STV online

STV online STv Multimedia Services NIG LTD Gidan Tv ne dake Yada Shirye-Shiryensa da Harshen Hausa. Da Dai Sauransu. https://youtu.be/5RaLbaocJrU

Muna kawo maku Taron Siyasa kaitsaye, Documentary, Drone Shot, Tallace- Tallacen Sana’o’inku.

KIRA GA SHUGABA TINUBU: A DUNKULE WANNAN BARAKA KAFIN ZABEN 2027Ya Kamata Mai Girma Shugaban Ƙasar Najeriya, Asiwaju Bol...
28/08/2026

KIRA GA SHUGABA TINUBU: A DUNKULE WANNAN BARAKA KAFIN ZABEN 2027

Ya Kamata Mai Girma Shugaban Ƙasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani domin sasanta rikice-rikicen siyasa da ke tsakanin wasu manyan jiga-jigan APC a Jihar Zamfara kafin zuwan zaɓen 2027.

Wannan kira na zuwa ne bisa la’akari da yadda har yanzu ake ganin akwai bambance-bambancen ra’ayi tsakanin wasu daga cikin manyan ƴan siyasar jihar.

Saboda idan aka samu haɗin kai da fahimtar juna tsakanin jagororin jam’iyyar, hakan zai ƙara wa APC ƙarfi tare da samar da kyakkyawan yanayi na tunkarar zaɓe.

A halin yanzu dai, an samu wasu matakai na haɗin kai a cikin APC na Zamfara; a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a watan Afrilu 2026, manyan jiga-jigan jihar ciki har da Bello Matawalle da Abdul’aziz Yari sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC.

STV ONLINE — Gaskiya da Gaskiya.

Motoci  Masu aiki da iskar Gas 120,000 zasu fara aiki don Saukakawa Yan Najeriya a bangaren zirga-zirga.Shugaban Ƙasa Bo...
28/08/2026

Motoci Masu aiki da iskar Gas 120,000 zasu fara aiki don Saukakawa Yan Najeriya a bangaren zirga-zirga.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi sun amince da ɗaukar matakan gaggawa domin rage kuɗin sufuri a faɗin Najeriya, da nufin tabbatar da cewa ’yan ƙasa sun fara cin gajiyar sauƙin kuɗin mota daga ranar 1 ga Oktoba, 2026.

Shirin zai mayar da hankali kan ƙara amfani da motocin da ke amfani da Gas ɗin CNG da kuma motocin lantarki, waɗanda kuɗin gudanar da su zai zama me sauƙi idan aka kwatanta da motocin da ke amfani da fetur.

Tinubu ya ce motocin da ke amfani da CNG na iya rage kashe kuɗin mai da kaso 60 zuwa 80 cikin 100 idan aka kwatanta da motocin da ke amfani da fetur.

Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa an riga an sauya tsarin motocin sama da 120,000 domin su riƙa amfani da CNG, yayin da ake kuma kera ƙarin na’urorin sauya tsarin motoci sama da 100,000.

Haka kuma, ya bayar da umarnin ƙara gina tashoshin cika CNG guda 500, wanda zai kai yawan tashoshin da ake shirin samarwa a faɗin ƙasar zuwa 1,000.

Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi za su kafa kwamitin haɗin gwiwa domin fara aiwatar da waɗannan matakai. Ya jaddada cewa sauƙin da za a samu wajen kashe kuɗin mai ya kamata ya haifar da raguwar kuɗin sufuri kai tsaye, musamman ga masu zirga-zirga a cikin jihohi.

Murtala Adamu STv
STV online

HotunanHegin Baza tare da Mai Palace
27/08/2026

Hotunan
Hegin Baza tare da Mai Palace

Tirkashi.
27/08/2026

Tirkashi.

27/08/2026

Cikakken Jawabin Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, Dan majalisa mai wakiltar Gusau da Tsafe a Majalisar Dokokin Najeriya.

Alokacin da Yake Raba Ma masu Tu’ammali da Gidajen Tv na Online dake Jahar Zamfara.

Online TV’s na Godiya Hon. Kabiru Amadu Maipalace Muna Godiya✅
26/08/2026

Online TV’s na Godiya Hon. Kabiru Amadu Maipalace Muna Godiya✅

Hon Kabiru Amadu Mai Palace Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Ƙananan Hukumomin Gusau Da Tsafe, A Yau ya Ƙaddamar da Ya...
25/08/2026

Hon Kabiru Amadu Mai Palace Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Ƙananan Hukumomin Gusau Da Tsafe, A Yau ya Ƙaddamar da Yaƙin Neman Zaɓen sa Karo na Ukku, A Garin Mada Dake Cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Gusau.

DA DUMI-DUMI: Tinubu Ya Janye Jerin Sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APCFadar Shugaban Ƙasa ta Najeriya ta janye jerin...
25/08/2026

DA DUMI-DUMI: Tinubu Ya Janye Jerin Sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC

Fadar Shugaban Ƙasa ta Najeriya ta janye jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, bayan ce-ce-ku-ce da jerin ya haifar tun bayan fitar da shi ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a sake duba tare da sake tsara kwamitin, domin tabbatar da cewa an bai wa manyan jiga-jigan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban gurbi.

Sai dai, rahotannin sun ce ba a janye nadin tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin ba.

24/08/2026

TAKAITATTUN LABARAN DUNIYA 24/08/2026

STV online

Address

Canteen Daji Gusau
Gusau
1234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when STV online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share