
05/09/2025
YAA ALLAH GAMU GAREKA😭
Wallahi da na saurari kalaman Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare sai da naji duniyar ma gaba daya ta fita a raina saboda cin amanar da ake yiwa tsaron Arewa
Gwamna Dauda yayi rantsuwa yace: Wallahi Tallahi a cikin wannan wayar tawa duk inda ‘yan bindiga s**a shiga a Zamfara ina gani, amma ban da ikon bawa Sojoji umarnin kai musu farmaki, sai dai abin da aka ce su yi daga sama.”
“Wallahi Tallahi wani lokacin har hawaye nake zubarwa idan na ga yadda nake neman agajin sojoji, amma suna ki, saboda sai sun jira umarni daga sama.”
Na tura bidiyon a Telegram ku je ku saurari bayanan Gwamnan ta nan
👇
https://t.me/DattiassalafiyTech
Gwamna Dauda Lawan yace wani laifi talaka ya maka da zaka kashe shi? wannan wani irin rashin imani ne haka?
A karshen bayanan Gwamnan yace duk mai hannu a kan wannan lamari na kashe-kashe ya Allah Ka birkitashi, idan mai Mulki ne Ya Allah Ka kwace mulkin, idan mai neman mulki ne Ya Allah kar ka bashi
Daga Datti assalafy.