Dan kullum online TV

Dan kullum online TV *Shirye muke a ko yaushe domin kawowa masu kallonmu ingantattun shirye - shirye dangane da rayuwa

29/07/2026
AYAU YA CIKA SHEKARA DAYA (1) KAN KARAGAR MULKI. WANE FATA ZAKUYI MASA??MAI MARTABA ABDULKADIR II : SARKIN KATSINAN GUSA...
29/07/2026

AYAU YA CIKA SHEKARA DAYA (1) KAN KARAGAR MULKI. WANE FATA ZAKUYI MASA??

MAI MARTABA ABDULKADIR II : SARKIN KATSINAN GUSAU NA 16.

An haifi Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello Ranar 1-12-1977. Bayan karatun Addinin Musulunci a wajen Malamai daban - daban a garuruwa daban daban ya kuma yi karatun zamani a Township Model Primary School, Gusau da GSSS, Gusau da GDSS Danturai, Gusau da GDSS B/Ruwa, Gusau da Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto da Biomedical College, Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Ahmadu Bello, Shika, Zaria daga shekarar 1985 zuwa shekarar 2013.

A lokacin wannan karatu nasa ya samu takardun shedar gama karatun Firamare da karatun Karamar Sakandare dana babbar Sakandare da Karatun Digirin farko a fannin Turanci da kuma Satifiket a fannin Injiniyancin kiyon lafiya.

Yayi aikin kula da rage cutar maleriya a Karamar Hukumar Mulkin Talata Mafara da Asibitin King Fahd, Gusau da Babbar Asibitin Gusau da Hukumar Kula da Asibitota/Asibotoci ta Jihar Zamfara da kuma Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Zamfara. Ya na da aure da kuma 'ya'ya.

An nad'a shi sarautar Bunun Gusau a shekarar 2017 matsayin da yake rike dashi har zuwa ranar Talata 29/07 /2025 da aka tabbatar masa da sarautar Sarkin Katsinan Gusau sanadiyar rasuwar mahaifinsa, Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR ranar 25/07 /2025.

Dan Sarkin Katsinan Gusau Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR wato Sarki na 15 ne, Sarkin Katsinan Gusau Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR d'an K'ogo /Kogo Bello Bello ne, K'ogo /Kogo Bello d'an Sarkin Katsinan Gusau na 6 Murtala (1900-1916) ne, Sarki Murtala dan Sarkin Katsinan Gusau na 3 Muhammad Modibbo (1867-1876) ne, Sarki Muhammadu Modibbo kuma d'an Sarkin Katsinan Gusau na farko, Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa (1799-1827) ne.

A gefen mahaifiyarsa kuwa d'an Hajiya Jamila Alh. Aliyu ne. Hajiya Jamila 'ya /d'iya ce ga mashahurin attajirin nan ne da aka yi a Birnin Gusau, Jihar Zamfara Alhaji Aliyu Dango da aka fi sani da kinayar "Dango d'an aljanna" ( zamu kawo dalilin kiran sa da wannan kinayar a nan gaba In Shaa Allah).

Wannan matsayi da Allah SWT ya bashi ya sa ake yi masa lak'abi da "Sarkin Katsinan Gusau Abdulkadir II" domin kuwa an yi Sarkin Katsinan Gusau Abdulkadir I d'an Sarkin Katsinan Gusau Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa wanda ya yi sarauta daga shekarar 1827 zuwa 1867, kenan shi ne Sarkin Katsinan Gusau na biyu domin shi ne ya gaji/gadi mahaifinsa Sarkin Katsinan Gusau na farko, Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa. Allah ya jaddada masu rahama, amin.

Daga Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ya zuwa yau anyi Sarakuna 16 a Gusau duk kuwa da yake ba dukan su ne s**a fito daga gidan sarautar Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ba.

Tsarin Sarakunan Gusau /Sarkin Katsinan Gusau :

1. Mal. Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa (1779-1827)
2. Mal. Abdulkadir I(1827-1867)
3. Mal. Muhammadu Modibbo (1867-1876)
4. Mal. Muhammadu Tub'uri (1876-1887)
5. Mal. Muhammadu Gid'e (1887-1900)
6. Mal. Muhammadu Murtala (1900-1916)
7. Mal. Muhammadu Dangidan (1916-1917)
8. Mal. Umaru Malam(1917-1929)
9. Mal. Muhammadu Mai'akwai(1929-1943)
10. Mal. Usman d'an Sama'ila (1943-1945)
11. Marafa Mal. Ibrahim (1945-1948)
12. Mal. Muhammadu S/Kudu(1948-1951)
13. Alh. Sulaimanu S/Kudu (1951-1984)
14. Alh. Muhammadu Kabir Danbaba(1984-2015)
15. Alh. Ibrahim Bello (2015-2025)
16. Alh. Abdulkadir II ( Juli 2025-)

Daga Sarki na 8, Malam Umaru Malam (1917-1929) zuwa Sarki na 13, wato Malam Sulaimanu S/Kudu (1951-1984) sune Sarakunan Gusau wadanda ba daga gidan sarautar Mal. Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa s**a fito ba. Sai a shekarar 1984 lokacin da aka nad'a Marigayi Mai martaba Alhaji Muhammad Kabir Danbaba sarauta ta dawo gidan Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ya zuwa yau.

Allah SWT ya jaddada rahamarsa zuwa ga magabatanmu, ya yiwa Sarkin Katsinan Gusau na 16, Alh. Abdulkadir Ibrahim Bello II jagora, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
04/08/2025.

Sojojin Bataliya ta 65 sun rushe wurin satar mai a Lagos, sun k**a mutum shidaSojojin Bataliya ta 65 ƙarƙashin jagoranci...
29/07/2026

Sojojin Bataliya ta 65 sun rushe wurin satar mai a Lagos, sun k**a mutum shida

Sojojin Bataliya ta 65 ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanal S. Adeojo sun rushe wani wurin da ake zargin ana yin haramtacciyar harkar bunkering (satar mai) a yankin Orile na Jihar Lagos.

A wata samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri, sojojin sun kai farmaki wurin tare da k**a mutane shida da ake zargin masu satar mai ne.

An kuma kwato manyan motoci huɗu, injin tura mai guda ɗaya, da wasu bututu da ganguna da ake zargin ana amfani da su wajen wannan haramtacciyar sana’a.

An miƙa waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato ga Hukumar NSCDC ta Jihar Lagos domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da s**a dace.

Babban Kwamandan Runduna ta 81 ta Sojojin Najeriya, Manjo Janar Adebayo Abdulrahman Babalola, ya yaba wa sojojin kan nasarar aikin tare da umartar su da su ci gaba da yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa da sauran ayyukan ta’addanci a yankin rundunar.

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Mutumin Da Ya Fi Kowa Tsawo A Ƙasar Ghana, Sulemana Abdulsamed Ya Rasu Yana Da Shek...
29/07/2026

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Mutumin Da Ya Fi Kowa Tsawo A Ƙasar Ghana, Sulemana Abdulsamed Ya Rasu Yana Da Shekara 33 Da Haihuwa

Allah Ya Jiƙan Sa Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa

Gwamna Dauda Lawal a ƙasar Sin domin halartar bikin ƙaddamar da katafaren kamfanin sarrafa ma’adanin lithium na Jinlide-...
29/07/2026

Gwamna Dauda Lawal a ƙasar Sin domin halartar bikin ƙaddamar da katafaren kamfanin sarrafa ma’adanin lithium na Jinlide-Qiangyu New Energy Plant da ke birnin Nanchang, lardin Jiangxi.

Ziyarar na da manufa ta ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Jihar Zamfara da masu zuba jari na ƙasar Sin, musamman wajen ƙara darajar albarkatun ma’adanan Najeriya ta hanyar sarrafa lithium zuwa kayayyakin da aka kammala, waɗanda ake amfani da su a masana’antar mak**ashi.

Ana kuma sa ran wannan haɗin gwiwa zata kawo sauyin fasaha (technology transfer), jawo sabbin masu zuba jari, bunƙasa masana’antu, samar da ayyukan yi, da ƙarfafa tattalin arzikin Jihar Zamfara.

Wannan wani muhimmin mataki ne na gwamnatin Gwamna Dauda Lawal wajen tabbatar da cewa albarkatun ma’adanan Zamfara ba kawai ana haƙo su ba, har ma ana sarrafa su domin ƙara musu ƙima, samar da ci gaba mai ɗorewa, da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Rundunar Sojin Najeriya Ta Nada Sabbin Kwamandojin Rundunoni Yayin da Sabbin Divisoshi S**a Fara AikiRundunar Sojin Naje...
29/07/2026

Rundunar Sojin Najeriya Ta Nada Sabbin Kwamandojin Rundunoni Yayin da Sabbin Divisoshi S**a Fara Aiki

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da naɗin sabbin General Officers Commanding (GOCs) domin jagorantar wasu daga cikin sabbin divisoshin da aka kafa, yayin da ake ci gaba da aiwatar da shirin faɗaɗa rundunar domin ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar.

Sabbin naɗe-naɗen sun haɗa da:

Manjo Janar Yakubu Yahaya – Babban Kwamandan 9 Division da ke Ilorin, kuma Kwamandan Operation SAVANNA SHIELD.

Manjo Janar Chinedu Ralph Nnebeife – Babban Kwamandan 10 Division da ke Jalingo.

Manjo Janar Moses Gara – Babban Kwamandan 5 Division da ke Makurdi, tare da riƙe muƙamin Kwamandan Operation WHIRL STROKE.

Manjo Janar Auwalu Mahmuda – Babban Kwamandan 2 Division da ke Ibadan.

Hakazalika, Rundunar ta kuma sanar da ƙaddamar da sabbin brigadoji tare da naɗa kwamandojinsu k**ar haka:

Birgediya Janar A.O. Odubiyi – Kwamandan 11 Brigade, Gboko.

Birgediya Janar A.M. Haruna – Kwamandan 29 Brigade, Kainji.

Birgediya Janar R.M. Aminu – Kwamandan 10 Brigade, Lafia.

Sabbin divisoshin 5, 9, 10 da 83 Division sun samu amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki na faɗaɗa Rundunar Sojin Najeriya daga divisoshi takwas zuwa goma sha biyu.

KBC Hausa

29/07/2026

Kai tsaye daga babbar kotun shari’ar musulunci dake Gusau (Shari'a court of Appeal) Shirye shirye sun kank**a domin gudanar da taron.

Karrama Alkalin Alkalan jihar zamfara da lambar ( KHADIMU SHARI'A) Dr Dahiru muhammad Gusau.

Kai tsaye daga babbar kotun shari’ar musulunci dake Gusau (Shari'a court of Appeal) Shirye shirye sun kank**a domin guda...
29/07/2026

Kai tsaye daga babbar kotun shari’ar musulunci dake Gusau (Shari'a court of Appeal) Shirye shirye sun kank**a domin gudanar da taron.

Karrama Alkalin Alkalan jihar zamfara da lambar ( KHADIMU SHARI'A) Dr Dahiru muhammad Gusau.

Address

Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan kullum online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dan kullum online TV:

Shortcuts

Share

Category