29/03/2024
Waye Sayyidina Aliyu ( RA ) عَلِيّ بْن أَبِي طَالِب; ?
Dan kabilar (Banu Hashim Bakuraishe) Mahaifinsa; Abu Talib ibn 'Abd al-Muttalib Mahaifiyarsa; Fatimah bint Asad.
Sayyadi Aliyu Radiyallahu Anhu, shi ne Aliyu Dan Abu-Dalib, babansa Abu-Dalib dan-Uwan mahaifin Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama ne, k*ma shine mijin Fatima Radiyallahu Anha diyar Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama.
Shi ne Khalifa na hudu daga jerin Khalifofin Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama, yana daya daga cikin wadanda akayi wa bushra da Aljannah.
Sayyadi Aliyu dan-uwan Annabi ne k*ma surikinsa ne. Ana masa kinaya da Abul-Hassan ko Abut-Turab. Mahaifiyar sa ita ce Fatima Diyar Asad dan Hashim.
Sayyadi Aliyu Jarimi ne, Mai fahimtar Al-Kur’ani ne da Sunnah, Adali ne, Mai Zuhudu ne, Mai Ilimi ne k*ma ga kunya, Aliyu nada Hikima da Fasaha, Allah yakara masa Rahama. Amin.
FALALAR SAYYADI ALIYU RADIYALLAHU ANHU
Hadisai sun inganta daga Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama, a cikin falalar Sayyadi Aliyu kamar Haka:
1. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Duk wanda na zamo shugabansa k*ma majibincin lamarinsa to, Aliyu ma shugabansa ne. (Ibn Maja 4/335)
2. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Lallai babu mai son Aliyu sai mumini, k*ma babu mai kin Aliyu sai Munafiki. (Ibn Maja 98)
3. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Aliyu daga gareni yake nima daga Aliyu nake. ( Tirmuzi 2931)
4. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: kallon Aliyu ibada ne. (Tarikh al- Khulafa p171).
5. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Matsayin Aliyu a gurina kamar matsayen Haruna ne ga Annabi Musa (Bukhari da Muslim)
6. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama ya daura shi akan gadonsa lokacin Hijira zuwa Madina k*ma ya danka amarnar ajiyar kuraishawa a hannun sa.
7. Sayyadi Aliyu ya yi Jihadi tare Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama don daukaka Addinin Allah, k*ma ya halacci duk yakunan Annabi banda yakin Tabuka.
Bayan tsawon Rayuwa a cikin Imani, Sayyadi Aliyu Radiyallahu Anhu, yayi Shahada