
21/09/2025
Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ‘yanci
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya tabbatar da amincewar ƙasarsa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kai daga yau Lahadi.
Me ya sa wannan ya zama tarihi?
Birtaniya (United Kingdom) ba England kaɗai bace. Ƙasa ce da ta haɗu da ƙasashe huɗu: England, Scotland, Wales da Northern Ireland.
Matakin yana nufin duka ƙasar UK ta ɗauki wannan matsaya, ba England kaɗai ba.
Starmer ya ce wannan ba goyon bayan Hamas ba ne, illa dai ƙoƙari na farfado da tsarin zaman lafiya na ƙasashe biyu.