cire hijabin nata.

Wasu na kallon lamarin a matsayin tauye hakkin Addini, yayin da wasu ke ganin yana da nasaba da dokokin tsaro da aka kafa a wuraren jarabawa.

Arewa Trends Don Samun Ingantattun Labarai Mun Gode

Kowane ɗan Najeriya ana binsa bashin naira dubu 724,000 sakamakon yawan bashin da ake bin ƙasar na naira tiriliyan 159 d...
16/04/2026

Kowane ɗan Najeriya ana binsa bashin naira dubu 724,000 sakamakon yawan bashin da ake bin ƙasar na naira tiriliyan 159 da biliyan 280.

Rahoton baya-bayan nan da ofishin kula da basuss**a na ƙasar ya fitar, ya bayyana yadda bashin Najeriya ya ƙaru matuƙa, saboda ciyo sabbin bas**a da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi daga cikin gida da kuma ƙetare.

Ƴan Najeriya na ta shaci faɗi da kokwanta haƙikanin abin da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya faɗi ...
16/04/2026

Ƴan Najeriya na ta shaci faɗi da kokwanta haƙikanin abin da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya faɗi dangane da burinsa na neman shugabancin Najeriya, inda ya ce ba zai sake takara ba bayan wadda zai yi a 2027.

Atiku Abubakar ya shaida hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Arise ranar Laraba.

Ɗan jaridar ya tambayi Atiku cewa yanzu shekarunsa sun kai 80 da alama wannan ce takararsa ta ƙarshe kasancewa shekarun nasa sun ja, sai tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce "E wannan haka yake. Babu ja a ciki."

Getty ImagesSa'o'i 5 da s**a wuceLokacin karatu: Minti 3Bayan rashin tabbas da tattalin arziƙin duniya ya fuskanta a she...
16/04/2026

Getty Images

Sa'o'i 5 da s**a wuce

Lokacin karatu: Minti 3

Bayan rashin tabbas da tattalin arziƙin duniya ya fuskanta a shekarar da ta gabata, tattalin arziƙin ya sake gamuwa da cikas sanadiyyar rikicin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya.

Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta ce ko da rikicin bai yi tsawo ko kuma ya ƙazance fiye da ƙima ba, duk da haka hasashen da aka yi na ci gaban tattalin arzikin duniya a 2026 zai gamu da cikas, inda zai yi rauni zuwa 3.1.

Amma hukumar ta yi gargadin cewa idan yain na Gabas ta Tsakiya ya tsananta, har ya kai ga cewa farashin makamashi ya jijjiga duniya, hasashen ci gaban tattalin arziin duniya zai iya faowa zuwa kashi 2% kacal a shekarar ta 2026.

Haka nan tashin farashin kaya zai iya haura kashi 6% a shekarar 2027.

Farashin man fetur da gas ya yi tashin da ba a gani ba a baya-bayan nan tun bayan da Amurka da Isra'ila s**a ƙaddamar da yaƙi kan Iran.

Ofishin kula da basuss**an Najeriya ya gabatar da wannan adadi, a ci gaba da rahotannin da yake bayarwa lokaci zuwa loka...
16/04/2026

Ofishin kula da basuss**an Najeriya ya gabatar da wannan adadi, a ci gaba da rahotannin da yake bayarwa lokaci zuwa lokaci dangane da bashin da gwamnatin ƙasar ke ciyowa domin gudanar da manyan ayyuka.

Ƙarin bayani: https://rfi.my/CcHb

Address

Zamfara
Gusau
860272

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa dae posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category