Dan kullum TV

Dan kullum TV *Shirye muke a ko yaushe domin kawowa masu kallonmu ingantattun shirye - shirye dangane da rayuwa

Sarkin Zuru ya kai ziyarar jaje ga yan' kasuwar Zuru ya bayar da tallafin Naira ₦25,000 ga kowane Mutum Daya wadanda Gob...
17/09/2025

Sarkin Zuru ya kai ziyarar jaje ga yan' kasuwar Zuru ya bayar da tallafin Naira ₦25,000 ga kowane Mutum Daya wadanda Gobarar kasuwar ta rutsa da su.

Mai martaba sarkin Zuru Alh Sanusi Mikailu Sami Sami Gomo III a yayin ziyararsa ya bayyana matukar jimaminsa game da wannan masifa da ta afkawa dimbin yan kasuwar tare da kone dukiyoyi masu tarin yawa.

Mai martaba Sarkin Zuru ya bayyana tausayinsa ga wadanda abin ya shafa Allah ya mayar musu da sabon arziki.

Sarkin ya baiwa kowane mai shago da Gobarar ta rutsa da shi Naira dubu ₦25,000 don rage musu radadin wannan babban al'amarin.

Sarkin Zuru ya samu rakiyar mataimakin shugaban karamar hukumar Mulkin Zuru Hon Samaila Abdullah da APC Chairman Zuru Alh Aliyu Abubakar Abiola da jami'an tsaro domin yin jaje ga yan' kasuwar da abin ya shafa.

📸 Abbakar Aleeyu Anache

Hukumar Kwastan ta Najeriya ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 4% na kayan da ake shigo da su bisa umarnin Ma’aikata...
17/09/2025

Hukumar Kwastan ta Najeriya ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 4% na kayan da ake shigo da su bisa umarnin Ma’aikatar Kudi

Hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ta karɓi umarnin Ma’aikatar Kudi na dakatar da aiwatar da harajin kashi 4% na Farashin kaya kafin ɗauko su daga ƙasar da aka samo su wato Free-on-Board (FOB) da aka ɗora kan kayayyakin da ake shigo da su ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Abdullahi Maiwada, ya fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce tana godiya da wannan matakin da Ma’aikatar Kudi ta ɗauka tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da bin manufofin gwamnati na tattalin arziƙi.

Dr Maiwada ya ce hukumar ta fara tattaunawa da Ma’aikatar Kudi domin tabbatar da cewa ba a samu cikas a ayyukan hukumar ba.

Hukumar ta kuma yi karin haske kan rahotannin da ke yaɗuwa a kafafen yaɗa labarai cewa harajin kashi 4% na FOB ƙirƙiro shi a kayi a ‘yan kwanakin nan. Ta ce wannan tanadi ne na doka da Majalisar Tarayya ta kafa a cikin Sashe na 18(1)(a) na Dokar Hukumar Kwastan ta 2023, wanda ya tanadi cewa “ba za a karɓi kasa da kashi 4% na FOB ba akan kayayyakin da ake shigo da su, bisa tsarin da duniya ke bi.”

Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, tare da tabbatar da sauƙaƙe cinikayya da kuma ƙara samun kudaden shiga ga gwamnati.

“Muna da kwarin gwiwa cewa tattaunawa da Ma’aikatar Kudi da sauran masu ruwa da tsaki za su samar da mafita da za ta fi amfani ga Najeriya baki ɗaya, ta hanyar ƙara samun kudaden shiga da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa,” in ji sanarwar.

Hukumar Kwastan ta ce za ta ci gaba da aiki da ‘yan kasuwa, masu fitar da kaya da hukumomin ƙasa da ƙasa wajen tabbatar da gudanar da ayyuka cikin bin ƙa’idoji.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Abuja daga birnin Paris bayan kammala hutun aikinsa domin ci gaba da aikinsa. Shu...
16/09/2025

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Abuja daga birnin Paris bayan kammala hutun aikinsa domin ci gaba da aikinsa. Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, Shugaban ma’aikata Femi Gwamnan jihar Nassarawa H. E Adbulahi Sule ne s**a tarbe shi

Farashin kayan masarufi na ci gaba da sauka a Najeriya - Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS)Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ...
16/09/2025

Farashin kayan masarufi na ci gaba da sauka a Najeriya - Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS)

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kaya a Najeriya ya sauka zuwa kashi 20.12 cikin ɗari a watan Agusta 2025.

A cikin rahoton da hukumar ta fitar kan Consumer Price Index (CPI) da hauhawar farashin kaya na watan Agusta, ta bayyana cewa adadin ya ragu da kashi 1.76 cikin ɗari idan aka kwatanta da na watan Yuli wanda ya kai kashi 21.88 cikin ɗari.

Hukumar ta ce idan aka yi la’akari da shekara ɗaya kacal, hauhawar farashin kaya ya yi ƙasa da kusan kashi 12.03 cikin ɗari, inda a watan Agusta 2024 aka samu kashi 32.15 cikin ɗari.

Rahoton ya kuma nuna cewa, hauhawar farashin abinci ya tsaya a kashi 21.87 cikin ɗari idan aka kwatanta da bara, inda ya kai kashi 37.52 cikin ɗari.

A matakin wata zuwa wata kuwa, farashin abinci ya tsaya a 1.65 cikin ɗari, bayan da a watan Yuli ya kai 3.12 cikin ɗari.

A cikin rahoton, an bayyana cewa hauhawar farashi a birane ya tsaya a 19.75 cikin ɗari, yayin da a karkara ya kai 20.28 cikin ɗari.

Rahoton ya kawo jerin jihohin da s**a fi samun hauhawar farashi a shekara wanda suma haɗa da:
• Ekiti (28.17%)
• Kano (27.27%)
• Oyo (26.58%)

Jihohin da s**a fi samun saukin hauhawar farashi kuwa sun haɗa da:
• Zamfara (11.82%)
• Anambra (14.16%)
• Enugu (14.20%)

A bangaren abinci kuwa, rahoton ya ce jihohin da s**a fi hauhawar farashi a shekara sun haɗa da:
• Borno (36.67%)
• Kano (30.44%)
• Akwa Ibom (29.85%)

Yayin da Zamfara (3.20%), Yobe (3.60%) da Sokoto (6.34%) s**a fi samun sauki.

"Zan kawo jihar Sokoto a zaben 2027 idan Allah ya nuna mana, zan yi kasa-kasa da Bola Ahmad Tinubu a jihar Sokoto".Sanat...
16/09/2025

"Zan kawo jihar Sokoto a zaben 2027 idan Allah ya nuna mana, zan yi kasa-kasa da Bola Ahmad Tinubu a jihar Sokoto".

Sanata Aminu Waziri Tambuwal

16/09/2025

Fitar SANATA KABIR GARBA MARAFA a jam'iyyar APC Dimbin magoya bayan shi sunce ALLAH RAKA TAKI GONA su kam suna nan DARAM-DAM a jam'iyyar su ta APC.

Kotu Ta Baiwa Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Umarnin Ta Gayyaci Jaafar Jaafar Domin Yin BincikeRundunar ƴan sandan Nije...
15/09/2025

Kotu Ta Baiwa Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Umarnin Ta Gayyaci Jaafar Jaafar Domin Yin Bincike

Rundunar ƴan sandan Nijeriya, yanki na ɗaya, Kano, ta bayyana cewa gayyatar da ta aike wa mamallakin Jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, da Mawallafinsa, Audu Umar, ba wai tsangwama bace, cika umarni ne na Kotun Majistiri ta 15 da ke Normans Land, Kano, kamar yadda Arewa Media ta ruwaito.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, rundunar ƴansandan ta ce kotun ta umurce ta da ta gudanar da bincike kan zargin haɗin-baki wajen aikata laifi, ɓatanci ga mutum, da ƙoƙarin tada hankalin jama’a bisa dokar ACJL 2019.

Sai dai kuma, sanarwar ta jaddada cewa kotu ta bayyana a fili cewa ba za a tsare waɗanda ake tuhuma ba har sai an kammala shari’ar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula, kafafen yaɗa labarai da jama’a gaba ɗaya da su bar bincike ya yi aikinsa. Sannan kuma a guji yin duk wasu maganganu da za su iya shafar shari’ar.

A cewar rundunar, za ta ci gaba da kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa, tare da tabbatar da adalci a kowane irin al'amari.

Shugaba Tinubu zai dawo gida daga hutu kafin wa’adin hutun sa ya cika. Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kammala hutunsa na ...
15/09/2025

Shugaba Tinubu zai dawo gida daga hutu kafin wa’adin hutun sa ya cika.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kammala hutunsa na aiki a waje tun kafin lokacin da aka tsara, inda ake sa ran zai dawo Abuja gobe Talata, 16 ga Satumba, 2025 domin ci gaba da aiki.

Shugaban ya tafi Faransa ne tun ranar 4 ga Satumba domin yin wani ɓangare na hutun shekara, inda a baya aka shirya ya raba lokacin hutun tsakanin Faransa da Birtaniya.

A makon jiya a Paris, Shugaba Tinubu ya gana da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a wata liyafa a fadar Élysée. Shugabannin biyu sun tattauna kan muhimman fannoni na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen su, tare da amincewa wajen ƙara zurfafa dangantaka domin ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya a duniya.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da dawowar shugaban a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.

Abin kaico ne yadda Nijeriya ta jima tana fama da rubabbun shugabanni, in ji Sarki Muhammad Sanusi na
15/09/2025

Abin kaico ne yadda Nijeriya ta jima tana fama da rubabbun shugabanni, in ji Sarki Muhammad Sanusi na

15/09/2025

Tattaunawa tare da shugaban Hukumar Hajji ta jihar zamfara. Akan shirye shirye aikin hajji da kuma sabbin tsare-tsaren Hukumar

Alh Musa Mallaha
Talban Gusau

15/09/2025

Bukin rantsar da shuwagabannin jiha da kuma na kananan hukumomin a madadin kungiyar Zannawa Movement

Karkashin shugaban kungiyar Hom Aliyu Ahmad ladan Gusau

PHOTOS: ZAMFARA STATE MINISTRY OF EDUCATION, SCIENCES AND TECHNOLOGY  GUSAU. ADOLESCENT GIRLS INITIATIVE FOR LEARNING AN...
14/09/2025

PHOTOS: ZAMFARA STATE MINISTRY OF EDUCATION, SCIENCES AND TECHNOLOGY GUSAU. ADOLESCENT GIRLS INITIATIVE FOR LEARNING AND EMPOWERMENT (AGILEPROJECT)

BIANNUAL MEDIA ROUND TABLE

THEME: DEVELOPMENT COMMUNICATION FOR ADOLESCENT GIRLS EDUCATION.

Address

Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan kullum TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dan kullum TV:

Share

Category