
12/09/2025
Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, a matsayin ginshiƙi na zaman lafiya da haɗin kai a Nijeriya, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen bunƙasa masarautar Nupe, Jihar Neja, da ƙasa gaba ɗaya.
A cikin saƙon taya murna na zagayowar ranar haihuwar sa ta 73 da kuma cika shekara 22 a kan karagar mulki, Ministan, wanda shi ne Kakakin Nupe, ya ce: “Etsu Nupe mutum ne mai jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, wanda a cikin shekaru 22 da s**a gabata ya jagoranci ƙasar Nupe zuwa cigaba da bunƙasar da ba a taɓa ganin irin ta ba.”
Idris ya jaddada rawar da Sarkin Mai Daraja ta Ɗaya ya taka wajen ƙarfafa haɗin kan Nijeriya, tun daga gudunmawar sa a rundunar sojin ƙasa har ya kai matsayin Birgediya Janar, zuwa irin gudunmawar da yake bayarwa a matsayin Shugaban Kwamitin Tsara Ayyuka na Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Nijeriya.
Ya ƙara da cewa: “Don haka taya ɗaya daga cikin shugabannin Nijeriya mafiya sauƙin kai, masu karamci da jarumtaka, murnar zagayowar ranar haihuwar sa, da roƙon Allah ya ci gaba da yi masa jagora a babban nauyin shugabanci na ƙasar Nupe da jama’ar ta, ya kuma ƙara masa ƙarfi don ci gaba da aiki wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da cigaban Nijeriya.”